Gwamnan jihar Jigawa a arewacin Najeriya Muhammad Badaru Abubakar ya ce mutum 20,000 za su iya kamuwa da cutar korona a jihar, kamar yadda hasashen kwararru ya nuna.
A wata hira da BBC, gwamnan ya bayyana cewa idan mutanen jihar suka bijire ba su bi ka'idojin da aka saka na kare kai daga kamuwa da cutar ba, adadin zai iya kaiwa dubu 20, idan kuma aka bi ka'idoji, adadin ba zai wuce 800 ba, idan aka yi sa a.
Gwamnan ya bayyana cewa an sassauta matakai na kulle a jihar inda cikin kananan hukumomi takwas da aka rufe sakamakon cutar an bude biyu.
Ya ce a yanzu sun dukufa wajen samar da karin wuraren killace jama'a da kuma jinyar masu fama da cutar, duba da wannan hasashe da aka yi.
Gwamnan ya kara da cewa a halin yanzu sauran kananan hukumomi shida da ke rufe za su iya gudanar da sallar Juma'a, amma akwai ka'idoji da aka saka wadanda masallatai za su bi.
Cikin matakan har da bayar da tazara a cikin masallaci da kuma wanke hannu kafin shiga.