Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Masu zanga-zanga dauke da makamai sun fada wa majalisa a Amurka

Wannan shafi na kawo muku bayanai da rahotanni kai tsaye kuma da dumi-duminsu dangane da annobar korona da ma wasu karin batutuwa da ke wakana a fadin duniya.

Rahoto kai-tsaye

Nasidi Adamu Yahaya

  1. Shirinmu na korona, ina mafita.

    Za ku iya bibiyar shirinmu na korona: Ina mafita? a shafinmu na Facebook.

    Shirin yana wayar da kan jama'a a kan annobar korona da matakan kaucewa kamuwa daga cutar da makamantansu.

    Muna gabatar da shirin ne daga ranar Litinin zuwa Alhamis kowanne tsakanin karfe 12 zuwa daya na rana duk mako.

  2. Kasuwar 'yan wasan ƙwallon ƙafa

    Shugaban Bayern Munich Karl-Heinz Rummenigge ya bayyana matukar mamakinsa bayan dan wasan Jamus da RB Leipzig dan shekara 24 Timo Werner, wanda ake rade radin zai koma Chelsea, Liverpool ko Manchester United, ya ce ya gwammace komawa kasashen waje maimakon zaman Jamus. (Bild, via Metro)

    Bayern Munich tana duba yiwuwar ware fiye da £50m domin dauko Manchester City Leroy Sane, a yayin da kwangilar dan wasan na Jamus mai shekara 24 take shirin karewa a karshen kakar wasa ta bana. (Telegraph)

    Manchester United ta samu damar sayen dan wasan Faransa da Lyon mai shekara 23 Moussa Dembele, wanda kuma Chelsea ta so dauko shi, a kan £61.8m. (Todofichajes, via Express)

    Manchester United tana son dauko dan wasa mai shekara 16 Jude Bellingham domin saka shi a cikin manyan 'yan wasa idan suka sayo shi daga Birmingham City a bazara. (Evening Standard)

    Chelsea tana shirin sayar da dan wasan Faransa Tiemoue Bakayoko, mai shekara 25, a kan £31m amma Paris St-Germain ba ta son sayensa a kan sama da £26.5m. (Le10 Sport, via Star)

  3. Sabo Nanono zai ciyo bashin dala biliyan 1.2

    Gwamnatin Najeriya ta amince a karbo bashin dala biliyan daya da rabi domin zamanantar da aikin noma.

    Ministan noman kasar, Sabo Nanono, ya bayyana hakan a jawabin da ya yi wa manema labarai da ke fadar shugaban Najeriya ranar Laraba bayan kammala taron majalisar ministoci.

    Ministan bai yi cikakken bayani kan yanayin bashin ba da kuma inda za a karbo shi.

  4. Malaman Musulunci sun buƙaci a buɗe masallatan Juma'a a Kano

    Rahotanni daga jihar Kano da ke Najeriya sun ce wasu malaman addinin Musulunci sun bukaci gwamnatin jihar ta sake bude masallatan Juma'a domin a rika gudanar da salloli kamar yadda aka saba duk mako.

    Rahotannin sun kara da cewa malaman sun bayyana haka ne a wata takarda da suka aike wa gwamnatin jihar.

    Bukatar tasu tana zuwa ne a daidai lokacin da cutar korona take ci gaba da yaduwa a jihar ta Kano mafi yawan al'umma a Najeriya.

    Ma'aikatar lafiya ta jiar ta tabbatar cewa mutum 707 ne jumulla suka kamu da cutar korona a Kano ya zuwa ranar Laraba da daddare.

    Kazalika mutum 79 sun warke yayin da mutum 33 suka mutu.

  5. Mawaƙiya ta soki Buhari kan naɗa Ibrahim Gambari

    Fitacciyar mawaƙiyar nan ta Najeriya Yemi Alade ta tsoma baki cikin harkokin siyasa inda ta soki Shugaba Muhammadu Buhari bisa nada Farfesa Ibrahim Gambari a matsayin sabon shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa.

    A ranar Laraba ne aka nada tsohon ma'aikacin difilomasiyyar wanda kuma ya taba zama ministan harkokin wajen Najeriya lokacin mulkin sojin Janar Buhari, a matsayin shugaban ma'aikatan fadar ta shugaban kasa.

    Ya maye gurbin Malam Abba Kyari, wanda ya rasu a watan jiya sakamakon cutar korona.

    Farfesa Gambari yana da shekara 75 a duniya kuma hakan ne ya sa mawakiyar take adawa da nadin nasa.

    A sakon da ta wallafa a shafinta na Twitter, Alade ta ce " mai shekara 75 a matsayin shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa? Allah Ya kare Najeriya."

    Da ma dai wasu masu lura da lamura na ganin ya kamata a bai wa matashi mai jini a jika wannan mukami musamman ganin yadda yake bukatar aiki ba dare ba rana.

    Ko da yake masu sharhi na ganin Farfesa Gambari yana da dukkan kwarea da ake bukata wajen gudanar da aikin.

  6. Shin Farfesa Ibrahim Gambari zai iya kawo sauyi a gwamnatin Buhari ?

    Naɗin da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi wa Farfesa Ibrahim Gambari a matsayin sabon shugaban ma'aikatan fadar shugaban Najeriya ya bai wa mutane da dama mamaki.

    Ko da yake akasarin masu sharhin siyasa ba sa shakkar ƙwarewar Farfesa Gambari wajen aiwatar da ayyukansa, kasancewarsa tsohon fitaccen jami'in difilomasiyya kuma tsohon shugaban jami'a.

    Shin wadanne kalubale ne suke a gabansa? Wadane abubuwa suka kamata ya fi bai wa muhimmanci?

  7. WHO ta ce ba lallai ba ne duniya ta iya kawar da cutar korona

    Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO, ta yi gargadi cewa mai yiwuwa cutar korona ta samu wurin zama ke nan na dindindin kamar cutar nan mai karya garkuwar jiki HIV.

    Dokta Mike Ryan, wani babban jami'in hukumar yayi wannan gargadin, yana cewa a guji yin hasashen lokacin da cutar za ta wanye.

    Ya kara da cewa ko da an sami rigakafi, kawar da cutar na bukatar yin aiki tare na dukkan kasashen duniya wanda a cewarsa "gagarumin aiki ne".

    Kusan mutum 300,000 ne suka mutu daga cutar a fadin duniya, inda aka tabbatar da mutum miliyan 4.3 da ke dauke da ita.

  8. Mai shekara 98 ta warke daga cutar korona a Najeriya

    Wata tsohuwa mai shekara 98 na cikin karin mutanen da suka warke daga cutar korona a jihar Lagos da ke kudu maso yammacin Najeriya.

    Gwamnan jihar Babajide Sanwo-Olu ne ya bayyana hakan a sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter ranar Laraba.

    Tsohuwar tana cikin mutum ashirin da shida da suka warke daga cutar a ranar ta Laraba.

    Gwamna Sanwo-Olu ya ce mutum 13 cikin wadanda aka sallama mata ne, yayin da sauran sha ukun maza ne.

    A cewarsa, hakan ya kawo yawan mutanen da suka warke daga cutar zawa 528.

  9. Buɗewa

    Nasidi Adamu Yahaya ne yake yi muku barka da warhaka.

    Muna fatan ku kasance tare da mu tsawon wannan rana domin sanar da ku halin da duniya take ciki.

    Za mu kawo muku labarai da rahotannin da suka shafi rayuwarku, musamman kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Nijar da makwabtansu, har ma da sassan duniya.