Coronavirus: WHO ta ce ba lallai ba ne duniya ta iya kawar da cutar

An wallafa

Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO ta yi gargadi cewa tana iya yiwuwa cutar korona ta samu wurin zama ke nan na dindindin kamar cutar nan mai karya garkuwar jiki HIV.

Dokta Mike Ryan, wani babban jami'in hukumar yayi wannan gargadin, yana cewa a guji yin hasashen lokacin da cutar za ta wanye.

Ya kara da cewa ko da an sami rigakafi, kawar da cutar na bukatar yin aiki tare na dukkan kasashen duniya wanda a cewarsa "gagarumin aiki ne".

Kusan mutum 300,000 ne suka mutu daga cutar a fadin duniya, inda aka tabbatar da mutum miliyan 4.3 da ke dauke da ita.

Me WHO ta ce?

"Yana da muhimmanci mu sanar da kowa cewa: wannan cutar na iya zama daya daga cikin cututtukan da tilas al'umominmu su rayu da ita, kuma ba lallai ba ne a ga bayanta ba", inji Dr Ryan ga wani taron hukumar da aka yi a birnin Geneva.

"Har yanzu ana fama da cutar HIV - sai dai dole ta sa mun ia rayuwa da ita."