A biya ma'aikata albashin watan Mayu yanzu - Zulum

Wannan shafi na kawo muku bayanai da rahotanni kai tsaye kuma da dumi-duminsu dangane da annobar korona da ma wasu karin batutuwa da ke wakana a fadin duniya.

Rahoto kai-tsaye

Nasidi Adamu Yahaya and Umar Mikail

  1. Ƙasar Slovenia ta ce ta kawo ƙarshen cutar korona

    Mawaƙiya Bilbi

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Mawaƙiya Bilbi kenan take rera waƙa a kan dogon ginin Narodni Dom da ke Maribor na Slovenia. Ana yaɗa kaɗe-kaɗen a shafukan sada zumunta domin debe wa mutane kewa yayin dokar kulle

    Slovenia ta zama ƙasa ta farko a Nahiyar Turai da ta ayyana kawo ƙarshen cutar korona a hukumance.

    Ƙasar wadda ke da al'umma kusan miliyan biyu kuma mamba a Kungiyar Tarayyar Turai ta EU, ba ta samu waɗanda suka kamu da cutar da yawa ba a cikin mako biyu da suka gabata. A jumlace, ta samu mutum 1,464 da suka kamu da cutar da kuma 103 da suka mutu.

    Daga yanzu, ba za a kuma killace matafiya ba da suka shiga ƙasar daga ƙasa mamba a ƙungiyar EU.

  2. 'Cutar korona ka iya jawo asarar alade miliyan 10 a Amurka'

    Aladu

    Asalin hoton, Getty Images

    Kusan alade miliyan 10 ne za su rasa rayukansu nan da tsakiyar watan Satumba a Amurka sakamakon annobar korona, a cewar wani gargaɗi da masana'antar aladu ta ƙasar ta yi.

    Ƙungiyar mai suna National Pork Producers Council ta ce masu kiwon aladu da suka gaza kai dabbobinsu zuwa masana'antar kiwon dabbobi ba su da wani zaɓi illa su lalata su, idan kuma ba su yi hakan ba to manoma za su rasa wurin ajiyarsu da kuma kayayyakin aikinsu.

    Wuraren sayar da nama a Amurka sun kulle ko kuma sun rage samar da naman sakamakon annobar korona. A watan Afrilu, Shugaba Trump ya umarci kamfanonin sarrafa nama su ci gaba ayyukansu.

    Sai dai sarrafa naman alade ya yi ƙasa da kusan kashi 40%.

    Akwai kusan mutum 14,000 da suka harbu da cutar korona a ma'aikatun sarrafa nama a Amurka, yayin da kusan 54 suka mutu, a cewar wani rahoton CBS.

  3. Ba mu san inda likitocin China suke ba – Gwamnatin Najeriya

    Likitocin China a Najeriya

    Asalin hoton, Getty Images

    Gwamnantin Najeriya ta ce bai zama wajibi a kanta ba ta bayyana inda likitocin China suka shiga - waɗanda suka isa Najeriya a farkon bullar cutar korona a ƙasar - saboda ba ita ta gayyace su ba.

    Jaridar Daily Trust ta ruwaito Ministan Lafiya Osagie Ehanire yana bayyana cewa likitocin na China ba baƙin gwamnnatin Najeriya ba ne domin kuwa sun shiga ƙasar ne da bizar kamfanin gine-gine na China Civil Engineering Construction Corporation (CCECC).

    Ministan ya bayyana hakan ne ranar Alhamis a wurin taron manema labarai na kullum kan matakan da ake dauka na yaƙi da cutar.

    An yi ta ce-ce-ku-ce kan likitocin da suka isa Najeriya ranar 8 ga watan Afrilu sannan suka killace kansu na tsawon kwana 14 a wani wuri da ba a bayyana ba, kamar yadda dokar hukumar NCDC ta tanada.

    "Ina tunanin ba dukansu ne likitoci ba, na ji cewa wasu daga cikinsu injiniyoyi ne kuma ma'aikatan kamfanin CCECC," in ji ministan.

    Ya ƙara da cewa: "Ba Ma'aikatar Lafiya ce ta sauke su ba, saboda haka ba zai yiwu kodayaushe mu rika bayanin inda suke ba. Waɗannan liktoci sun ja hankalin mutane da dama, amma ma'aikatan kamfani ne kuma da bizar kamfanin suka shigo.

    "Zan so ku daina tambayata a kansu domin ba baƙinmu ba ne. Sai dai mun koyi wasu abubuwa daga gare su kan abin da ƙasarasu ta yi game da yaƙi da cutar korona."

  4. An 'kashe 'yan ta'adda hamsin' a Mozambique wannan watan

    M

    Asalin hoton, AFP

    Jami'an tsaron Mozambican sun kashe masu ikirarin kishin Musulunci kimanin 50 a yankin da ke da arzikin man fetur na Cabo Delgado cikin kwana goma, a cewar ministan cikin gidan kasar.

    Amade Miquidade ya ce an soma kaddamar da hare-hare kan masu tayar da kayar bayan ne ranar 4 ga watan Mayu a larduna bakwai, wadanda suka hada da Nangade, Quissanga, Mocimboa da Praia, Meluco, Muidimbe da kuma Mueda.

    Ministan ya zargi masu ikirarin kishin Musulunci da ji wa mutane rauni da sace jama'a da dukiyoyinsu da kuma yi musu kwanton-ɓauna.

    Mr Miquidade ya ce babban burin masu tayar da kayar bayan shi ne su "dauki hankalin mutane sannan su kawo rudani a tsakanin jama'a".

    Ya kara da cewa an kashe 'yan ta'adda takwas ranar Alhamis a lardin Quissanga.

    Mayakan kungiyar IS suna kai hare-hare a kauyuka da garuruwan da ke lardin, inda suka kashe daruruwan mutane sannan suka raba dubbai daga gidajensu tun daga shekarar 2017.

  5. Jihohin Arewacin Najeriya suna buɗe masallatai da coci-coci

    Bayanan sautiLatsa hoton da ke sama domin sauraron cikakken rahoton Ibrahim Isa

    A yau Juma'a ne wasu daga cikin jihohin arewacin Najeriya za su bude wuraren ibada da aka rufe na tsawon makonni saboda daƙile yaɗuwar cutar korona.

    Jihohin Borno da Adamawa da Gombe da Jigawa sun sassauta dokar wadda ta haramta yin taruka ciki har da na addini kuma yanzu mazauna yankunan za su iya zuwa masallatan Juma'a da majami'u.

    Kazalika an buɗe Babbar Kasuwar Dabbobi ta Adamawa bisa sharaɗin za a bi ka'idojin yin nesa-nesa da juna.

    Gwamnan Borno, Babagana Umara Zulum, ya bukaci 'yan jihar da kada su manta da kungiyar Boko Haram yayin addu'o'insu a sallolin dare, yana mai cewa "yanzu suna fama ne da annoba biyu"; Boko Haram da cutar korona.

    A nasa bangaren, Gwamna Badaru Abubakar na Jigawa ya ce:"Mun sharɗanta cewa duk waɗanda za su shiga masallaci sai sun wanke hannayensu sannan su saka takunkumi da kuma bayar da tazarar mita biyu (tsakanin sahun salla). Yawanci ana yi wa masallatan feshi kafin sallar Juma'a."

    Jihohin sun ce zuwa yanzu al'amura sun fara daidaituwar da za ta sa a sassauta tare da buɗe wuraren ibadar, kuma abin da ya sa suka yi hakan kenan.

    Wasu daga cikin limaman masallatan sun bayyana fatansu na ganin matakin ya taimaka wurin dakile cutar.

  6. 'Yan Afirka miliyan 250 ke iya kamuwa da cutar korona cikin shekara ɗaya

    Afirka

    Asalin hoton, Getty Images

    Masana kimiyya na Hukumar Lafiya ta Duniya sun ce kusan mutum miliyan 250 ne ke iya kamuwa da cutar korona a Afirka cikin wannan shekara.

    Nazarinsu wanda aka wallafa a mujallar BMJ Global Health ya ce tsakanin mutum dubu 150 zuwa dubu 190 ne kuma ke iya mutuwa sakamakon covid-19 a Afirka.

    Binciken ya ce mutum miliyan 5 da rabi kuma za su bukaci kulawar asibiti, lamarin da ka iya fin karfin harkokin kula da lafiyar da tuni ke fama da cutukan maleriya da tarin TB da kwayar cuta mai karya garkuwar jiki.

    Kwayar cutar na tafiyar hawainiya wajen yaduwa a Afirka idan an kwatanta da sauran kasashen duniya amma ana fargabar idan ta fantsama, nahiyar ba za ta iya da ita ba.

    Tuni dai cutar ta kunna kai cikin sansanonin mutanen da rikici ya raba gidajensu a Sudan ta Kudu.

  7. Barkanmu da Juma'a

    Nasidi Adamu Yahaya ne yake yi muku barka da Juma'a. Da fatan za ku kasance da mu domin sanin halin da ake ake ciki dangane da cutar korona, wacce ta addabi kasashen duniya.

    Baya ga batun wanna cuta, za kuma mu kawo muku sauran labarai da rahotannin da suka shafi rayuwarku, musamman daga kasashen Najeriya da Nijar da ma wasu sassan duniya.

    Kuna iya tafka muhawara da bayyana ra’ayoyinku a shafukanmu na sada zumunta a BBC Hausa.