Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

'Ma'aikatan lafiya kusan 1,000 sun kamu da cutar korona a Afirka'

Wannan shafi yana kawo muku labarai da bayanai kai tsaye dangane da irin wainar da ake toyawa a Najeriya da ma sauran sassan duniya kan annobar korona da sauran batutuwa.

Rahoto kai-tsaye

Usman Minjibir, Nasidi Adamu Yahaya and Buhari Muhammad Fagge

  1. Ana samun karuwar mace-macen dabbobi a arewacin Najeriya

    A yayin da ake ta samun rahotannin mace-macen mutane a sassa daban-daban na arewacin Najeriya, wasu makiyaya sun ce su ma dabbobi na mutuwa barkatai a halin yanzu a wasu sassan yankin.

    Shugaban kungiyar matasa makiyaya na shiyyar arewa maso gabashin Najeriyar, Abdurrahman Buba Kwacham, ya shaida wa BBC cewa, sai da suka gudanar da bincike sannan suka gano cewa a yanzu haka ana asarar dabbobi na fitar hankali.

    Ya ce, dalili kuwa shi ne mutane sun kiwota dabbobi masu yawa na tsawon lokaci amma idan sun je kasuwa domin su siyar ba bu kasuwa, sannan kuma su masu dabbobin ba su da wadataccen abincin da zasu rinka ba wa dabbobin.

    Abdurrahman Buba Kwacham, ya ce " Ba zan iya cewa ga adadin dabbobin da suka mutu ba musamman a jihohin Adamawa da Zamfara da Kano da Jigawa da Sokoto da Kebbi da kuma Kaduna, Allah ne kadai ya san adadinsu".

  2. Yau ce ranar tuna wa da ma'aikatan jinya ta duniya

    A yayin da ake ci gaba da fama da annobar korona a duniya, yau Talata ce ranar ma'aikatan jinya ta duniya.

    Wannan ranar ce kuma ranar da ake tuna wa da cika shekaru 200 da haifar Florence Nightingale- wata ma'aikaciyar Jinya 'yar Burtaniya da ta taimaka wa sojoji a lokacin yakin Crimea.

    Kungiyoyin da ke wakiltar ma'aikatan Jinya sun nuna damuwarsu kan yadda ake musu a wannan lokaci da duniya ke fama da annoba har a kasashen da ake gani suna da arziki.

    Sun ce akwai gazawa wajen gwaje-gwaje a asibitoci da karancin kayayyakin kariya wato PPE, da kuma rashin tallafa musu a bangaren lafiyar kwakwalwa saboda damuwar da suke shiga, ganin sune a gaba-gaba a wannan yakin.

    Kungiyar ma'aikatan jinya ta duniya ta yi gargadi cewa suna cikin hadarin karar da ma'aikatansu a lokacin da duniyar tafi bukatarsu.

  3. China za ta yi wa mutum miliyan 11 gwajin korona a kwana 10

    China na shirin yin gwajin cutar korona ga dukkan mutanen birnin Wuhan – mutum miliyan 11 – bayan kara samun sabbin rahotannin bullar annobar a birnin.

    Kafar yada labaran kasar ta ce, hukumomin za su gudanar da wannan gwajin ne cikin kwanaki 10 kacal.

    An samu akalla sabbin mutum biyar da suka kamu da cutar a yankin – wanda su ne masu dauke da cutar da aka samu cikin sama da wata daya a birnin – wurin da nan ne cutar ta samo asali.

    Ana sake bude wurare a hankali a birnin bayan shawo kan wannan annoba da ta barke a baya.

  4. Adadin masu cutar korona a Najeriya na neman kai wa 5000

    Hukumar da ke dakile yaduwar cutuka ta Najeriya, NCDC ta ce ya zuwa daren ranar Litinin, yawan wadanda suka kamu da cutar korona a kasar ya kai 4641, inda 902 suka warke kuma aka salleme su sannan mutum 150 suka rasu.

    Wannan dai ya biyo bayan samun karin mutum 242 da hukumar ta yi a ranar Litinin.

    Jihar Legas da Kano da Katsina da kuma Kaduna ke saman jadawalin sabbin masu dauke da cutar amma har yanzu Jihar Legas ce ke kan gaba a jumillar

  5. An tsawaita dokar kulle a Kano

    Gwamnatin jihar Kano ta tsawaita dokar kulle da gwamnatin tarayya ta sanya wa jihar na mako biyu.

    Yanzu haka Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya ce ya kara mako guda kan makonni da gwamnatin tarayyar ta sanya da manufar ganin cutar korona ba ta yadu a jihar ba.

    Kwamishinan yada labarai na jihar, Muhammad Garba ya ce an cimma matsayar tsawaita dokar ne tsakanin jami'an gwamnatin tarayya da na jiha da ma kwararru kan harkar lafiya.

    A wata sanarwa, Malam Muhamamd Garba ya kara da cewa "gwamnati na sane da irin radadin da jama'a ke ji sakamakon dokar kullen amma muna jan hankalin jama'a da su kwantar da hankalinsu domin gwamnatin na kokarin ganin ta takaita yaduwar wannan cuta."

    Tsawaita lokacin dai na zuwa ne kwana daya bayan da wa'adin mako biyu da gwamnatin tarayyar kasar ta sanya wa jihar ta Kano ke karewa.

    A ranar Litinin ne dai gwamna Ganduje ya sanar da kaddamar da shirin raba takunkumin fuska ga 'yan jihar, wanda hakan ke nufin bayan dokar kullen, sanya takunkumin ne zai zama wajibi.

    Adadin mutanen da aka tabbatar sun harbu da cutar korona a Jihar Kanon dai sun kai 666, a cewar ma'aikatar lafiya ta jihar.

  6. Ma'aikata za su koma aiki a Rasha

    Masu aikin gine-gine da manoma da ma’aikatan kamfanoni a Rasha za su koma bakin aiki a yau, kwana daya bayan shugaba Putin ya ba da sanarwar fara sassauta dokar hana zirga-zirgar da aka sanya saboda cutar korona.

    An tilasta amfani da takunkumi da kuma safar hannu a tashoshin ababan hawa da shaguna a birnin Mascow, inda nan ne rabin masu dauke da cutar a kasar suke.

    To sai dai wadanda za su iya aiki daga gida an ba su damar ci gaba da hakan.

    Shugaba Putin ya ba da wannan sanarwa ne bayan samun rahoton adadin masu dauke da cutar mafi yawa da aka taba samu a rana guda a Rasha, tun bayan bullar annobar.

  7. Kun san tsawon lokacin da ake dauka kafin warkewa daga cutar korona?

    Yayin da cutar korona ke ci gaba da yaduwa a duniya, masana sun yi bayanin tsawon lokacin da mutane ke ɗauka kafin su warke daga cutar.

    A wani bincike da suka yi an gano cewa wasu kan warke cikin mako biyu wasu kuma har sai sun kai wata uku. Kalli wannan bidiyon domin ganin cikakken bayanin.

  8. Ba zan sake kulla yarjejeniya da China ba - Trump

    Shugaba Trump ya ce ba shi da ra'ayin sake cimma yarjejeniyar kasuwancin wucin gadin da ya cimma da China a watan Janairu.

    Mista Trump ya yi wannan maganar ne a lokacin da 'yan jarida suka jefa masa tambaya kan rahotan da jaridar China ta wallafa da ke cewa wasu mashawarta gwamnatin Beijing sun bukaci a sake sabuwar tattaunawa da Amurka.

    A karkashin yarjejeniyar, Amurka ta amince ta dage duk wasu karin haraji a kan kayayyakin China zuwa nan gaba, yayin da Chinar ta alkawarta kara dala biliyan dari biyu na kudaden kayayakin da take saye a Amurka a cikin shekaru biyar.

  9. Coronavirus: India za ta bude zirga-zirgar jiragen kasa

    India za ta soma dawo da jiragen kasa a yau Talata, yayin da kasar sannu a hankali take sassauta dokar hana zirga-zirga.

    Jirage za su ke kai komo sau 30 daga birnin kasar na New Delhi zuwa Mumbai da Bangalore da Chennei.

    Ma'aikatar layin dogon kasar ta ce za a bukaci Fasinjoji su sanya takunkumi da kuma yi musu gwaji kafin su hau jirgin, mutane da masu gwada wata alamar cuta ba kawai za a bari su hau jirgin ba.

    Layin dogon Indiya dai shi ne mafi girma a duniya kuma jiragensu na jigilar akalla mutum miliyan 20 a duk rana.

    Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da a jiya Litinin kasar ta India ta tabbatar da da samun mutane mafi yawa da suka kamu da cutar korona inda mutum 4, 213 ma'aikatar lafiyar kasar ta rawaito sun kamu.

    Ya zuwa yanzu akwai kusan mutum dubu 50 da suka kamu da cutar a kasar inda mutum dubu 20 suka warke sai kuma 2, 206 suka mutu.

  10. Shugaban Brazil na son a bude shagunan gyaran jiki da gidajen motsa jiki

    Shugaban Brazil, Jair Bolsonaro ya bukaci a bude shagunan gyaran jiki, wurin motsa jiki da shagunan aski wanda ya ce su ma ayyukansu na da muhimmanci.

    Ya ce wajibi ne a daidaita yaki da cutar korona da ceto ayyukan mutane.

    Lokacin da aka mika tambaya ga ministan lafiyar kasar, Nelson Teich, kan wannan batu, ya amsa cewa ba shi da masaniya a kan shawarar da shugaban ke yankewa.

    Mista Bolsonaro na wannan batu ne a dai-dai lokacin da alkaluman mutane da cutar a hallaka a Brazil suka karu da 400 - A jimillance sun zarce dubu 11,500.

  11. Coronavirus: Iran za ta bude masallatai saboda goman karshe

    Iran za ta sake bude dukkanin masallatan kasar a yau Talata a wani mataki na sasauta dokar kulle.

    Rahotanni sun ce aa a bude masallatan na kwanaki uku ne kawai domin samun damar ibada a cikin dare masu daraja na watan Ramadan. sannan za a bayar da damar ibadar ne kawai na tsawon sa'a biyu, sannan mutane za su sanya takunkumi da safar hannu da kuma bai wa juna tazara.

    Watanin biyu da suka gabata aka rufe masallatai a kasar lokacin da aka soma samun barkewar cutar korona, ko daya ke a makon daya gabata an sake bude wasu masallatai amma a yankunan da cutar ba ta yadu sosai ba.

    Ma'aikatan Lafiya sun sha gargadi cewa dage dokokin yakar wannan annoba a yanzu ka iya jefa al'ummacikin wata sabuwar barazanar barkewar cutar.