Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

'Ma'aikatan lafiya kusan 1,000 sun kamu da cutar korona a Afirka'

Wannan shafi yana kawo muku labarai da bayanai kai tsaye dangane da irin wainar da ake toyawa a Najeriya da ma sauran sassan duniya kan annobar korona da sauran batutuwa.

Rahoto kai-tsaye

Usman Minjibir, Nasidi Adamu Yahaya and Buhari Muhammad Fagge

  1. Rufewa

    A nan muka zo karshen labarai da rahotannin da muke kawo muku a wannan shafin. Sai ku tare mu ranar Laraba domin sanin halin da duniya ke ciki.

    Za ku iya ci gaba da karanta labarai da sauran abubuwan da suka shafi rayuwarku a bbchausa.com, ko ku tafka muhawara a shafukanmu na sada zumunta.

    Mun gode

  2. Najeriya: 'Yan bindiga sun kori mutum dubu 23 daga gidajensu

    Hukumar Kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce kusan mutane dubu 23 ne tashe-tashen hakulla suka tilastawa barin garuruwansu a shiyyar arewa-maso yammacin Najeriya zuwa cikin Nijar tun daga watan jiya na Aprilu.

    Ta ce galibin mutanen sun kaura ne daga jihohin Sakkwato da Zamfara da kuma Katsina.

    Wannan bayanin dai na zuwa ne yayin bayanai daga jihar Katsina ke cewa ‘yan bindinga sun kai hare-hare a kauyukan masu yawa a jihar cikin kwanakin nan.

  3. An soma yi wa 'yan jaridar White House gwajin cutar korona

    Fadar shugaban Amurka White House ta soma yi wa 'yan jaridar da ke dauko rahotanni a fadar gwajin cutar korona.

    'Yan jaridar da ke dauko rahotanni kan shugaban kasar sun mika kansu inda aka yi musu gwajin cutar, abin da ba ya wuce minti 15 a samu sakamakonsa.

    Duk cikinsu babu wanda ya kamu da cutar, a cewar mai bayar da shawara kan sha'anin tsaro na kasa a White House Robert O'Brien.

    Biyu daga cikin ma'aiakatan fadar White House sun kamu da cutar. Ranar Litinin, Shugaba Donald Trump ya bukaci dukkan mutumin da ke shiga bangaren West Wing na White House ya sanya makarin fuska.

  4. Likitar da ta gano mai dauke da cutar korona na farko a Najeriya

    Wata likita mace a jihar Legas Alison Amarachi Karen, ce wadda ta fara gano mai dauke da cutar korona a Najeriya.

    Likitar ta bayyana yadda ta gano haka bayan ta lura cewa ba zazzabi ba ne ba shanyewar ruwan jiki ba ne.

  5. Covid-19: Bayanai na baya-bayan nan kan cutar a duniya

    Bari mu duba bayanai na baya-bayan nan kan cutar korona a duniya:

    • A Amurka, babban mai bayar da shawara kan lafiya Dr Anthony Fauci ya yi gargadi kan matakin da gwamnati take son dauka na sake bude kasar nan ba da jimawa ba inda ya ce watakila alkaluman mutuwar da ake yi a kasar sun fi 80,000
    • Firai Ministan India Narendra Modi ya kaddamar da shirin bayar da agaji na $266bn wanda za a bai wa 'yan kasar da zummar rage musu radadin da suke ciki sakamakon cutar korona.
    • Yanzu Rasha ita ce kasa ta biyu da ta fi fama da cutar korona a duniya bayan Amurka, inda mai magana da yawun Shugaba Vladimir Putin ya kamu da cutar.
    • An samu karin masu kamuwa da cutar korona a Koriya ta Kudu abin da ake dangantawa da wani gidan rawa da aka bude a Seoul
    • A kasar Spaniya, matar nan mai shekara 113 a duniya - wacce aka yi amannar cewa ita ce mafi tsufa a kasar - ta warke daga cutar korona.
  6. Yaushe ake sa ran samun riga-kafin cutar korona ?

    Masana a harkar lafiya sun dukufa wajen ganin sun samar da riga-kafin cutar korona.

    Sama da kungiyoyin masana daban-daban har guda 70 ne a fadin duniya ke wannan kokari a cewar hukumar kula da lafiya ta duniya.

    Tuni wasu har sun fara gwajin riga-kafin a kan dabbobi da kuma mutane. Wasu na ganin zuwa watan Satumbar wannan shekarar ta 2020 za a samu riga-kafi.

    Wasu kuma na ganin cewar zai iya kai wa watan Yulin 2021.

    Ga bayanin dan jarida mai sa ido a kan coronavirus Abdulbaki Jari.

  7. 'Ma'aikatan lafiya kusan 1,000 sun kamu da cutar korona a Afirka'

    Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO, ta wallafa sakon Twitter da ke cewa ma'aikatan lafiya kusan 1,000 ne suka kamu da cutar korona a Afirka.

    WHO ta yi kira ga gwamnatoci su tabbatar cewa sun bai wa likitoci da ma'aikatan jinya kayan kariya lokacin da suke aiki.

    A cewarta, ya kamata duk wanda zai yi mu'amala da mutumin da ake zargi yana dauke da cutar ya kasance sanye da kayan kariya.

    Ma'aikatan lafiya da ke kula da masu korona suna iya daukar cutar ta hanyar shafar wayu ko ruwan da ke fita daga jikin mai dauke da cutar don haka ya kamata su rika sanya kayan kariya, ciki har da rigar kariya da ke rufe mutum daga sama zuwa kasa da abin da ke taimakawa mutum yin numfashi da makarin ido.

    Sai dai kayan kariya sun yi karanci a duk fadin duniya saboda matukar bukatarsu da ake yi.

  8. Coronavirus: 'Akwai lauje cikin naɗi game da shirin ciyar da 'yan makaranta'

    Shugaban kwamitin ilimi mai zurfi na majalisar wakilai na Najeriya Aminu Suleiman Goro ya yi kakkausar suka game da shirin gwamnatin kasar na ciyar da 'yan makaranta a faɗin kasar.

    A wata hira da ya yi da BBC, Aminu Suleiman Goro ya ce babu yadda za a yi shirin ciyar da 'yan makaranta a ko ina a duniya a ce an manta da ma'aikatar ilimi ta kasar.

    Dan majalisar ya ce idan aka damka aikin a hannun ma'aikatar ilimi, aikin zai ta fi tafiya daidai la'akari da cewa suna da kididdigar yawan 'yan makaranta a ko wacce jiha cikin jihohin Najeriya.

    "Ina da tabbacin ma'aikatar ilimi ta Najeriya ba ta san komai kan wannan shirin ba, haka mu ma kwamitin ilimi, yadda ko wa ke jin maganar a kafar sadarwa haka mu ma muka ji," In ji shugaban kwamitin ilimin.

    Ya kuma bayyana cewa shi kansa shirin abu ne mai kyau saboda an yi ne domin a kwadaita wa waɗanda ke ganin ilimin zamani ya musu tsada, da kuma karfafa gwiwar wadanda ke zuwa amma ba su da karfi sosai.

    "Tun da aka shigo da tsarin a farko, ofishin mataimakin shugaban kasa da kuma gwamnonin jihohi ne ke gudanar da shirin tsakaninsu, wanda kuma ba alhakin ofin ba ne gudanar da wannan aiki. Suna aiki ne bisa rahoton da gwamnonin jihohi suka ba su, saboda haka wasu gwamnonin - ban ce duka ba - wasu sun dauki shirin ne kawai tamkar wata dama daga gwamnatin tarayya," ji Aminu Suleiman.

  9. Ethiopia za ta fara cike dam duk da rashin cimma matsaya

    Manyan jami'an Habasha sun ce ma'aikatansu za su ci gaba da gina sabon dam daga kogin Nilu, ko sun cimma yarjejeniya da Masar ko ba su cimma ba.

    Akwai yiwuwar gina dam din na Grand Renaissance ya shafi yawan ruwan da Masar ke samarwa. Duk da zama kan teburin shawara lokuta da dama a tsakanin Habasha da Sudan da kuma Masar, hakan bai sa an cimma matsaya kan bukatar gina dam din da Habasha ke son yi ba.

    Burin gwamnati a Addis Ababa shi ne samar da wutar lantarki ta hanyar dam din don ci gaban al'ummarta.

  10. Likitoci a Indiya sun yi tir da yada labaran karya

    Wasu manyan likitoci da ke cibiyar hada magunguna ta Indiya da kuma wani babban likita, sun yi alawadai da wani sakon karya da ke yawo a kafar sada zumunta ta Whatsapp wanda ke ba da shawarwarin lafiya kan cutar korona.

    Akwai jerin matakan kariya cikin sakon domin kauce wa kamuwa da cutar, ciki har da wadanda aka sani irinsu ba da tazara da kuma matakan tsaftace kai.

    Sakon ya ce a rika cin 'ya'yan itace kawai, kada a rika daura belt da zobe ko agogo, kuma a daina amfani da hankici, wanda duka babu mai ba da kariya daga korona.

    A kasan sakon an ce, wannan sakon ya zo ne daga cibiyar binciken magunguna ta Indiya, sako daga wani babban jami'i da ake kira Sir Ganga Ram da kuma wani fitaccen mai tiyatar zuciya Dakta Devi Shetty.

    Sai dai dukkansu sun shaida mana ba su san komai ba kan wannan sako, kuma sun yi alawadai da wanda ya rubuta shi.

    Devi Shetty ya shaida wa BBc cewa "Abin takaici ne a irin wannan matsanancin yanayi mutane su rika amfani da damar halin da ake ciki suna yada labaran karya".

  11. 'Bai kamata a rika maganar kwallon kafa ba'

    Dan wasan Ingila mai taka lega a kungiyar Tottenham Danny Rose ya yi suka kan shirin sake gasar yayin da ake tsakan matsalar annobar korona.

    "Bai kamata a rika maganar kwallon kafa ba yanzu, har sai adadin mutanen da ke mutuwa ya ragu," in ji Rose.

    A wasu labaran kuma:

    • An soke gasar wasannin tsalle-tsalle da guje-guje da za a yi a Landan a watan Yuli mai zuwa saboda cutar korona.
    • Kazalika an dage wasannin share fagen cin kofin duniya na mata na shekara mai zuwa da za a yi a Sri Lanka a watan Yuli saboda annobar
  12. Isabel dos Santos na son a sakar mata dakarorinta

    Hamshakiyar mai arzikin nan Isabel Dos Santos ta bukaci da a sakar mata kadarorinta da ake rike da su a kasashen Angola da Portugal.

    'Yar gidan tsohon shugaban Angola ta ce akwai shaidun da ke nuna cewa akwai hadin baki tsakanin gwamnati da kotuna wurin shirya bayanan bogi game da ita.

    A watan Janairu ne masu shigar da kara a Angola suka zargi Misis dos Santos da wasu abokan huldarta da almubazzaranci da kudin man fetur din kasar, da yawansu ya kai dala biliyan daya.

    Isabel ta ce a takardun da aka gabatar a matsayin shaida a gaban kotu, akwai fasfo na bogi da aka gabatar da sunanta, amma yana dauke da sa hannun shahararren tsohon mai wasan karetin nan dan kasar koriya Bruce Lee, da ya mutu tun da dadewa.

  13. 'Yan bindiga sun kashe mutum 13 a Afghanistan

    Hukumomi a Afghanistan sun sanar da mutuwar mutun 13 da suka hada da jarirai biyu tare da jikkata wasu 15 a harin ‘yan bindiga a wani asibiti da ke birnin Kabul.

    Rahotanni dai sun ce mahara uku ne suka kutsa kai asibitin inda suka harba bama-bamai kafin suka ci gaba da bude wuta.

    Kusan ma'aikata 140 da suka hada da likitoci da ma'aikatan jinya ne ke cikin ginin kuma ana cikin harin ne aka haifi wani jariri.

    Ana tunanin harin ya shafi wani sashe da ke karkashin kulawar kungiyar bayar da agajin lafiya ta Medicins Sans Frontiers da ke da ma'aikatan kasashen waje.

    To sai dai kungiyar Taliban da ta kulla yarjejeniyar da Amurka na janyewa daga yankin watanni biyu da suka wuce ta ce ba ta da hannu a harin.

  14. Amurka da Brazil ba su dauki anobar korona da muhimmanci ba - WHO

    Hukumar lafiya ta duniya ta ce cutar korona ta yi kamari ne a wasu kasashe saboda rashin bin shawarwarin da ta bayar tun da farko.

    WHO ta yi jawabi ne kai tsaye game da yadda cutar ke dada barna a Brazil da Amurka, kasashen da ta ce shugabanninsu sun musanta irin barnar da cutar korona ka iya yi tun da farko suka kuma rika sukar hukumar.

    Mai magana da yawun WHO ta ce tun a watannin Janairu da Fabrairu suka rika kira da a gudanar da gwaji da kuma killace jama'a amma kasashen bas u dauki abun da muhimmanci ba.

    Duk da ita ma hukumar lafiya ta duniya ta fuskanci suka kan yadda take tafiyar da aikinta, mai magana da yawun hukumar ta ce babu mamaki kasashe irin Amurka da Brazil ba su fuskanci annoba mai hadari ba a baya da ta tayar musu da hankali sosai.

    Shi ya sa ba su dauki cutar korona da wani muhimmanci ba har ta yi barnar da ta yi musu a yanzu.''

  15. 'Yan Najeriya 23,000 sun yi kaura zuwa jamhuriyar Nijar

    Babban Kwamishinan hukumar kula da 'yan gudun hijra ta Majalisar Dinkin Duniya, ya ce akalla mutum 42,000 suka tsere daga kusa da iyakar Najeriya da Nijer sakamakon ayyukan masu dauke da bindiga.

    "Rikicin da ke wakana a wasu sassan arewa maso yammacin Najeriya ya tilasta mutum 23,000 yin kaura domin neman mafaka a jamhuriyar Niger a watan Afrilu.

    Ya kara da cewa "an kuma samun mutum 19000 'yan jamhuriyar ta Nijer da su ma suka tsere saboda rikice-rikicen da ke addabar su a cikin kasarsu.

  16. Shugaban Madagascar ya mayar wa da Turai martani kan maganin korona

    Shugaban Madagascar, Andry Rajolina ya mayar da martani ga masu caccakar sa kan amfani da maganin gargajiya wajen neman waraka daga annobar korona.

    A makon da ya gabata ne dai Hukumar Lafiya ta Duniya,WHO ta fitar da gargadi cewa jama'a su guji yin amfani da magungunan gargajiya domin neman waraka daga cutar korona.

    WHO ta ce ya kamata 'yan Afirka su yi amfani da magungunan da aka tabbatar da sahihancinsu a dakunan gwaji.

    Tuni dai shugaban na Madagascar ya aike wa kasashen Afirka maganin gargajiyar, inda Najeriya ta zama kasa ta baya-bayan nan da ta ce ita ma za ta karbo nata kason.

    Da yake magana da gidan talbijin na Faransa, France24, Mista Rajoelina ya ce "idan misali a ce daga Turai aka samu wannan maganin shin za ku ji wani ya ce uffan?

    Rajoelina ya kara da cewa "masu sukar maganin suna yi ne kawai saboda ya fito daga nahiyar Afirka."

  17. Senegal ta bude masallatai da coci-coci

    Kasar Senegal ta sassauta dokar kulle ranar Talata inda aka bude masallatai da coci-coci.

    An dai kyale masallatai su bude domin yin sallolin goman karshe.

    Har wa yau, an kuma rage tsawon lokacin dokar hana zirga-zirga da awa biyu.

    Yayin wani jawabi ta talbijin din kasar ranar Litinin, Shugaba Macky Sall ya ce akwai bukatar 'yan Senegal sun san yadda za su kasnace tare da kwayar cutar korona.

    Sanarwar dai na zuwa ne a daidai lokacin da da kasar ta samu mutum 177 masu duake da cutar a ranar Litinin.

    Jimilla Senegal na da mutum 1,886 da ke dauke da cutar korona inda mutum 19 suka mutu.

  18. Cocin Katolika ta yi tayin kayan aiki domin yakar korona

    Kungiyar bishof-bishof ta 'yan Katolika da ke Najeriya ta yi tayin kayan aiki ga cibiyoyin killace masu cutar korona a fadin kasar.

    Darektan kungiyar, Dr Emmaneul Okechukwu ya shaida wa BBC cewa cocin katolika tana da aiki fiye da guda 400 afadin kasar kuma a shirye take ta bayar da su a yi amfani a zamanin annobar korona.

    Ya kara da cewa cocin na da gadaje da kayan gwaje-gwaje da cibiyoyin killace marasa lafiya da ma asibitoci.

    Kayayyakin cocin dai sun kasance a birane da kauyuka domin amfanin 'ya'yan cocin da ma sauran marasa lafiya da suka kai kansu.

    Kungiyoyi da daidaikuwar jama'a dai a Najeriya na ta bayar da gudunmowar kudi da kayan aiki wajen ganin an yaki annobar korona.

  19. Wuta ta tashi a wurin killace masu cutar korona

    Mutane biyar ne suka rasa rayukansu a wata gobara da ta tashi a wani asibiti na birnin Saint Petersburg da ke Rasha.

    Duka mutanen na dauke da cutar korona kuma a na lura da su a sashen kulawa ta musamman na asibitin.

    Ma’aikatan asibitin sun kwashe majinyata 15 a sashen, amma sun gaza ceton wadannan biyar din ne saboda an daure su da na’urar taimakawa nunfashi.

    Shugaban ma’aikatar ba da agajin gaggawa na yankin ya ce ana binciken musabbabin tashin gobarar, sai dai akwai yuyuwar ta kama ne daga jikin daya daga na’urar taimakawa nunfashi na sashen.

  20. 'Gwajin ne kawai zai iya tabbatar da babu korona a Kogi da Cross Rivers'

    Kungiyar likitoci ta Najeriya, NMA ta bukacin gwamnatin tarayya ta sa kwamitinta da ke yaki da cutar korona ya gudanar da bincike a kan gaskiyar halin da jihohin Kogi da Cross River suke ciki game da annobar korona.

    Jihohin biyu dai su ne har yanzu muhukuntansu ke ikirarin cewa ba a samu bullar cutar korona a yankunansu ba.

    Ko a makon da ya wuce ma wani ayarin ma`aikatar lafiya ta tarayya da jami`an hukumar da ke yaki da cututtuka masu yaduwa sun kai ziyara jihar Kogin, amma sai mahukunta suka musu kora da hali.

    Dr Nagayawa Ayuwaja, jami`i na kungiyar likitocin Najeriyar ya ce "ba za a taba amince wa da batun ba annobar a wadannan jihohi ba har sai an gudanar da gwaji tukunna."