Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Zan yi wa Buhari biyayya - Gambari

Wannan shafi na kawo muku bayanai da rahotanni kai tsaye kuma da dumi-duminsu dangane da annobar korona da ma wasu karin batutuwa da ke wakana a fadin duniya.

Rahoto kai-tsaye

Usman Minjibir, Mustapha Musa Kaita and Nasidi Adamu Yahaya

  1. An bude masallatai da coci-coci a jamhuriyar Nijar

    Za a bude masallatai da coci-coci a jamhuriyar Nijar bayan sassauta dokar kunle da za ta bai wa Musulmi da Kiristoci samun zarafin gudanar da ibadunsu daga yau Laraba.

    Gwamnatin Nijar din dai ta ce ta dauki wannan matakin ne bayan gano cewa al'amura sun fara daidaita dangane da bazuwar cutar ta korona.

    To sai dai gwamnatin ta ce dole ne a feshin kashe cututtuka a masallatan da coci-coci kafin masu ibada su fara amfani da wuraren.

    To sai dai gwamnatin ta ce otal-otal da filayen jirgin sama da iyakokin kasar za su ci gaba da kasancewa a rufe.

    Jmahuriyar Nijar dai na da mutum 854 da ke dauke da cutar korona, inda mutum 47 suka mutu.

  2. Covid 19: Singapore ta daure direban jirgi dan Amurka

    Kasar Singapore ta tura wani direban jirgin sama dan asalin kasar Amurka gidan yari na makonni hudu sakamakon karya dokar killacewa.

    Direban wanda matukin jirgin aika sako ne na FedEx, ya kamata tun a farkon watan Afrilu ya killace kansa a wani otel da ke filin jirgin sama na Singapore, amma ya saba dokar da aka saka inda ya shiga jirgin kasa domin zuwa zuwa shagunan cikin gari.

    A ranar Laraba Singapore ta kara samun sabin wadanda suka kamu da cutar 675 inda a halin yanzu sama da mutum 25,000 suka kamu da cutar, mutum 21 kuma suka mutu.

  3. Mike Pompeo ya nemi aiki tare da kungiyar Taliban

    Sakataren wajen Amurka, Mike Pompeo ya yi kira ga Taliban da kuma gwamnatin Afghanistan su yi aiki tare don gurfanar da mutanen da suka kai wasu miyagun hare-hare guda biyu gaban hukunci.

    Na farko wani harin bindiga ne kan wani asibitin haihuwa a birnin Kabul, inda aka far wa jarirai da masu jego da kuma ma'aikatan jinya. Mutum goma sha shida ne suka mutu.

    Na biyu kuma ya faru ne a gabashin Afghanistan, inda kungiyar IS ta ce wani dan kunar-bakin wakenta ya hallaka mutane sama da 20 a wani gidan makoki lokacin jana'iza.

  4. Boris Johnson ya sanar da sabbin matakai a Burtaniya

    Mako bakwai bayan fira ministan Burtaniya Boris Johnson ya sanar da daukar matakan da ba a saba gani ba don katse bazuwar korona, yunkurin sassauta kulle a Ingila ya fara aiki.

    Hada-hadar gidaje za ta ci gaba, inda aka bai wa masaya izinin kai wa dillalai ziyara da kuma zuwa ganin gidaje.

    Ana kuma sassauta tarnakai ta yadda mutane za su iya barin gidajensu don fita takaitaccen motsa jiki kuma an bari mutum biyu daga gidaje daban-daban na iya haduwa a waje, matukar za su ba da rata a tsakani.

    Mista Johnson ya kuma karfafa wa karin mutane gwiwa su koma bakin ayyukansu.

  5. Cutar korona ta bulla a sansanin 'yan gudun hijra na Sudan ta Kudu

    Jami'an lafiya a Sudan ta Kudu karon farko sun tabbatar da bullar korona a sansanonin mutanen da rikici ya raba da gidajensu.

    Mutum biyu sun kamu a wani sansani da ke Juba babban birnin kasar da kuma guda a Bentiu da ke arewacin kasar.

    Kwararru sun yi ta gargadi game da hatsarin da za a fuskanta idan kwayar cutar ta kunna kai cikin sansanoni masu cunkoso da ke dauke da kusan mutum dubu 200 a fadin kasar.

    Rikici tsawon shekaru ya bar Sudan ta Kudu da d'aya daga cikin tsarin kula da lafiya mafi rauni a fadin nahiyar Afirka.

  6. Gwamnan New York ya sanar da sassauta dokar kulle

    Gwamnan jihar California ya ba da sanarwar sassauta matakan kulle da aka kakaba wa jihar mafi yawan jama'a a Amurka.

    Gwamna Gavin Newsom ya ce ofisoshi da wasu gidajen abinci na iya budewa yanzu, matukar sun bi matakan kandagarki da aka shimfida.

    Ya ce "Wani babban kuskure da za mu yi game da wannan annoba, a daidai lokacin da muke sake bude harkoki, shi ne mu yi romon baka kan abin da hakan yake nufi."

    Lamarin ya zo ne bayan gargadin da daya daga cikin manyan masana cutuka masu yaduwa a kasar, Dr. Anthony Fauci ya yi cewa sake bude harkoki cikin sauri na iya janyo karin mace-mace da wahalhalu.

    Shugaba Trump ya buga sakon a Twitter da ke goyon bayan Elon Musk, Babban Jami'in kamfanin Tesla, da ya sake bude masana'antarsa ta hada motocin lantarki a Califonia, ta hanyar bijire wa ka'idojin da jami'an lafiya a jihar suka shimfida.

  7. Jair Bolsanaro na son a bude kasuwanci a Brazil duk da karuwa da korona ke yi

    Brazil ta samu kari mafi yawa na mutanen da suka mutu cikin kwana daya sanadin cutar korona tun bayan barkewar annobar.

    Ma'aikatar Lafiya ta ce mutum 881 sun rasu cikin sa'a 24 a kasar.

    Kwararru sun yi imani cutar za ta kara fantsama nan da 'yan makwanni kafin ta kai kololuwarta, barazanar da ka iya fin karfin harkokin kula da lafiyar Brazil.

    Alkaluma na ci gaba da hauhawa, sai dai daukin Brazil don shawo kan annobar a hargitse yake, da yawan gwamnonin jihohin kasar sun yi biris da tarayya, inda suke kara bullo da tsauraran matakai.

    Shugaba Jair Bolsonaro ya ce bazuwar kwayar cutar abu ne da ba za a iya kauce masa ba don haka jazaman ne harkokin kasuwanci su ci gaba saboda a kauce wa wani gagarumin koma-bayan tattalin arziki.

  8. Buhari zai nada mutumin da zai maye gurbin marigayi Abba Kyari

    A yau Laraba ne lokacin taron majalisar zartarwa ake sa ran Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari zai nada shugaban ma'aikatan fadarsa, tun bayan rasuwar Mallam Abba Kyari.

    A ranar 17 ga watan Afrilu ne dai Allah ya yi wa Mallam Abba Kyari rasuwa sakamakon cutar korona.

    Abba Kyari ya rasu ne a Legas, inda ya koma can bayan ya kamu da cutar korona domin ci gaba da jinya.

    Da ma rahotanni sun ce Abba Kyari yana fama da wata rashin lafiya kafin ya kamu da cutar korona, kuma masana harkar lafiya sun ce masu fama da wata cutar na daga cikin wadanda suka fi fuskantar hadarin mutuwa daga cutar ta korona.

    Abba Kyari ya kasance mutum mai karfin fada a ji a gwamnatin Shugaba Buhari.

    Dan asali jihar Borno ne da ke arewa maso gabashin kasar. Kyari tsohon dan jarida ne, kuma tsohon ma'aikacin banki, inda ya rike manya-manyan mukamai a wasu bankunan kasar.

    Yanzu abun jira agani shi ne ko mutumin da zai gaji wannan gogaggen ma'aikacin yana da irin haibar da marigayin yake da ita.

    'Yan kasar dai na ta faman hasashe dangane da mutumin da zai maye gurbin marigayi Abba Kyari, inda a yau din nan za a tabbatar da hasashen nasu ko kuma akasin haka.