Wannan shafi na kawo muku bayanai da rahotanni kai tsaye kuma da dumi-duminsu dangane da annobar korona da ma wasu karin batutuwa da ke wakana a fadin duniya.
Rahoto kai-tsaye
Usman Minjibir, Mustapha Musa Kaita and Nasidi Adamu Yahaya
Mu kwana lafiya
A nan muka zo karshen bayanan da muke kawo muku a wannan shafi na wannan rana. Sai ku kasance da mu gobe Alhamis domin samun sabbin labarai da rahotannin da suka shafi rayuwarku.
Kafin nan, za ku iya lekawa kasa don karanta labaran da muka kawo muku tun daga safiyar yau.
Kuna iya garzayawa shafukanmu na sada zumunta da muhawara don bayyana ra'ayoyinku.
Mu kwana lafiya.
Karin mutum 26 sun warke daga cutar korona a Lagos
Gwamnan jihar Lagos da ke Najeriya Babajide Sanwo-Olu ya ce an sallami karin mutum 26 daga cibiyar killace masu dauke da cutar korona bayan sun warke daga cutar ranar Laraba.
A sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter, Gwamna Sanwo-Olu ya ce mutum 13 cikin wadanda aka sallama mata ne, yayin da sauran sha ukun maza ne.
A cewarsa, a cikinsu akwai wata mata mai shekara 98 a duniya, wacce ta kasance mafi girman shekaru da ta kamu da cutar korona a jihar.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.
Karshen labarin da aka sa a X
Zan yi wa Buhari biyayya - Gambari
Sabon shugaban ma’aikata
a fadar shugaban kasar Najeriya, Farfesa Ibrahim Gambari ya ce zai yi wa Shugaba Buhari biyyaya tare da aiki tukuru.
A hirarsa da manema
labarai a fadar Aso Rock, Gambari ya ce “Shugaban kasa zan yi wa aiki ba wai
kasa baki daya ba”.
Dan shekaru 75, Farfesa
Gambari ya maye gurbin Malam Abba Kyari ne wanda ya rasu a watan da ya wuce
sakamakon kamuwar da cutar korona.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.
Karshen labarin da aka sa a X
Asalin hoton, Getty Images
Ko mutum zai iya ɗaukar korona ba tare da nuna wasu alamomi ba?
Masana a harkar lafiya sun ce mutum ka iya daukar cutar korona ba tare da jikinsa ya nuna masa wasu alamomi ba.
Hukumomin lafiya na gargadin mutane a kan rashin daukar matakan kariya inda suka ce kashi 80 cikin 100 na masu cutar kananan alamomi suke nunawa ko kuma ma babu wata alama.
Ga bayanin dan jarida mai sa ido a kan coronavirus Abdulbaki Jari.
Bayanan bidiyo, Coronavirus: Ko mutum zai iya daukar cutar ba tare da nuna alamomi ba?
Covid-19: Gwamna Zulum ya raba wa marasa galihu kayan abinci
Gwamnan jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya ya ce ya raba wa marasa galihu kayan abinci da zummar rage musu radadi sakamakon dokar kulle da aka sanya don dakile cutar korona.
A sakon da ya wallafa a Twitter, Gwamna Zulum ya ce bayan kammala rabon kayan abincin a kwaryar birnin Maiduguri, yanzu an soma raba kayan abincin a makwabtan kananan hukumumi irin su Jere.
Ya kara da cewa nan gaba kadan kwamitin rabon kayan abincin zai je wasu kananan hukumomin domin bai wa mutanen da ba su da hali tallafin.
Ya zuwa ranar Talata da daddare, mutum 188 aka tabbatar sun kamu da cutar korona a jihar ta Borno.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.
Karshen labarin da aka sa a X
'Kasashen duniya za su iya cinye ribar shekaru hudu da suka samu'
Asalin hoton, Getty Images
Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa matsin tattalin arzikin da kasashen duniya da dama suka fada a halin yanzu, kan iya sanadiyar cinye ribar da kasashen suka samu na shekaru hudu a jere.
Hasashen da MDD ta yi ya nuna cewa akwai yiwuwar mutum miliyan 30 su fada cikin matsanancin talauci a bana kuma akasarinsu a Afirka.
Ta kuma bayyana cewa kasashe masu tasowa na kashe karin kudaden ruwa kan bashi, wanda hakan zai iya ja kasashen su gaza kashe kudi kan matakan da ya kamata a dauka domin kare kai daga coronavirus.
MDD ta yi hasashen cewa arzikin kasashe masu karfin tattalin arziki a duniya zai ragu da kusan kashi 5 cikin 100.
Abinci biyar da ke kare garkuwar jiki
Masana ilimin abinci sun bayyana cewa akwai bukatar mutane su rika shan cin nau'in abinci da 'ya'yan itace domin inganta garkuwar jikinsu.
Masanan sun ce cin wadannan na'ukua na abinci zai yi tasiri sosai a jikin mutum ta yadda zai ba shi kariya daga cututtuka irin su cutar korona.
Hajiya Zainab Ujudud Shariff, wata masaniyar abinci da tsarin amfani da shi ta shaida wa BBC nau'ukan abincin da suka kamata a rika ci domin inganta garkuwar jiki:
Zogale
Cin zogale da koren tattasai da kuli-kuli ko kuma tafasa shi a yi sirace da shi sannan a sha ruwansa. Kazalika za a iya mayar da shi gari sannan a rika sanya shi a cikin shayi ana sha. Binciken kimiyya ya gano cewa zogaye yana gyara garkuwar jiki.
Kun san tarihin sabon shugaban ma'aikatan fadar shugaban Najeriya
Farfesa Ibrahim Gambari fitaccen malamin jami'a ne kuma ma'iakacin diflomasiyya da ya rike mukamai manya-manya a duniya da Afirka da kuma Najeriya.
An haifi Ibrahim Gambari a shekarar 1944, a Ilorin, jihar Kwara da ke arewa ta tsakiyar Najeriya.
Gambari ya yi sakandarensa a King's College da ke Lagos. Ya yi digirinsa na farko a London School of Economics inda ya kammala a 1968 kuma ya samu kwarewa a fannin harkokin kasashen waje.
Ya yi digirinsa na biyu da na uku a 1970 da 1974 a jami'ar Columbia University, New York d ake Amurka a fannin kimiyyar siyasa da harkokin kasashen waje.
Daga nan sai Farfesa Gambari ya koma jami'ar Ahmadu Bello University da ke Zaria a jihar Kaduna inda ya koyar daga 1977 zuwa 1980.
Farfesa Ibrahim Gambari ya kasance mutum na farko da ya zama Magatakardar Sakataren Majalisar Dinkin Duniya kuma bai ba da shawara na musamman ga Sakatare Janar na Tarayyar Afirka,
A shekarar 1984 zuwa 1985 Ibrahim Gambari ya zamo ministan harkokin wajen Najeriya.
Ibrahim Gambari ya sake zama ambasada kuma wakilin Najeriya na dundundun a Majalisar Dinkin Duniya a 1990 zuwa 1999.
A 1999 din dai Gambari ya kasance Shugaban Kwamitin gudanarwa na UNICEF.
A 2012 Gambari ya jagoranci kwmaitin wanzar da zaman lafiya na hadin gwiwa tsakanin Majalisar Dinkin Duniya da Tarayyar Afirka a Darfur daga 2010 zuwa 2012.
Gambari ya lashe karramar Shugaban Afirka ta Kudu, Jacob Zuma ga wadanda ba 'yan kasa ba a 2012.
Farfesa Ibrahim ya zamo shugaban jami'ar jihar Kwara na farko a 2013.
Ibrahim Gambari ne mutumin da ya kafa cibiyar bincike ta Savannah Centre for Abuja.
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Farfesa Ibrahim Gambari ya zama ministan wajen Najeriya lokacin mulkin sojin Janar Buhari
An bukaci Bankin Duniya da IMF su yafe bashin kasashe masu tasowa
Asalin hoton, Getty Images
Sama da 'yan siyasa 300 daga kasashe daban-daban na duniya suka bukaci Bankin Duniya da kuma hukumar bada lamuni ta duniya wato IMF da su yafe bashin da ake bin kasashe masu tasowa.
'Yan siyasar na wannan kiran ne domin kasashe masu tasowa da bashi yayi musu katutu su samu damar mayar da hankali wajen yaki da coronavirus.
Wadanda ke jagorantar wannan kudirin a duniya sun hada da Ilhan Omar wadda 'yar siyasa ce a Amurka da kuma Bernie Sanders wanda tsohon dan takarar shugabancin kasar Amurka ne.
Sun bayyana cewa wannan taimakon da ake bukatar bankin duniya da IMF su yi, wani abu ne da zai rage karuwar talauci da yunwa a wadannan kasashe.
Lebanon za ta kara saka dokar kulle a kasar
Kasar Lebanon za ta kara saka dokar kulle a na kwanaki hudu sakamakon samun sabbin mutum 100 da suka kamu da cutar a fadin kasar.
A makon da ya gabata ne dai gwamnatin kasar ta fara janye takunkumin da ta saka inda tuni gidajen sayar da abinci da shagunan aski suka fara budewa, sai dai a halin yanzu dole za su sake rufewa.
An yaba wa gwamnatin kasar dangane da yadda ta tunkari cutar bayan bullarta a kasar inda mutanen da suka mutu ba su haura 30 ba.
Fiye da mutum 4,000 sun kamu da korona cikin wata daya a Najeriya
Asalin hoton, CDC
Adadin wadanda suka kamu da coronavirus a Najeriya ya karu da sama da mutum 4,000 cikin wata daya.
A ranar 12 ga watan Afrilun 2020, hukumar da ke yaki da cutuka masu yaduwa NCDC ta bayyana cewa jumullar mutum 323 ne suka kamu da cutar coronavirus tun bayan barkewarta.
Sai dai a jiya Talata 12 ga watan Mayun 2020, hukumar ta tabbatar da cewa jumullar mutum 4,787 ne suka kamu da cutar, wannan na nufin an samu karin mutum 4,464 cikin wata daya da suka kamu da cutar.
Haka zalika adadin wadanda suka mutu sakamakon cutar ya karu da kusan mutum 148, inda a watan da ya gabata mutum 10 ne aka shaida sun mutum kamar yadda a sanar a ranar 12 ga watan Afrilu.
Sai dai a wani bangaren kuma an samu karin mutanen da aka sallama ko kuma suka samu sauki daga cutar da kusan mutum 874 kamar yadda hukumar NCDC ta sanar a ranar 12 ga watan Mayu.
Atiku da Saraki sun taya Gambari murna
Jama'a da dama musamman a shafukan sada zumunta na taya sabon shugaban fadar Najeriya Farfesa Ibrahim Gambari murna kan sabon mukamin da shugaba Buhari ya ba shi.
Cikin masu murnar har da Tsohon Mataimakin Shugaban Najeriya Atiku Abubakar da kuma Tsohon Shugaban Majalisar Dattijai Bukola Saraki.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.
Karshen labarin da aka sa a X, 2
Merkel ta gargadi Jamus kan sassauta dokar kulle
Asalin hoton, Getty Images
Shugabar Gwamnatin Jamus Angela Merkel ta gargadi kasar kan cewa kada a yi sauran bude kasar domin idan aka yi gaggawar yin hakan, za a mayar da hannun agogon baya.
Ta bayyana cewa idan aka kuskura aka bude kasar, duk kokarin da aka yi na dakile yaduwar coronavirus zai bi ruwa.
An yabi kasar Jamus matuka sakamakon yadda ta tunkari cutar ta coronavirus ta hanyar yin gwaje-gwaje masu yawa ga mutane a duk rana da kuma saka dokar hana fita wanda hakan ya taimaka wajen rage yaduwar cutar da kuma mace-mace.
A wannan makon dai, an bayar da umarni ga jihohi 16 na kasar kan cewa su sassauta takunkumin da suka saka domin bayar da dama ga shaguna su bude da kuma makarantu.
'Mutum 20,000 ka iya kamuwa da korona a Jigawa'
Asalin hoton, Awwal D Sankara
Gwamnan jihar Jigawa a arewacin Najeriya Muhammad Badaru Abubakar ya ce mutum 20,000 za su iya kamuwa da cutar korona a jihar, kamar yadda hasashen kwararru ya nuna.
A wata hira da BBC, gwamnan ya bayyana cewa idan mutanen jihar suka bijire ba su bi ka'idojin da aka saka na kare kai daga kamuwa da cutar ba, adadin zai iya kaiwa dubu 20, idan kuma aka bi ka'idoji, adadin ba zai wuce 800 ba, idan aka yi sa a.
Gwamnan ya bayyana cewa an sassauta matakai na kulle a jihar inda cikin kananan hukumomi takwas da aka rufe sakamakon cutar an bude biyu.
Ya ce a yanzu sun dukufa wajen samar da karin wuraren killace jama'a da kuma jinyar masu fama da cutar, duba da wannan hasashe da aka yi.
Gwamnan ya kara da cewa a halin yanzu sauran kananan hukumomi shida da ke rufe za su iya gudanar da sallar Juma'a, amma akwai ka'idoji da aka saka wadanda masallatai za su bi.
Cikin matakan har da bayar da tazara a cikin masallaci da kuma wanke hannu kafin shiga.
Kusan yara 1,000 za su iya mutuwa kullum a Najeriya – UNICEF
Asusun Kula da Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) ya yi gargadin cewa akwai yiwuwar yara 'yan kasa da shekara biyar fiye da 950 za su iya mutuwa a kullum a Najeriya sakamakon yadda cutar coronavirus ke kawo cikas da kuma kokarin gurgunta bangaren kiwon lafiya.
Asusun ya bayyana cewa za a iya samun irin wadannan mace-mace a kasar muddun ba a dauki matakai na gaggawa ba.
A wani bincike da jami'ar Johns Hopkins ta gudanar, ya nuna cewa kusan yara 6,000 za su iya mutuwa a kullum a fadin duniya.
An bayyana cewa kuma za a iya samun mutuwa wajen haihuwa na kusan mutum 6,800 a Najeriya a watanni shida masu zuwa.
Coronavirus a Najeriya: Masu cutar sun karu zuwa 4,787
Hukumar da ke dakile cutuka masu yaduwa ta Najeriya, NCDC ta ce an kuma samun mutum 146 da suka kamu da cutar korona a kasar, don haka yanzu yawan masu cutar 4787.
Alkaluman da hukumar ta fitar a daren Talata na cewa karin masu cutar 57 sun warke a ranar, kuma da wannan adadin mutanen da suka warke daga cutar 959 a fadin Najeriya.
Har yanzu Legas ce kan gaba a jihohin da suka fi yawan masu korona, inda aka sake samun mutum 57 da suka kamu.
Ita ma jihar Kano, an samu mutum 27 sabbin kamuwa da korona, don haka yawan masu cutar a Kano ya kai 693.
Haka kuma, alkaluman NCDC sun nuna cewa Allah Ya yi wa mutum takwas rasuwa a cikin sa'a 24 da ta wuce sakamakon annobar a fadin Najeriya.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.
Karshen labarin da aka sa a X
Hotunan taron Majalisar Zartarwa Ta Tarayya a yau
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari yayin da ya ke jagorantar taron Majalisar Zartarwa Ta Tarayya a Abuja.
Cikin mahalarta taron har da sabon shugaban ma'aikata na fadar wato Farfesa Ibrahim Gambari.
Asalin hoton, @BashirAhmaad
Asalin hoton, @BashirAhmaad
Asalin hoton, @BashirAhmaad
Shirin Korona Ina Mafita kai tsaye a shafinmu na Facebook
Shigar Farfesa Ibrahim Gambari Fadar Shugaban Najeriya
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.
Karshen labarin da aka sa a X
Labarai da dumi-dumi, Farfesa Ibrahim Gambari ne mutumin da ya maye gurbin Abba Kyari
Asalin hoton, Twitter
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nada Farefesa Ibrahim Gambari a matsayin shugaban ma'aikata na fadarsa.
Sakataren gwamnatin kasar Boss Mustapha ne ya fitar da sanarwar kafin fara zaman majalisar zartarwa ta tarayya a safiyar yau.
Tun a jiya Talata aka yi ta ce-ce-ku-ce musamman a kafafen sada zumunta kan cewa akwai yiwuwar a bai wa Farfesa Ibrahim Gambari mukamin shugaban ma'aikata Fadar Shugaban Najeriya.