Trump ya buƙaci coci-coci a Amurka su buɗe

Wannan shafi na kawo muku bayanai kai tsaye kuma da dumi-duminsu game da abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya musamman masu alaka da annobar korona da ma karin wasu daban.

Rahoto kai-tsaye

Nasidi Adamu Yahaya and Umar Mikail

  1. COVID-19: Za a rage albashin ma'aikata a Masar

    Gwamnatin Masar ta sanar da daukar matakan yin tsimi domin samun damar farfado da tattalin arzikinta wanda ya tabarbare sakamakon annobar korona.

    Cikin matakan har da rage kashi daya cikin dari na albashin ma'aikata sannan za a rage kashi hamsin cikin 100 na kudin fansho da ake bai wa tsofaffi.

    Za a soma aiwatar da matakan ne daga watan Yuli kuma za a yi shekara guda ana aiwatar da su. Sai dai lamarin ba zai shafi ma'aikatan da ke karbar kasa da $125 a duk wata ba.

    Kazalika lamarin ba zai shafi ma'aikatan da ke aiki a fannin yawan bude ido ba, wanda annobar korona ya shafa sosai.

    Sai dai lamarin ba zai shafi ma'aikatan da ke karbar kasa da $125 a duk wata ba.

    Asalin hoton, Getty Images

  2. Netflix zai ƙaddamar da fim ɗinsa na farko da aka yi a ƙasar Zimbabwe

    Kamfanin nan na nuna fina-finai ta intanet Netflix yana shirin ƙaddamar da fim ɗinsa na farko da aka yi a ƙasar Zimbabwe.

    Fim ne na barkwanci da soyayya mai taken "Cook Off".

    Labari ne na wata mata da ɗanta ya sanya ta shiga gasar dafa abinci ta gidan Talbijin.

    Ta dai fafata da goggagun kuku-kuku a kasar kafin ta kamu da ciwon so.

  3. Coronavirus a Kano: Yadda Ganduje ya zaftare albashin ma'aikata

    Ma'aikatan gwamnatin jihar Kano da ke Najeriya sun yi zargin cewa gwamnatin Abdullahi Umar Gandue ta zaftare musu albashi a daidai lokacin da suke shirye-shiryen ƙaramar Sallah.

    Galibin ma'akatan da BBC ta yi hira da su sun ce an biya su albashi a tsohon tsari – wato kafin a yi karin albashi - kuma an tsaftare kashi 10 zuwa 20 cikin 100.

    A cewarsu, lamarin ya jefa su cikin halin ƙunci da rashin tabbas, ganin yadda ƙungiyar ƙwadago a jihar ke cewa ba a tuntuɓe ta ba kafin daukar wannan matsaya.

    A makon jiya gwamnatin ta sanar da rage wa masu muƙaman siyasa rabin albashi saboda raguwar kuɗaɗen shiga dalilin faɗuwar farashin man fetur sakamakon annobar korona.

    Latsa alamar lasifika da ke sama don sauraren rahoton Khalifa Shehu Dokaji:

    Bayanan sautiCoronavirus a Kano: Yadda Ganduje ya zaftare albashin ma'akata
  4. Ministoci 10 sun kamu da cutar korona a Sudan ta Kudu

    An tabbatar da cewa ministoci goma sun kamu da cutar korona a Sudan ta Kudu.

    Ministan watsa labaran kasar Michael Makuei ya shaida wa BBC dukkan mambobin kwamitin yaki da cutar korona – idan ban da Ministan Lafiya -- sun kamu da cutar ta korona.

    Sai dai ya yi watsi da rahotannin da ke cewa Shugaba Salva Kiir - wanda shi ma mamba ne na kwamitin - ya harbu da cutar.

    Hakan ya faru ne kwana guda bayan mataimakin shugaban kasar Riek Machar ya sanar cewa shi da mai dakinsa da kuma Ministan Tsaro sun kamu da cutar korona

    Sun kamu da cutar ne bayan sun yi mu'amala da wani mamba na kwamitin, wanda ya kamu da cutar.

    Yanzu haka an killace dukkan ministocin da suka kamu da cutar kuma gwamnatin kasar ta ce suna cikin koshin lafiya.

    Masu taron lafiyar ministocin da dama sun kamu da cutar kuma su ma an killace su.

    An samu karuwar masu dauke da cutar korona a Sudan ta Kudu, inda alkaluma suka ce wadanda suka dauki cutar a kwanakin baya-bayan nan sun zarta 300 kuma mutum shida sun mutu.

    Salva Kiir

    Asalin hoton, AFP

  5. Barkanmu da Juma’a

      • Marubuci, Nasidi Adamu Yahya
      • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Hausa, Abuja

    Nasidi Adamu Yahaya ne yake yi muku barka da Juma’a.

    Da fatan za ku kasance da mu domin sanin halin da ake ciki dangane da cutar korona, wacce ta addabi kasashen duniya.

    Baya ga batun wannan cuta, za kuma mu kawo muku sauran labarai da rahotannin da suka shafi rayuwarku, musamman daga kasashen Najeriya da Nijar da ma wasu sassan duniya.

    Kuna iya tafka muhawara da bayyana ra’ayoyinku a shafukanmu na sada zumunta a BBC Hausa.