Coronavirus: Ko Buhari da Ganduje sun raba gari ne?

Wannan shafi na kawo muku bayanai kai tsaye dangane da irin wainar da ake toyawa a fadin duniya musamman batutuwan da suka shafi annobar korona na ma karin wasu daban.

Rahoto kai-tsaye

Usman Minjibir, Nasidi Adamu Yahaya and Buhari Muhammad Fagge

  1. India da Bangladesh za su fuskanci guguwar Cyclone

    INDIA

    Asalin hoton, EPA

    Kasashen India da Bangladesh na ta faman jigilar kwashe miliyoyin al'ummarsu da ke zaune a bakin ruwa a yunkurin kawar da su gabanin mahaukaciyar guguwa mai tafe da ruwa da ke tunkarar kasashen biyu yanzu haka.

    Ana hasashen guguwar za ta afka kan jihohin India guda biyu na Bengal ta yamma da Odisha da kuma wasu sassan kasar Bangladesh.

    Masana yanayi sun hasashe cewa guguwar za ta afka wa wani wuri ne da ke kan iyakokin kasar guda biyu ranar Laraba.

    Duk da cewa kasashen guda biyu na da kwarewa wajen tun karar irin wannan guguwa idan ta taso saboda sabo da suka yi da ibtila'in, cutar korona na yi wa shirin kwashe jama'ar cikas.

    An kafa karin tanti-tanti a wuraren da za a tsugunar da mutanen domin tabbatar da samun tazara tsakaninsu sannan kuma ana raba wa mutane takunkumin fuska domin kariya daga annobar korona.

  2. China ta mayar wa Amurka martani kan Hukumar Lafiya ta Duniya

    China US

    Asalin hoton, Getty Images

    Rashin jituwa tsakanin China da Amurka dangane da rawar da Hukumar Lafiya ke takawa kan annobar korona na kara yin tsami.

    Ministan kasashen wajen China ya zargi shugaba Trump na Amurka da caccakar Hukumar Lafiya ta Duniya inda ya ce hakan wani abu ne mai kama da barin jaki a bugu taiki saboda Amurkar ta kasa shawo kan annobar da ke damun ta.

    Shi kuma shugaba Trump ya bai wa Hukumar Lafiyar ta Duniya wa'adin kwana 30 inda ya ce idan har al'amura ba su daidaita ba to zai daina bai wa hukumar tallafi baki daya kuma Amurka ta fice daga Hukumar.

    Ministan harkokin China, Zhao Lijan ya shaida wa manema labarai cewa Amurka na shirin bata wa China sunane saboda ta gaza.

  3. Brazil ce kasa ta uku mai yawan masu korona a duniya

    Bolsanaro

    Asalin hoton, Getty Images

    Kasar Brazil ta zama kasar duniya ta uku da ke da yawan masu dauke da cutar korona, inda take da mutum 250,000 masu fama da cutar.

    Amurka da Russia ne kawai ke gaban Brazil a yawan wadanda annobar ta shafa.

    Masana sun ce rashin yi wa mutane gwaji ka iya jefa kasar zama a gaba-gaba wajen yawan masu cutar a duniya.

    Shugaba Jair Bolsonaro ya yi watsi da gargadin inda ya kwatanta korona da mura.

  4. Zimbabwe ta kulle dakin cin abinci na kasar China

    Kasar Zambia ta rufe wani gidan abinci mallakar 'yan kasar China a birnin Lusaka sakamakon rahotanni da ke nuna yadda ake nuna wa bakar fata wariya a China.

    Rahotanni dai sun ce gidan abincin ya ki amince wa wani dan Zimbabwe ya shiga domin cin abinci inda aka ayyana da shi da cdan kasar waje.

    Mutumin da aka hana shiga ya bayyana hanin da wariyar launin fata.

    Magajin Garin birnin Lusaka, Miles Sampa ya zargi masu gidan cin abincin da sayar da abincin da ake kira na China ba na Turai ba sabanin yadda doka ta amince.

  5. Matakan kare kai daga cutar korona

    Coronavirus
  6. Coronavirus: Mun dauko 'yan Nijar fiye da 2000 daga Turai

    Mahamadou Issoufou

    Asalin hoton, Getty Images

    Jamhuriyar Niger ta ce ta samu nasarar kwashe 'yan kasar kimanin 2000 da suka makale a kasashen Turai sakamakon annobar korona.

    Ministan labarai na kasar, Kalla Hankurau ne ya bayyana wa majalisar dokoki wadda ta nemi da ya bayar da bahasi kan inda aka kwana dangane da jigilar 'yan kasar.

    Kimamin mutum 1000 ne ke dauke da cutar korona a jamhuriyar ta Niger, inda mutum fiye da 50 suka mutu sakamakon cutar.

  7. Mataimakin shugaban Sudan ta Kudu ya kamu da korona

    Riek Machar

    Asalin hoton, Reuters

    Mataimakin shugaban Sudan ta Kudu, Riek Machar ya kamu da cutar korona.

    Mista Machar ya ce har yanzu cutar ba ta nuna alamu a tare da shi ba amma zai killace kansa har tsawon kwana 14.

    Matarsa wadda ita ce ministar tsaaron kasar, Angelina Teny da wasu masu ba su kariya su ma duk sun kamu da cutar.

    Mista Machar dai na kwamiti na musamman domin yaki da cutar korona.

    Adadin masu cutar a Sudan ta Kudu ya kai 288 inda mutum hudu suka mutu.

  8. Ina shan hydroxychloroquine domin maganin cutar korona - Trump

    Donald Trump

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Amurka, Donald Trump ya ce yna shan maganin maleriya na hydroxychloroquine domin kashe kwayar cutar korona duk da cewa jami'an lafiya na gargadi da yin hakan.

    Da yake magana a fadar White House, mista Trump ya shaida wa manema labarai cewa ya fara shan maganin a baya-bayan nan.

    "Na kimanin mako guda ina shan maganin kuma gani kyam, gani lafiya lau." ya fada cike da mamaki.

    Babu dai wata kwakkwarar shaida da ke nuna maganin na hydroxychloroquine ka iya warkar da cutar ta korona sannan masana magani sun yi gargadin cewa maganin ka iya gada wa mutum matsalar zuciya.

  9. Coronavirus: Ko Buhari da Ganduje sun raba gari ne?

    Buhari

    Asalin hoton, Presidency

    Gwamnatin Tarayya ta nuna rashin gamsuwarta da yadda ake samun sabani tsakanin matakan da take dauka kan yaki da korona da kuma matakan da wasu jihohi ke dauka a nasu bangaren.

    Wannan na zuwa ne bayan tsawaita dokar takaita zirga-zirga da gwamnatin ta yi a Jihar Kano da mako biyu gaba.

    A ranar Litinin ne shugaba Muhammadu Buhari ya tattauna da wasu gwamnonn jihohi ta Intanet kan batun yaki da cutar korona da kuma batutuwan da suka shafi tattalin arziki da tsaro.

    Sai dai Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nemi hadin kan jihohin, inda ya ce gwamnatin Tarayya na tufka wasu jihohin na warwarewa.

    A tattaunawarsa da BBC Malam Garba Shehu mai taimakawa shugaban kan harakokin watsa labarai ya shaidawa cewa abin takaici ne a ce gwamnati tana daukan matakan yaki da annoba amma ana samun matsalar hadin-kai.

    A jiya Litinin ne dai Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya ce ya amince da shawarwarin da wasu malamai suka ba shi na bayar da izinin yin Sallar Juma'a da kuma Idi.

    A wata sanarwa da Salihu Tanko Yakasai, mai bai wa gwamnan shawara kan kafafen watsa labarai ya fitar ta ce gwamnan ya bayar da umarnin ne bayan ya tattauna da wakilan Malamai 30 da kuma wasu jami'an gwamnatinsa ranar Litinin.

    Sai dai ya ce ba za a bari mutane su yi shagulgula ba lokacin Sallar Idi. yana mai cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da tabbatar da dokar kulle.

    Gwamnatin jihar ta bi sahun wasu jihohi ne wajen bari a gudanar da sallolin na Juma'a da na Idi.

  10. Trump ya bai wa hukumar lafiya ta duniya wa'adin kwana 30

    Donald Trump

    Asalin hoton, EPA

    Amurka Donald Trump ya bai wa Hukumar Lafiya ta Duniya wa'adin kwana 30 kan kodai ta fito da mafita ta gaggawa dangane da annobar korona ko kuma ya janye tallafin da Amurkaa ke bai wa hukumar baki daya.

    A wata wasika da ya aike wa hukumar, Trump ya ce Amurka za ta fice daga kasancewarta mambar hukumar baki daya abin da zai janyo wa WHO asarar biliyoyin daloli.

    Wasikar ta soki irin matakan da hukumar lafiyar ke dauka watanni shida da suka gabata lokacin da cutar korona ta barke.

    A ranar Litinin ne dai mista Trump ya bayyana shugaban hukumar, Tedros Adhanom a matsayin dan koren kasar China.

  11. Sojojin Najeriya sun 'kashe gomman 'yan Boko Haram'

    Boko Haram

    Asalin hoton, Getty Images

    Rundunar sojin Najeriya ta ce ta kashe gomman 'yan Boko Haram sannan ta kwace makamai masu yawa daga hannunsu kafin ta fatattake su.

    Rundunar wadda ta wallafa wannan sanarwa a shafinta na Twitter ta ce dakarun rundunar Lafiya Dole ne suka gudanar da wani samame a kan 'ya'ayn kungiyar ranar Lahadin da ta gabata a garin Gajigana na karamar hukumar Nganzai da ke jihar Borno.

    Wannan sanarwa dai na zuwa ne 'yan awanni bayan da wasu 'yan bindiga da ake kyautata zaton 'yan Boko Haram ne suka kai hari garin Daptchi da ke jihar Yobe, inda suka bude wuta irin na kan mai-uwa-da-wabi.