Ganduje ya ƙaddamar da rabon takunkumin fuska 'miliyan ɗaya'

Wannan shafi na kawo muku bayanai kai tsaye dangane da annobar korona da ke yi wa duniya fyadar 'ya'yan kadanya da ma karin wasu labaran daban.

Rahoto kai-tsaye

Usman Minjibir, Umar Mikail and Nasidi Adamu Yahaya

  1. Coronavirus: Saudiyya ta kara haraji

    Saudiyya

    Asalin hoton, Getty Images

    Kasar Saudiyya ta rubanya harajin kaya sau uku a wani matakin samun kudaden tayar da komadar tattalin arzikin kasar da ya samu koma-baya saboda annobar korona.

    Gwamnatin kasar ta ce za ta dakatar da duk alawus-alawus din da ake bai wa 'yan kasar marasa aikin yi domin tsuke bakin aljihun baitil malin kasar.

    Kasar ta Saudiyya dai wadda ta dogara kan arzikin albarkatun man fetir ta fuskanci matsalar tattalin arzikin sakamakon yadda farashin danyen mai ya yi faduwar warwas a kasuwar duniya.

    Shekaru biyu kenan dai da kasar ta fito da harajin kayan a wani mataki na rage yawan dogaro ga man fetur.

  2. Coronavirus: Me ya sa Gwamna WIke ya ruguje otal guda biyu?

    Governor Wike

    Asalin hoton, Nyesom Twitter

    Gwamnan jihar Rivers, Nyesom WIke ya ce masu otal-otal din sun yi wa dokar hana zirga-zirga karan tsaye.

    Batun rushe otal guda biyu da gwamna Wike na Rivers ya yi a karamar hukumar Eleme na ci gaba da bai wa jama'a al'ajabi.

    An dai ce wasu mutane ne ke yin sharholiya a wani otal mai suna Prodest ain da ya sa wani ya kai tseguminsu ga kwmaitin gwamnatin jiha mai yaki da cutar korona, inda kwamitin ya je otal din.

    Ana cikin hakan ne sai wani matashi dan jam'iyyar PDP ya je wurin ana sa-in-sa har ta kai ga ya daki wasu daga cikin 'yan kwamitin da gwamna ya kafa.

    Wani wanda ya gane wa idanunsa faruwar al'amarin, Jeremiah ya shaida wa BBC cewa "al'amarin ya faru ne da yammacin ranar Asabar inda matashin a jam'iyyar PDP ya koma kauyensu kuma jama'a suka tarbe shi a otal din Prodest da Alode.

    Can da yamma kuma sai kawai 'yan kwamitin yaki da korona suka zo suka ce akwai abun da ke faruwa saboda haka sai an ba su kudi naira 100,000.

    Hakan ne kuma ya fusata matashin jam'iyyar PDP inda ya ce ba zai ba su ko da anini ba. Sai suka ce idan har bai ba su abin da suka tambaye shi to za su kai kararsa wurin gwamna Wike kuma sai an rushe otal din.

    Abin mamaki sai kawai muka ji wai gwamnati ta ayyana wannan matashi abin nema har ma ta sanya kudi naira miliyan biyar ga duk wanda ya samo shi.

    Daga nan kuma sai jami'an tsaro suka zo suka kama manajan otal din kuma suka rushe shi sannan suka rushe karin wani otal bisa zargin cewa sun karya dokar kulle."

    Tuni dai gwamnan jihar Rivers din, Nyeson WIke ya ce otal din guda biyu sun karya dokar kulle da gwamnatin jihar ta kafa.

    To sai dai mutane da masana harkar shari'a na ta fama tofa albarkacin bakinsu dangane da ko gwamnan na da dama a dokance ta rushe wadannan otal guda biyu.

    Ana dai yi wa gwamnoni kallon sanya siyasa a yayin gudanar da al'amuransu a zamanin annobar korona, inda suke cuzguna wa abokan hamayya.

    Rivers

    Asalin hoton, RSGH

  3. Adadin masu cutar korona ya kai 4399 a Najeriya

    Hukumar da ke dakile yaduwar cutuka ta Najeriya, NCDC ta ce ya zuwa daren ranar Lahadi, yawan masu dauke da cutar korona a kasar ya kai 4399, inda 778 suka warke kuma aka salleme su sannan mutum 143 suka rasu.

    Wannan dai ya biyo bayan samun karin mutum 248 da hukuma rta yi a ranar ta Lahadi.

    Jihar Legas da Jigawa da Borno da Kano ke saman jadawalin sabbin masu dauke da cutar.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  4. Coronavirus: Gwamna Ganduje zai raba takunkumi guda miliyan daya

    Ganduje

    Asalin hoton, Ganduje/Twitter

    Gwamnan jihar Kano Abudullahi Umar Ganduje ya ce zai raba wa al'ummar jihar takunkumi har guda milyan daya, a wani mataki na dakile cutar korona a jihar.

    A yau Litinin ne dai al'ummar jihar ke samun zarafin fita kan tituna da kasuwanni domin yin cefane.

    Gwamnatin dai ta ce ta kafa dokar tilasta wa mutanen jahar sa takunkumin wato face mask a wuraren taruwar jama’a.

    Gwamman jahar Abdullahi Umar Ganduje ne dai ya sanar da haka a yayin wata ganawa da 'yan jarida a jiya lahadi, bayan lura da cewa jama’ar sun yin biris da wannan umarnin.

    Gwamna Ganduje ya ce tuni sun tani kotunan tafi-da-gidanka inda da zarar an kama masu karya dokar za a hukunta su nan take.

    Gwamnan na wannan jawabi ne a dai-dai lokaicin da adadin wadan ke dauke da cutar a Kano ya haura sama da dari biyar da hamsin, a wata sanarwa da ma’aikatar lafiya ta jahar ta fitar a shafinta na twitter.

  5. Farawa

    Masu bibiyarmu barkanku da war haka. Da fatan kuna cikin koshin lafiya. Yaya muka ji da annobar korona? Allah ya kare mu baki daya. Ku kasance da shafin bbchausa.com domin kawo muku labarai sabbin da dumi-duminsu kuma kai tsaye. Mun gode