Shugaban kwamitin ilimi mai zurfi na majalisar wakilai na Najeriya Aminu Suleiman Goro ya yi kakkausar suka game da shirin gwamnatin kasar na ciyar da 'yan makaranta a faɗin kasar.
A wata hira da ya yi da BBC, Aminu Suleiman Goro ya ce babu yadda za a yi shirin ciyar da 'yan makaranta a ko ina a duniya a ce an manta da ma'aikatar ilimi ta kasar.
Dan majalisar ya ce idan aka damka aikin a hannun ma'aikatar ilimi, aikin zai ta fi tafiya daidai la'akari da cewa suna da kididdigar yawan 'yan makaranta a ko wacce jiha cikin jihohin Najeriya.
"Ina da tabbacin ma'aikatar ilimi ta Najeriya ba ta san komai kan wannan shirin ba, haka mu ma kwamitin ilimi, yadda ko wa ke jin maganar a kafar sadarwa haka mu ma muka ji," In ji shugaban kwamitin ilimin.
Ya kuma bayyana cewa shi kansa shirin abu ne mai kyau saboda an yi ne domin a kwadaita wa waɗanda ke ganin ilimin zamani ya musu tsada, da kuma karfafa gwiwar wadanda ke zuwa amma ba su da karfi sosai.
"Tun da aka shigo da tsarin a farko, ofishin mataimakin shugaban kasa da kuma gwamnonin jihohi ne ke gudanar da shirin tsakaninsu, wanda kuma ba alhakin ofin ba ne gudanar da wannan aiki.
Suna aiki ne bisa rahoton da gwamnonin jihohi suka ba su, saboda haka wasu gwamnonin - ban ce duka ba - wasu sun dauki shirin ne kawai tamkar wata dama daga gwamnatin tarayya," ji Aminu Suleiman.