Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

El-Rufai ya gano mutanen da aka boye a bayan tirela

Wannan shafi yana kawo muku labarai da rahotannin abubuwan da ke faruwa a duniya game da cutar korona da ma wasu labarai da suka shafi rayuwarku.

Rahoto kai-tsaye

Nasidi Adamu Yahaya, Umar Mikail and Buhari Muhammad Fagge

  1. Cutar korona: Bayanan baya bayan nan game da Turai

    Mene ne yake faruwa a Turai game da cutar korona?

    Dokar kullen da aka sanya a kasashen duniya ta sa kasashe da dama na Turai za su yi bikin cika shekara 75 da kammala Yakin Duniya na Biyu ba tare da tarukan jama'a ba. Shugaba Emmanuel Macron na Faransa ya tafi ginin nan na tarihi mai suna Arc de Triomphe da ke Paris, Shugabar Gwamnatin Jamus Angela Merkel da kuma shugaban kasar ta Jamus Frank-Walter Steinmeier za su ajiye furanni a Berlin, sannan kuma za a yi tsit na minti biyu a Birtaniya da misalin karfe 11 na safe. A wasu labaran kuma:

    • Shugabar hukumar lafiya ta Madrid Yolanda Fuentes ta ajiye mukaminta domin adawa da matakin da gwamnatin babban birnin na Spaniya ta dauka na sassauta dokar kulle daga ranar Litinin mai zuwa. Mutanen da suka mutu sakamakon cutar korona a Madrid sun zarta na kowanne yanki na Spaniya, amma ana samun raguwar masu kamuwa da cutar.
    • Rasha ta sanar da karin mutum 10,669 da suka harbu da cutar korona cikin kwana guda - kuma wannan shi ne karo na shida a jere da masu kamuwa da cutar suka zarta 10,000
    • Denmark ta sanar da matakan sassauta dokar kulle. Tun a watan jiya ta soma sassauta dokar kuma yanzu ta ce za a iya ci gaba da kwallon kafa ko da yake ba tare da 'yan kallo ba; sannan za a bude kantuna daga ranar Litinin.
    • Serbia ta janye dokar ta-baci ranar Alhamis kuma jiya da daddare 'yan sanda sun kama mutum fiye da 100 da suka shiga zanga-zangar siyasa a wajen ofishin Shugaba Aleksandar Vucic.
    • Kayan da Jamus take fitarwa kasashen waje sun ragu da kashi 11.8 a watan Maris. Wannan ne karon farko da aka samu mummunar raguwa ta fitar da kayan zuwa kasashen waje tun bayan sake hada Gabashi da Yammacin Jamus a 1990.
  2. Me ya sa APC da PDP suke ce-ce-ku-ce a kan kudin Abacha?

    Zargin da PDP, babbar jam'iyyar hamayya a Najeriya ta yi cewa wasu shafaffu da mai na shirin wawure $311m da Amurka ta mayar wa gwamnatin Najeriya a makon nan, ya janwo ce-ce-ku-ce tsakaninta da jam'iyyar APC mai mulkin kasar.

    Wata sanarwa da kakakin PDP, Kola Ologbondiyan ya fitar ranar Laraba ta yi zargin cewa ta bankado wani shiri da "wasu shafaffu da mai da ke fadar shugaban kasa da jam'iyyar APC suke yi na amfani da kwangilar bogi da kuma fakewa da yin aikin da aka taba yi da zummar sake sace $311m."

    Sai dai a martanin APC ta yi zargin cewa PDP tana hadiyar yawu ne kawai saboda ganin zunzurutun kudin da bata isa ta sace kamar yadda take yi a baya ba.

    "Mun fahimci mawuyacin halin da PDP take ciki. Yunkurinsu na shafa wa APC kashin-kaji game da cin hanci don ɓata mata suna ya gaza... Abin takaici shi ne, PDP ta kasa fitar da cin hanci daga cikin ɓargonta kuma idan bata watsar da ɓurɓushin cin hancin da ke jikinta ba, ba za ta daina magagi kan kudaden jama'a ba," in ji sanarwar da mai magana da yawun APC, Mallam Lanre Issa-Onilu, ya fitar.

  3. COVID-19: Za a bar mutane su je masallatai da coci-coci a Lebanon

    Gwamnatin Lebanon za ta bar mutane su ci gaba da halartar masallatai da coci-coci daga yau Juma'a, bayan kusan wata biyu da ƙaƙaba matakan hana taruka.

    Amma sai masu ibada sun sanya takunkumai da safunan hannu kuma sun ba wa junansu rata.

    Wakiliyar BBC ta ce daga yau Juma'a, Musulmi za su iya ci gaba da zuwa masallatai a wannan wata na Ramadana, za kuma a bude coci-coci ranar Lahadi.

    Hakan na nufin masallatai za su takaita mutanen da kan je ibada zuwa kashi 30 cikin 100 a wannan lokaci na azumin Ramadan.

    Matakin wani bangare na wani shiri mai fuska biyar don d'age duk tarnak'an da aka sanya kafin tsakiyar watan gobe.

    A 'yan kwanakin nan, mutanen da aka gano sun kamu da covid-19, sun koma ƙasar ne daga ƙetare.

  4. Zan haɗa kan al'ummar Ƙauran Namoda - Sabon Sarki

    Sabon Sarkin Ƙauran Namoda da ke jihar Zamfara a Najeriya, Alhaji Sanusi Mohammed, ya ce babban aikin da zai sanya a gaba yanzu shi ne hada kan al'ummar masarautar da kuma yi wa Najeriya hidima.

    Alhaji Sanusi Mohammed - wanda Manjo ne na sojin Najeriya kafin ya zama Sarki - ya maye gurbin mahaifinsa Alhaji Mohamned Ahmed Asha wanda ya rasu ranar Lahadin da ta gabata.

    A hirarsa da BBC, Sabon Sarkin ya ce "babban abin da zan mayar wa hankali bai wuce in yi tunanin ganin cewa na hada kan al'umma ba...mu tabbatar cewa mun kara hada kanmu saboda mu zauna lafiya."

    Ya kara da cewa zai yi amfani da kwarewarsa ta aikin soji domin taimakawa gwamnatin jihar Zamfara da ma Najeriya wajen shawo kan matsalolin tsaron da suka addabi jihar.

    Ya yi kira da al'ummar masarautarsa su ci gaba da biyayya ga matakan kare lafiya da hukumomin lafiya suka bayar da shawarar bi wajen kauce wa kamuwa da cutar korona.

    Latsa alamar lasifika da ke kasa domin sauraren hira da Sarki Sanusi Mohammed:

  5. Cutar korona za ta iya kashe 'yan Afirka 190,000 - WHO

    Hukumar Lafiya ta Duniya ta yi gargadin cewa cutar korona za ta iya kashe mutanen da suka kai 190,000 a nahiyar Afirka a shekarar farko da bullar ta idan matakan da aka dauka na yaki da ita suka gaza.

    Hukumar, wacce ta bayyana haka a cikin wani bincike da ta gudanar, ta kara da cewa wannan adadi zai sa cibiyoyin kula da lafiya su yi cikar da ba za a iya shawo kan cutar ba.

    Shugaban WHO a Afirka Matshidiso Moeti ya ce yaduwar cutar a nahiyar ba ta da yawa amma zai iya zama haifar da bullar cutar ta tsawon lokaci.

    "Ko da yake mai yiwuwa cutar korona ba za ta yadu da yawa a Afirka kamar yadda take yi a wasu nahiyoyi ba, amma za ta iya jimawa a yankunan da ta yi katutu," in ji Dr Moeti.

    Hukumar ta bayar da shawarar inganta fannin kiwon lafiyar nahiyar.

    "Covid-19 za ta iya zama wani bangare na rayuwarmu nan da wasu shekaru masu zuwa har sai gwamnatoci sun dauki matakan gaggawa a nahiyar. Muna bukatar yin gwaji don gano masu dauke da cutar da gano su da kuma killace su, har ma da yi musu magani," a cewar Dr Moeti.

  6. Barkanmu da Juma'a

      • Marubuci, Nasidi Adamu Yahya
      • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Hausa, Abuja

    Nasidi Adamu Yahaya ne yake yi muku barka da Juma'a.

    Muna fatan za ku kasance tare da mu tsawon wannan rana mai albarka domin sanin halin da duniya take ciki, musamman game da annobar korona.

    Za kuma mu kawo muku wasu labarai da rahotannin da suka shafi rayuwarku, musamman kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Nijar da makwabtansu, har ma da sassan duniya.