Shugaban Bayern Munich Karl-Heinz Rummenigge ya bayyana matukar mamakinsa bayan dan wasan Jamus da RB Leipzig dan shekara 24 Timo Werner, wanda ake rade radin zai koma Chelsea, Liverpool ko Manchester United, ya ce ya gwammace komawa kasashen waje maimakon zaman Jamus. (Bild, via Metro)
Bayern Munich tana duba yiwuwar ware fiye da £50m domin dauko Manchester City Leroy Sane, a yayin da kwangilar dan wasan na Jamus mai shekara 24 take shirin karewa a karshen kakar wasa ta bana. (Telegraph)
Manchester United ta samu damar sayen dan wasan Faransa da Lyon mai shekara 23 Moussa Dembele, wanda kuma Chelsea ta so dauko shi, a kan £61.8m. (Todofichajes, via Express)
Manchester United tana son dauko dan wasa mai shekara 16 Jude Bellingham domin saka shi a cikin manyan 'yan wasa idan suka sayo shi daga Birmingham City a bazara. (Evening Standard)
Chelsea tana shirin sayar da dan wasan Faransa Tiemoue Bakayoko, mai shekara 25, a kan £31m amma Paris St-Germain ba ta son sayensa a kan sama da £26.5m. (Le10 Sport, via Star)