Masu zanga-zanga dauke da makamai sun fada wa majalisa a Amurka

Wannan shafi na kawo muku bayanai da rahotanni kai tsaye kuma da dumi-duminsu dangane da annobar korona da ma wasu karin batutuwa da ke wakana a fadin duniya.

Rahoto kai-tsaye

Nasidi Adamu Yahaya

  1. Ban kwana

    To a nan muka kawo shirin namu na bayanai da labarai kai tsaye. Da fatan za ku kasance da mu da safe idan Allah ya kai mu. Mun gode

  2. An yi zanga-zanga a Amurka kan dokar kulle

    Michigan

    Asalin hoton, Getty Images

    Daruruwan masu zanga-zanga dauke da makamai ne suka dirar wa ginin Capitol da ke jahar Michigan, inda suke bukatar gwamnan jahar da ya kawo karshen dokar kulle.

    Masu boren sun nuna goyon baya ga shugaba Donald Trump da ya yi kira ga jahohin Amurka da su bar jama'a su fito duk da masana sun ce hakan na da hadari.

    Jahar Michigan na daga cikin jahohin da suka fuskanci yawan mace-mace daga annobar korona. Ko a jahar Wisconsin kotun koli ta ki amincewa da tsawaita dokar kullen a ranar Laraba.

    Mr Trump ya soki babban jami'in da ke kula da hukumar cutuka masu yaduwa ta Amurka Dr Anthony Fauci, kan gargadin da ya yi a kan batun sassauta dokokin dakile cutar.

  3. Coronavirus ta sa an haramta wa ministoci sayen motoci a Namibia

    A wani sakon Twitter da ya wallafa, ofishin shugaba Hage Geingob na Namibia ya ce, shugaban kasar ya haramta wa ministoci da kuma jami'an gwamnati sayen sabbin motoci na tsawon shekara biyar, don a yi amfani da kudin wajen yaki da cutar korona.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

    Matakin zai iya kai wa ga ajiye dala miliyan 10.7 kamar yadda sakon ya bayana.

    Ya kuma kara da cewa za a kashe kudin ne ga bukatun gaggawa musamman a wannan lokacin da kasar ke fama da matsalar kiwon lafiya da ta tattalin arziki saboda korona.

    Haka kuma shugaban ya rage kudin alawus din man fetur.

    Mutum 16 ne kawai ke dauke da korona a kasar kuma ya zuwa yanzu babu wanda ya mutu.

    Kasar ta Namibia dai na da yawan mutane da ya kai miliyan 2.5.

    Ana bai wa kowanne minista da aka nada mota kirar Mercedes-Benz in ji kamfanin dillanci labarai AFP.

  4. Coronavirus: Mutane kadan ne za su halarci wurin ibada a Mozambique

    Gatty

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Mutane da dama ne suka halarci taron a bara domin ganin Pop

    Cocin Katolika da ke Mozambique ta ce za ta takaita zuwan mabiya addinin zuwa ziyarar ibada da aka saba yi duk shekara, wanda aka tsara yi a karshen wannan makon.

    An dai tsara zuwa wajen bauta na Lady Fatima da ke Namaacha a lardin Maputo da ke kusa da iyakar eSwatini.

    Wannan hukunci wani mataki ne na dakile yaduwar cutar korona.

    Fada Alberto Buque, wanda ke cikin kwamitin shirya bikin, ya ce dole ce ta janyo wadannan hane-hanen, yana cewa mabiya addinin Kirista za su iya bin wannan biki ta kafafen radiyo da talabijin da sauran kafafen sada zumunta.

    Fada Buque ya ce mutane kalilan ne za a bari su halarci taron, ciki har da babban Bishop na kasar.

    A sauran bukukuwan da ake yi, sama da mutum 15,000 ne ke halarta, daga cikin kasar ta Mozambique da kuma makwabtan kasashe.

  5. An samu mutuwar mutum na farko a Sudan ta Kudu saboda korona

    Hukumomi a Sudan ta Kudu sun ba da rohoton mutuwar farko a kasar saboda cutar korona.

    Akwai mutum sama da 230 da ke dauke da cutar a kasar.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

    Rahoton mutuwar na zuwa ne bayan an gano wasu 'yan gudun hijrah da ke zaune a sansanin 'yan gudun hijira mai cunkoso da ke kusa da babban birnin kasar Juba bayan an yi musu gwaji.

    Kungiyar ba da agaji ta Red Cross ta ce, yana da wahala dakile yaduwar cutar a wajen da kusan mutum 30,000 ke rayuwa, inda mutane uku ke amfani da gidan sauro guda daya.

    Akwai matakan tsaftace kai da ake dauka a wajen, amma yana da wuya ka iya nesanta mutanen da juna.

    Kungiyar ba da agaji ta Red Cross ta ce ta damu da yaduwar cutar korona a gidajen yari da kuma asibitoci da ke da cunkoson mutane.

    Sama da mutum miliyan hudu suka rabu da mahallansu saboda rikicin Sudan ta Kudu.

  6. 'Yan majalisar jam'iyyar adawa sun yi batan dabo a Zimbabwe

    Wasu lauyoyin kare hakkin dan adam a Zimbabwe sun ce har yanzu akwai uku daga cikin jami'an jam'iyyar adawa da ba a san inda suke ba.

    An dai ce an kama 'yan majalisar jam'iyyar MDC Joanna Mamombeda da Cecilia Chimbiri da Netsai Marov ne ranar Laraba, yayin da suke jagorantar wata zanga-zangar kan yadda gwamnati ke daukar matakan kariya daga cutar korona.

    Suna zanga-zanga kan zargin mutane na fama da yunwa yayin da ake cikin dokar kulle.

    Lauyoyin sun ce sun kasa gano inda aka boye mutane ukun a ofishin 'yan sandan, amma tuni sun shigar da kofrafi gaban kotu na neman umarnin matsa wa 'yan sanda su fito da su a gaban mutane.

    A wani sakon tiwita, ofishin jakadanacin Burtaniya a Zimbabwe ya shawarci hukumomi da zu bayyana inda mutane ukun suke, tare da bai wa jami'an tsaro shawarar su rika amfani da kundin tsarin mulkin Zimbabwe ko da yaushe.

    Kauce wa X, 1
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X, 1

    Ofishin jakadancin Amurka shi ma ya nuna damuwa kan al'amarin:

    Kauce wa X, 2
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X, 2

    Zimbabwe ta sanyan dokar hana zirga-zirgar da bata kai ta kawo ba, kuma an janye ta a ranar Lahadin da ta gabata.

  7. Coronavirus: Ina makomar kasashen masu arzikin mai?

    Getty

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumar makamashi ta duniya IEA ta ce ta fahimci gagarumin koma baya ga yawan man da kasashen da ba a kulla yarjejeniya da su ba ke samarwa.

    Rahoton da ta fitar ya nuna cewa annobar korona ta sa an rage bukatar man fetur sosai wanda ya shafi daukacin kasashen da ke samar da shi, duk da an saukar da farashinsa kasa warwas.

    Yarjejeniyar da kungiyar kasashen da ke da arzikin man fetur OPEC ta kulla da kuma wata kungiya da Saudiyya da Rasha ke jagoranta na nufin ko a wannan watan zai dada rage yawan man da za a samar.

    IEA ta ce kasashe kamar Amurka da Canada da ‘yan kasuwa ne ke da wuka da nama can ma labarin irin daya ne.

    To amma hukumar ta fahimci cewa matakin sassauta dokar kulle a kasashen duniya ya taimaka wuirn dawo da bukatar man fetur, duk da cewa kasashen ba su taba fuskantar faduwa ba irin wannan a tarihi.

  8. Coronavirus: Trump na shirin yanke alaka da China

    Reuters

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, Shugaban Amurka daga hagu na China daga dama, an dauki hoton a 2019

    Shugaban Amurka Donald Trump ya kara sukar yadda China ta tafiyar da annobar korona, yana barazanar kawo karshen alakarsa da China.

    "Akwai abubuwa da dama da za mu iya yi. Za mu iya yanke kowacce irin alaka da Cjina" Trum ya bayyana a wata tattaunawarsa da gidan talbijin na Fox.

    "Yanzu idan muka aikata hakan, menene zai faru?" Trump yake tambaya cikin san birgewa. "Za ka aje dala bilyan 500 idan ka yanke dukkan alaka."

    Wannan wata hujja ce ta zahiri da ke nuna wagegen gibin da Amurka ke da shi na rikicin kasuwanci tsakaninta da China.

    Amurka ta sha kokarin matsa wa China biyan diyya da ke da alaka da cutar korona, tana zargin ta da rashin fitar da bayanan da suka dace kan cutar. Sai dai China ta sha musanta wannan zargi.

  9. An tuhumi TikTok da saba doka kan bayanan kananan yara

    Getty

    Asalin hoton, Getty Images

    An zargi kamfanin da ya samar da Manhajar sada zumuntan nan ta TikTok da keta dokokin da suka shafi boye bayanai game da kananan yara a Amurka.

    Kamfanin ya taba biyan tarar dala miliyan shida a shekarar 2019, bayan amsa laifin cewa ya karbi bayanan yara 'yan kasa da shekaru 18 ba tare da izinin iyayensu ba.

    Sabon korafin da aka shigar ya hada da rashin mutunta yarjejeniyar da aka kulla da TikTok na goge duk wani hoton bidiyo da yara 'yan kasa da shekaru 13 ke dorawa a manhajar, da kuma kara tsaurara matakan neman izinin iyaye ga kananan yara kafin su iya anfani da manhajar.

    Mai magana da yawun kamfanin TikTok ta ce sun kuduri kiyaye bayanan masu anfani da manhajar ta su.

  10. Za a tasa keyar Vijay Mallya zuwa Indiya

    Getty

    Asalin hoton, Getty Images

    Wata kotu a Landon ta yanke hukuncin cewa hamshakin mai arzikin nan dan Indiya Vijay Mallya zai koma Indiya don fuskantar hukunci. Haka ma an hana shi izinin daukaka kara zuwa Kotun Koli.

    Mista Mallya wanda ya taba mallakar kamfanin Kingfisher beer da kuma Kingfisher Airlines ya je Birtaniya ne shekaru hudu da ta wuce, inda ya tara bashin dala biliyan daya a kansa.

    A yanzu yana fuskantar tuhume-tuhume da suka hada da yin hada-hadar kudade ba bisa ka'ida ba, zargin da ya musanta.

    Kafafen yada labarai a Indiya sun jinjina wa kokarin gwamnatin Indiya a kokarinta na sa kafar wando daya da sanannun yan kasuwa da ta ke zargi da almundahana.

  11. 'Amurka ka iya fuskantar hunturu mafi muni a tarihi'

    Reuters

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, An nada Dakta Rick Bright a matsayin shugaban sashen bangaren bincike mai zurfi kan kwayoyin cuta

    Wani babban likitan samar da allurar rigakafi a Amurka da aka tube daga mukaminsa a watan Afirulu, ya ce gwamnatin Trump bata shirya shawo kan annobar korona ba.

    Dakta Rick Bright shi ne ke jagorantar bangaren bincike mai zurfi kan kwayoyin cuta wadda aka bukaci ta samar da maganin da za a yi amfani da shi wajen dakile cutar.

    Ya ce "Amurka ka iya fuskantar mummunan hunturu a tarihi", kamar yadda bayanan da kafar yada labarai ta CNN ta samu suka bayyana.

    A makon da ya gabata ya shigar da korafin zargin kwarmata cewa an cire shi ne daga mukaminsa saboda ya nuna kin amincewa da amfani da hydroxychloroquine - wata kwayar magani da shugaban Amurka ya tallata - a matsayin maganin cutar korona.

  12. Kanun labaran da ke faruwa a duniya

    • Alkaluman da hukumomi suka fitar a Australia sun nuna an samu karuwar rashin aikin yi da kashi 6.2 cikin 100 saboda cutar korona.
    • Japan ta janye dokar kulle da ta sanya kan cutar Korona a mafi yawan yankunan kasar, saboda raguwar masu kamuwa da cutar.
    • New Zealand ta sake bude dubban kasuwanci a fadin kasar wanda ya kawo karshen dokar hana zirga zirga da aka Sanya a baya saboda cutar Korona.
    • Shaguna da manyan kantinan zamani da wuraren cin abinci na maraba da abokan huldarsu a karon farko tun karshen watan Maris.
    • Hukumar dakile cutuka masu yaduwa ta Najeriya NCDC ta ce mutum 184 sun sake kamuwa da cutar korona a fadin kasar.
    • Gwamnatin Najeriya ta amince a karbo bashin dala biliyan goma sha biyu domin zamanantar da aikin noma.
    • Fitacciyar mawaƙiyar nan ta Najeriya Yemi Alade ta tsoma baki cikin harkokin siyasar kasar inda ta soki Shugaba Muhammadu Buhari bisa nada Farfesa Ibrahim Gambari a matsayin sabon shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa.
    • Manchester United ta samu damar sayen dan wasan Faransa da Lyon mai shekara 23 Moussa Dembele, wanda Chelsea ta so dauko shi.
  13. TP Mazembe ta zama gwarzuwar gasar DR Congo

    Getty

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Kungiyar kwallon kafa ta TP Mazembe

    An bayyana kungiyar TP Mazembe a matsayin wacce ta lashe gasar kwallon kafa ta Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo, wanda ya kawo karshen kakar wasanni ta bana saboda annobar korona.

    Hukumar kwallon kafa ta kasar Fecofa ce ta bayyana hakan cikin wata sanarwa da ta fitar, tana cewa sun cimma wannan matsayar ne a ranar Laraba, kan kakar wasannin ta 2019/20 wadda cutar korona ta sanya aka dakatar karfi da yaji.

    TP Mazembe ce ke jan ragamar gasar kafin dakatar da ita.

    Fecofa ta tabbatar da faduwar kungiyoyin biyun karshe na gasar OC Bukavu Dava da AS Nyuki, zuwa rukuni na biyu, da kuma haurowar kungiyoyin biyun farko na rukuni na biyun zuwa rukuni na daya, wadanda suka hada da JSK da Etoile Jaune.

  14. Japan ta kara sassauta dokar kulle

    Japan ta janye dokar kulle da ta sanya sakamakon cutar korona a mafi yawan yankunan kasar.

    Kasar dai dta janye dokar ne saboda raguwar masu kamuwa da cutar.

    Firai minista Shinzo Abe ya shawarci mutanen yankunan da su ci gaba da sanya ido kan abin da ke faruwa a inda suke, su rinka sanya takunkumi idan za su fito waje, su kuma kasance masu bin dokar bayar da tazara tsakaninsu.

    Ya ce dokar kullen za ta ci gaba da aiki a birnin Tokyo, da kuma wasu manyan biranen kasar har zuwa karshen wannan watan da muke ciki.

    Har yanzu ana ci gaba da shawartar mutane da su guji cudanya da juna a wuraren shan barasa da gidajen rawa.

    Getty

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Firai ministan Japan Shinzo Abe
  15. Yadda manyan hafsoshin tsaron Najeriya suka saka takunkumi

    .

    Asalin hoton, @BashirAhmaad

    .

    Asalin hoton, @BashirAhmaad

    .

    Asalin hoton, @BashirAhmaad

  16. Covid-19: Al'amura na komawa daidai a New Zealand

    Getty

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Firaiminista Jacinda Ardern

    New Zealand ta sake bude dubban kasuwanci a fadin kasar, wanda ya kawo karshen dokar hana zirga-zirga da aka sanya a baya saboda cutar korona.

    Shaguna da manyan kantunan zamani da wuraren cin abinci na maraba da abokan huldarsu a karon farko tun karshen watan Maris.

    Masu gyaran gashi da masu aski sun fara aiki tukuru tun tsakiyar daren Laraba, domin yi wa wadanda suka kwashe makonni ba tare da gyara ba.

    Hukumomi a kasar sun ce hadarin kamuwa da cutar a yanzu ba shi da yawa sosai, amma suna shawartar mutane da su ci gaba da bin dokar ba da tazara tsakaninsu.

    Da take sanar da kasafin kudinta, gwamnatin kasar ta sanar da ware dala biliyan 30 domin taya da komadar da tattalin arzikinta ya yi.

    Za kuma a kashe kudade kan tsarin tallafin albashi, da na kiwon lafiya da kuma ababen more rayuwa.

  17. Mutum 34 sun sake mutuwa a Scotland

    Mutum 34 sun sake mutuwa a Scotland bayan sun kamu da coronavirus,

    Shugabar gwamnatin kasar Nicola Sturgeon ce ta bayyana haka a jawabinta na kullum.

    Hakan ya kawo adadin wadanda suka mutu a kasar zuwa 2,007.

    Sturgeon ta bayyana cewa mutum 14,117 sun kamu da cutar a Scotland.

    Akwai mutum 71 da ke dakin kula da marasa lafiya na musamman wadanda ke dauke da cutar ko kuma alamomin cutar, in ji ta.

  18. An umarci ma'aikatan WHO su fita daga Burundi

    Burundi

    Asalin hoton, Getty Images

    Burundi ta kori wakilin Hukumar Lafiya ta Duniya a kasar da kuma ma'aikatan lafiya uku daga kasar.

    A wata takarda da ba a saka wa hannu ba da ta fito daga ofishin kula da harkokin kasashen waje na kasar, takardar ta ayyana Dakta Walter Kazadi Mulombo da kuma wasu ma'aikatan lafiya a matsayin wadanda ba a bukatar zamansu a kasar.

    Ministan harkokin waje na Burundi Ezechiel Nibigira bai musanta fitar da wannan takardar ba a wata hira ta waya da BBC, amma wata majiya daga ma'aikatar harkokin waje ta kasar ta tabbatar da sahihancin takardar ga BBC.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

    Ma'aikatar ba ta bayar da dalilan korar jami'an daga kasarta ba.

    Ana sukar Burundi kan shirya zabe a daidai lokacin da annobar korona ke dibar rayukan mutane a fadin duniya.

    Mutum 15 ne suka kamu da cutar korona a kasar inda mutum daya ya mutu.

  19. Buhari ya kira taro kan matsalolin tsaro

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kira taron Majalisar Tsaro ta Kasa sakamakon rashin tsaro da ake fuskanta a wasu sassa na kasar.

    Mai taimaka wa shugaban kasar kan kafofin sada zumunta na zamani Bashir Ahmad ne ya wallafa hakan a shafinsa na Twitter.

    Mataimakin Shugaban Kasar Farfesa Yemi Osinbajo na cikin mahalarta taron da kuma manyan hafsoshin tsaro na Najeriya.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  20. An sake buɗe masallatai da majami’u a Borno

    .

    Asalin hoton, @PROFZULUM

    Gwamnatin jihar Borno ta sake bude masallatai da majami'u a jihar sakamakon gamsuwar da ta yi da yadda mazauna jihar ke bin dokokin kare kai daga kamuwa da cutar korona.

    Mataimakin gwamnan jihar kuma shugaban kwamitin yaki da Covid-19 a jihar wato Umar Usman Kadafur ne ya fitar da sanarwar inda ya ce za a iya ci gaba da gudanar da ibadu a masallatai da majami'u amma da sharadin bayar da tazara da juna da kuma saka takunkumin rufe fuska.

    Sai dai a sanarwar gwamnatin ta bayyana cewa ba za a gudanar da Sallar Idi ba saboda ba farilla ba ce, hakan na nufin ranar sallah mabiya addinin musulunci za su zauna a gida.

    A sanarwar, gwamnatin jihar na nan kan bakanta na haramta sayarwa da kuma shan barasa da sauran kayan maye a jihar inda gwamnatin ta sha alwashin hukunta wadanda suka karya doka.