Covid-19: Ganduje ya ɗauki ma'aikatan agaji a masallatai

Wannan shafi na kawo muku bayanai kai tsaye kuma da dumi-duminsu dangane da wainar da ake toyawa a sassan duniya musamman masu alaka da annobar korona da ma karin wasu daban.

Rahoto kai-tsaye

Usman Minjibir, Nasidi Adamu Yahaya and Buhari Muhammad Fagge

  1. 'Kasancewar Amurka ja gaba a yawan masu korona daukaka ce'

    Trump

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Amurka, Donald Trump ya ce kasancewar Amurka a gaba wajen yawan masu cutar korona "alamar girma".

    Shugaban ya ce "ina kallon wannan abu a matsayin wani abun alkairi saboda hakan na nufin mun fi kowa yin sahihin gwajin cutar."

    Amurka na da mutum miliyan 1.5 da ke dauke da cutar ta korona inda kimanin 92,000 suka mutu, kamar yadda jami'ar Johns Hopkins University ta rawaito.

    Kasar Russia ce dai ke biye wa Amurkar inda take da mutum kimanin 300,000 masu dauke da cutar.

    Shugaba Trump dai ya bai wa Hukumar Lafiya ta Duniya wa'adin kwana 30 da ko dai ta fito da mafita kan cutar ko kuma Amurka ta fita fit daga hukumar abin da ke nuni da irin biliyoyin dalolon da hukumar ka iya rasawa.

    Har wa yau, Shugaba Trump ya ayyana maganin maleriya na hydroxychloroquine a mastayin maganin korona.

    Sai dai masana da likitoci sun soki wannan ikrarin nasa.

  2. Venezuela ta maka Burtaniya kotu kan zinariya

    Nicholas Maduro

    Asalin hoton, Getty Images

    Venezuela da ke fama da karanci kudi ta kai Burtaniya Kotu, a kokarin tilasta wa Bankin Ingila ba ta kudin zinariyarta da ya kai dala biliyan 1 da ta yi ajiya a asusun kasar.

    Venezuela na karkashin takunkumin Amurka da Burtaniya, inda kowacce kasa cikinsu ke daukar gwamnatin shugaba Nicolas Maduro a matsayin haramtacciya.

    Lauyoyin da ke wakiltar Babban bankin Venezuela sun ce ana bukatar kudin zinariyar --wadda wani bangare ne na ajiyar kasar -- domin yakar annobar korona.

    Sun ce bankin ya amince zai tura kudin kai tsaye ga Majalisar Dinkin Duniya domin tabbatar da cewa ba a karkatarsu zuwa wasu harkokin ba.

  3. Za a wajabta sanya takunkumi a Brazil

    Bolsonaro

    Asalin hoton, Getty Images

    'Yan majalisar Brazil sun yi wata doka da ta wajabta wa kowanne dan kasa ya kasance yana amfani da takunkumi idan ya fito daga gida.

    Dokar dai ta tanadi cewa duk wanda ya karya doka zai biya tarar dala 50.

    Rahotanni sun ce dole sai Kudirin dokar ya samu amincewar majalisar dattijai da kuma shugaba Jair Bolsonaro - wanda ba kasaifi yake amfani da takunkumin ba.

    Shugaban ya kuma ce mukaddashin ministan lafiyar kasar, zai sa hannu a kan dokar ba da izinin amfani da hydrocholoroquine wato maganin Maleriya don yi wa masu dauke da cutar maganin.

    Mista Bolsonaro ya ce ya yanke wannan shawarar ne ganin shugaba Trump na Amurka na shan kwayar.

  4. Saudiyya ta mayar da 'yan Najeriya kusan 300 gida

    King Salman

    Asalin hoton, Getty Images

    Ministan harkokin wajen Najeriya, Geoffrey Onyeama ya ce sun karbi 'yan Najeriya mutum 292 da suka makale a Saudiyya.

    Ministan wanda ya wallafa bayanin a shafinsa na Twitter ya ce jirgin Saudiyya ne ya kai mutanen filin jirgin sama da ke birnin Abuja a daren Talata.

    Ya kara da cewa mafi yawancin mutanen da aka mayar da su Najeriyar mata ne masu shayarwa da kananan yara.

    Sai dai ya ce yanzu haka an killace su a otal har zuwa makonni biyu kamar yadda dokokin kasa da kasa suka tanadar.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  5. Paul Biya ya umarci 'yan Kamaru su rinka sa takunkumi

    Paul Biya

    Asalin hoton, Getty Images

    A karo na farko Shugaban kasa Paul Biya na jamhuriyar Kamaru ya yi jawabi tun lokacin da aka gano mutum na farko da ya harbu da annobar korona a kasar a ranar 6 ga watan Maris.

    A yanzu haka dai cutar na dada yaduwa a kasar masamman ma a manyan birane.

    Alkaluman baya-bayannan sun nuna cewa mutane sama da 3,000 suka kamu da cutar ko da yake an samu sama da 1,500 da suka warke.

    Sakamakon wannan lamari Shugaban kasa ya ce sanya takunkumi na kariya ya zama dole har zuwa wani lokaci domin kaucewa kamuwa da cutar.

  6. 'Za mu dawo da duk dan Nijar da ke son dawo wa gida'

    Mahamdou Issoufou

    Asalin hoton, Getty Images

    Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta bayyana cewa kawo yanzu ta samu kwashe 'ƴan kasar kusan 2,000 da suka makale a kasashen waje dalilin annobar korona.

    Ministan harakokin wajen ƙasar Kalla Hankurau ya ce gwamnati za ta ɗauki nauyin mayar da duk dan kasar da ke son koma wa gida.

    ƙasa da mutum 1000 ne suka kamu da annobar a Nijar kuma sama da 700 suka warke yayin da kasa da 200 ke ci gaba da karbar magani inda kuma cutar ta kashe mutum 55

  7. Mun dogara ga sojojin jamhuriyar Nijar domin tsaro - Sanata Gobir

    Sanata Gobir

    Asalin hoton, WEbsite/Gobir

    Majalisar dattijai a Najeriya ta tabka muhawara kan matsalar tsaro da ta addabi yankunan arewacin kasar inda ta bukaci shugaba Muhammadu Buhari ya faɗaɗa umurnin da ya ba sojojin kasar na fatattakar barayi a jihar Katsina zuwa sauran jihohin da 'yan fashin suka addaba wato Zamfara da Kaduna da Niger da kuma Sokoto.

    Sanata Sabi ya'u na jihar Neja ne ya gabatar da bukatar, inda Sanata Ibrahim Abdullahi Gobir ya mara wa bukatar baya kuma majalisar ta amince.

    Wasu 'yan majalisar daga jihohin sun ce barayin za su gudu ne daga Katsina su koma domin fakewa a jihohinsu.

    Sanata Abdullahi Ibrahim Gobir daga Sokoto na Jam'iyyar APC ya zargi sojojin Najeriya da gazawa tare da cewa "yanzu sun dogara ne ga sojojn Nijar".

  8. Burundi za ta shiga zabe duk da annobar korona

    Nkurinziza

    Asalin hoton, Getty Images

    Kasar Burundi ta shirya gudanar da Babban zaben shugaban kasa domin maye gurbin shugaba mai-ci Pierre Nkurunziza, wanda gwamnatinsa ke fuskantar zarge-zargen tauye hakkin bil' adama a tsawon shekaru 15 da suka gabata.

    Tsohon janar din soja, Evariste Ndayi-shimiye ne ke wakiltar jam'iyyar CNDD-FDD da ke mulki.

    shugaban 'yan adawa Agathon Rwasa da wasu mutum biyar su ma sun shiga wannan takara.

    Pierre Nkurunziza ya lashe zaben 2015 a wani sabon wa'adi na uku cikin yanayi na kazamar zanga-zanga, da kuma kauracewa zaben da 'yan adawa suka yi, lamarin da ya ja hankalin kasashen duniya.

    A karkashin wata sabuwar dokar kasar, Shugaba Nkurunziza zai ci gaba da rike madafun iko har zuwa shekara ta 2034 a matsayin mai karfin fada aji kan lamura masu muhimmanci da suka shafi kasar.

    Kamfe

    Asalin hoton, Getty Images

  9. Za a koma makaranta a Koriya ta Kudu bayan zaman gida na watanni

    South Korea

    Asalin hoton, Getty Images

    Dubban dalibai za su koma makaranta a Koriya ta Kudu bayan shafe tsawon watanni ana zaman gida saboda annobar korona.

    Wadanda ke shirin gudanar da jarrabawar shiga Jami'i a watan Disamba su ne farkon komawa, sannan sauran dalibai sannu a hankali za su bi sahu a cikin makonni masu zuwa.

    Da zarar sun isa makarantu, ana bai wa daliban sinadarin tsafttace hannu, sannan a auna zafin jikinsu da kuma bin ka'idar bai-wa juna tazara.

    A farkon wannan watan an yi ta fargabar sake barkewar cutar a wani gidan rawa da ke Seol, sai dai mahukunta kasar sun ce zaa iya bude makarantu bayan tabbatar da cewa su ci karfin annobar.

  10. Guguwar Cyclone ta sauka a India da Bangaladesh

    India

    Asalin hoton, Getty Images

    Guguwa mai karfin gaske tafe da ruwan sama ta sauka a yankunan bakin teku da ke Bangladesh da Jihar Odisha ta Indiya da yammacin Bengal.

    Mahukunta na kokarin ganin sun kwashe dubban mazaunan yankunan musamma wayanda suka fi fuskantar barazanar guguwar irinta mafi karfi a tsawon shekaru.

    Rahotanni sun ce ambaliyar ruwa ita ce abin da ake fargaba, Akawai matsugunai da aka tanadar, sai dai akasarin wadanda ake kwashewar na nuna halin ko-in-kulla na zama a cibiyoyin da aka ware domin kebe masu korona idan an samu barkewar annoba.

    A yankin kudu maso gabashin Bangladesh jami'an agaji sun jibge abinci da magunguna ga kusan 'yan gudun hijirar Rohingya miliyan guda a sansanin da ke yankin.

  11. 'Mun gano dalilin mace-mace a arewacin Najeriya'

    Dr Sani Gwarzo

    Tawagar ƙwararrun da gwamnatin Najeriya ta tura zuwa yankin arewacin kasar domin bincike sanadiyyar mace-mace a wasu jihohin yankin ta ce ta kasa mace-macen gida bakwai kuma yanzu ta kusa kammala rangadin da take a jihohin, inda daga bisani za ta fitar da bayani.

    Shugaban kwamitin Dr Nasiru Sani Gwarzo ya ce kawo yanzu sun ziyarci jihohi shida daga cikin takwas da aka fuskanci mace-macen mutane a watan jiya.

    Dr Gwarzo ya kuma sun gano abubuwa da yawa game da mutuwar ta farat ɗaya da mutane suka rinka yi a jihohin arewacin kasar.

    "Mun je har makabarta inda muka kidaya kabarbarun mutane wasu mutanen kuma sun yi mana bayanai kan mamatansu. Amma kuma mun gano yadda a wasu jihohi an kambama mace-mace.

    Mun samu samfurin mamata a jihohi da dama kuma muna jiran sakamakon abin da ya kashe su."

  12. Budewa

    Masu bibiyarmu barkanku da war haka. Da fatan kuna cikin koshin lafiya. Yaya daruruar annobar korona? Allah ya kare mu baki daya. Da fatan za ku ci gaba da kasance wa da shafin bbchausa.com domin samun labarai da bayanai kai tsaye kuma da dumi-duminsu. Mun gode.