Rufewa
Masu bibiyarmu nan muka kawo karshen shirin. Mun gode.
Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wannan shafi yana kawo muku labarai da rahotannin abubuwan da ke faruwa a duniya game da cutar korona da ma wasu labarai da suka shafi rayuwarku.
Nasidi Adamu Yahaya, Umar Mikail and Buhari Muhammad Fagge
Masu bibiyarmu nan muka kawo karshen shirin. Mun gode.
R0 wato R Naught da turanci wata lamba ce mai muhimmanci da ke nuna yiwuwar wadanda suka kamu da cuta su yadawa wasu.
Gwamnatoci na yin amfani da ita wajen tsaurarawa ko kuma sassauta dokar hana fita a cikin kasashe.
Ga bayanin dan jarida mai sa ido a kan coronavirus Abdulbaki Jari.
Sarki Muhammadu Sanusi wanda aka cire a gadon sarautar Kano, ya dukufa wajen yin wa'azi tun da aka soma azumin watan Ramadana.
Sarki Sanusin yana gudanar da wa'azin ne daga gidansa da ke Lagos.
Alhaji Muhammadu Sanusi II ya gabatar da wa’azinne ta shafin Zoom wanda ke bada damar ganin bidiyonsa.
Yana karanta littafin Madaarij us Saalikeen da yake fassarawa da harshen hausa.
Jami'an gwamnatin jihar Kaduna a yankin Jere kusa da Abuja sun gano wasu mutane da dama da aka boye a bayan tirela mai dakon taki.
Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir ElRufai ne ya wallafa hakan a shafinsa na Twitter.
Gwamnan ya ce an rarraba jami'an gwamnatin jihar a manyan mashigar jihar domin gano wadanda ake kokarin shigo dasu ta barauniyar hanya.
An kafa dokar takaita jirga-jirga tsakanin jihohin Najeriya a wani mataki na rage yaduwar cutar korona.
Ku kalli tattaunawar da muke yi da Sheikh Dr. Bashir Aliyu Umar kai-tsaye a shafinmu na Facebook.
Muna tattauanawa ne game da falalar kwana 10 na karshe a watan Azumin Ramadana.
Mai Alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa'ad Abubakar III ya bi sahu wurin wayar da kan al'umma kan yadda za su kare kansu daga kamuwa da cutar korona.
Wani sako da hukumar National Orientation Agency - hukuma mai wayar da kai ta Najeriya - ta wallafa a Twitter ya nuna hoton sarkin yana bayyana cewa cutar korona gaskiya ce.
Mai Alfarma Sarkin Musulmi ya yi kira ga 'yan Najeriya da su sanya takunkumi kuma su zauna a gida domin kare lafiyarsu.
"An san sarakunan gargajiya da kasancewa kusa da al'umma a yankunansu, hakan kan sa su yi tasiri kan talakawansu," a cewar sakon.
Kungiyar Tarayyar Turai ta yi kakkausar suka ga jakadanta a Beijing, game da bai wa ministan harkokin wajen China wata budaddiyar wasika da ya gyara, wadda ta yi kiran a hada hannu a wannan lokacin da ake fama da annobar korona.
Jami'ai a Brussels sun ce abin da Nicolas Chapuis ya yi kuskure ne, da ya bayar da wasikar aka cire wani bangare daga cikinta.
Wanda ke cewa korona ta samo asali ne daga China sannan ta yadu zuwa sauran sassan duniya.
An dai wallafa wannan wasikar mai dauke da sa hannun jakadan da kuma duka mambobin kungiyar EU a jaridar China Daily.
Amma ba dukansu bane suka san an cire wani bangaren nata.
Rundunar sojin kasar Congo ta ce sojinta sun kashe 'yan tawayen kungiyar Codesco 23 tare da kwace iko da wasu kauyuka biyu, ciki harda Djugu da ke da matukar mahimmanci ga kungiyar, wanda ke arewa maso gabashin lardin ituri.
Kungiyar 'yan tawaye ta Codesco ta kwashe shekara uku tana gudanar da ayyukanta a yankin.
Mayakanta sun kashe daruruwan fararen hula tare da tilastawa sama da mutum 500,000 barin muhallansu.
A farkon makon nan ne, shugaban kungiyar ya mika wuya ga gwamnatin Congo tare da wasu mayakansa, ya kuma yi kira ga sauran mayakan da su mika wuya suma.
Sojojin Congo sun kai simame mai yawa ga mambobin kunyar a yankin gabas da ke da arzikin ma'adanai, inda akwa kwashe sama da shekara 20 ana fama da rikicin 'yan tada kayar baya.
Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce za'a shafe kusan shekara guda kafin a kai ga gano ainihin tushen cutar Korona.
Da yake jawabi a birnin Geneva, wani kwararre da ke aiki da hukumar ya ce, hujja daya tak da ake da ita zuwa yanzu ita ce wadda ke nuna cewa cutar ta faro ne daga jemagu, da suka yada ta zuwa wasu dabbobi da jama'a ke cin namansu, har ta kaiga bil'adama sun dauka.
Kwararru na ganin har yanzu masana kimiyya basu samu tabbaci akan ko daga ina cutar ta samo asali ba, hujjar da kawai ake da ita ce wacce ta nuna cewa ta faro ne daga wata kasuwa da ke birnin Wuhan, sai dai cikin mutane 41 da suka kamu da cutar a China tun da farko, 27 ne suka dauke ta a kasuwar.
A makon da ya gabata ne WHO ta yi watsi da ikirarin shugaban Amurika Donald Trump na cewa, cutar Korona ta samo asali ne daga wani dakin binciken kimiyya da ke China.
Saudiyya ta bayar da rahoton samun karin mutum 1,701 da suka harbu da cutar korona ranar Juma'a, abin da ya kai jumillar adadin zuwa 35,432, a cewar Ma'aikatar Lafiya kasar.
Wasu mutum 10 sun rasa rayukansu, inda baki dayan adadin nasu ya kai 229.
Kazalika ma'aikatar lafiyar ta ce mutum 1,322 sun warke daga cutar, su ma adadinsu ya zama 9,120.
Daga cikin sabbin wadnda suka kamun, 308 a garin Madina suke, 246 a Makkah, 373 a Jeddah, 142 Rayadh. Sauran suna garuruwan Dammam da Juabil.
Gwamnatin Najeriya ta samar da hanyar da 'yan ƙasa za su nemi tallafi da na kusan kimanin naira miliyan 25 domin rage radadin halin da annobar cutar korona ta saka su ciki.
Iyalai da wannan annoba ta yi wa rayuwarsu illa za su iya neman tallafi amma sai suna da hujjar tabattar da hakan, a cewar sharuɗɗan da aka wallafa a shafin neman tallafin.
Masu kanana da matsakaitan sana'o'i ma na da damar neman tallafin matukar dai suna da hujjojin da za su tabbatar da cewa annobar ta durkusar da sana'o'insu.
Domin karanta ka'idoji da kuma cike fam din neman tallafin cikin harshen Ingilishi, ku latsa wannan adireshi.
Dan wasan gaban kungiyar Tottenham, Son Heung-min ya kammala hidimar kasa ta aikin soja ta tsawon mako uku da ya yi wa kasarsa Koriya ta Kudu, har ma ya lashe kyautar bajinta.
Hukumomi sun ce ɗan shekara 27 ɗin ya nuna bajinta a horon harba bindiga a cikin masu karbar horon su 157.
Son ya koma ƙasarsa ne a watan Maris domin ci gaba da jinyar hannunsa da ya raunata, yayin da aka dakatar da wasannin kwallo sakamakon annobar korona.
Wajibi ne maza 'yan Koriya ta Kudu su yi hidimar aikin soja kafin su cika shekara 28 da haihuwa.
An daga wa Son ƙafa ne bayan ya taimaka wa kasarsa lashe wasannin Nahiyar Asiya na 2018.
Alkaluman rashin aikin yi a Amurka sun yi tashin gwauron zabi zuwa kashi 14.7%, yayin da mutum miliyan 20.5 suka rasa aikin yi a watan Afrilu kadai sakamakon lahanin da annobar korona ke ci gaba da yi wa tattalin arzikin kasar.
Waɗannan alƙaluma na nufin ba a taba samun irinsu ba tun bayan lokacin Great Depression da aka yi a shekarun 1930.
Tun bayan ɓullar annobar, Amurka ta ɗanɗana mafi munin tabarbarewa a harkar kasuwanci. Wata biyu da suka wuce, ƙiyasin rashin aikin yin yana kashi 3.5%, mafi muni cikin shekara 50.
Alƙaluman da aka bayar na ranar Alhamis sun nuna Amurkawa miliyan 3.2 ne suka bukaci tallafi na marasa aikin yi a makon da ya gabata. Wannan ya kawo jumillar adadin wadanda suka yi ikirarin rashin aikin yi zuwa miliyan 33.3 tun daga tsakiyar watan Maris - kashi 20% kenan na kafatanin ma'ikatan kasar.
Wata kotu a Bahirdar, arewacin Habasha, ta tura tsohon ministan sadarwar kasar kuma na hannun-daman marigayi firai minista Meles Zenawi zaman gidan yari na shekara shida saboda samunsa da laifin cin hanci.
A watan Janairun 2019 aka kama Bereket Simon a gidansa da ke Addis Ababa, babban birnin kasar inda aka kai shi Bahirdar, baban birnin lardin Amhara. Tun wancan lokacin yana gidan yari.
Ranar Talata aka same shi d laifi. Wasu daga cikin magoya bayansa sun ce tuhumar da aka yi masa tana da alaka da siyasa.
Shi ne mutumin da ya fi karfin fada-a-ji a gwamnatin Mr Zenawi kuma ana yi masa kallon mutumin da yake juya al'amura a lokacin da gamayyar jam'iyyar Ethiopian People’s Revolutionary Democratic Front (EPRDF), ta yi mulki tun a shekarun 1990.
Kungiayar Islamic State (IS) ta tabbatar a karon farko cewa ta gwabza da dakarun kungiyar al-Qaeda a kasashen Mali da Burkina Faso.
A wani rahoto da ta wallafa a shafinta na intanet mai suna al-Naba, ta siffanta dakarun al-Qaeda na yankin Sahel da cewa sun yi ridda sannan kuma karnuka ne.
IS ta ce ta kai wa abokan hamayyarta harin kunar bakin wake da kuma sauran hanyoyi.
An samu rahotannin da ke cewa mayakan al-Qaeda sun yi watsi da wani tayin tsagaita wuta, wanda zai sa a saki fursunonin IS sannan a biya ta fansar dakarunta da suka mutu.
Hare-haren 'yan bindiga masu ikirarin jihadi ya karu a yankin Sahel a baya-bayan nan.
Dan wasan Manchester City da Ingila, Kyle Walker ya ce "ana tsangwamarsa" bayan rahotanni sun ruwaito cewa ya sake karya dokar hana fita da yin nesa-nesa da juna.
Dan wasan mai shekara 29 ya tabbatar cewa ya je Sheffield wurin 'yar uwarsa, inda ya ba ta kyauta ta ranar haihuwarta sannan ya rungume ta a ranar Laraba, kafin daga bisani ya je gidan iyayensa domin "karbar dafaffen abinci".
Tuni da ma yake fuskantar tuhuma daga Man City bisa karya dokar a farkon watan Afrilu bayan ya hada shagalin biki a gidansa tare da wasu mata biyu.
Hukumar da ke daƙile cutuka masu yaduwa a Afirka mai suna Africa CDC ta ce tana wani yunkuri na tura ma'aikatan lafiya miliyan daya a ƙasashen nahiyar nan da karshen shekarar 2020 domin yaki da cutar korona.
A ranar Alhamis ne hukumar ta fara tura jami'ai 20 zuwa ƙasar Habasha wato Ethiopia domin taimaka wa ƙasar a yaƙi da cutar da ake yi wa lakabi da Covid-19.
CDC ba ta fayyace yawan ma'aikatan lafiyar da za ta tura zuwa kowace ƙasa ba. Sai dai kasashe a nahiyar za su bukaci kowane irin tallafi da ya shafi lafiya ganin irin yadda cutuka ke wahalar da su.
Cutar korona ta bulla kasashe mambobin kungiyar AU guda 53 na Nahiyar Afirka, inda ta kama mutum fiye da 54,027 sannan 2,074 suka mutu, sai kuma 18,636 da suka warke, a cewar alkaluman CDC.
Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Ogun da ke kudu maso yammacin Najeriya Abimbola Oyeyemi ta ce za a kama duk wanda aka gani a waje ba tare da makarin fuska ba.
Jihar tana cikin jihohin da suka fi fama da cutar korona inda aka kwashe kwana 35 cikin kulle wanda aka sassauta a makon jiya.
Gwamna Dapo Abiodun na jihar ya bayar da umarnin tilasta wa mutane sanya takunkumin fuska domin ya zama matakin dakatar da yaduwar cutar.
Tun ranar 1 ga watan Mayu aka bayar da umarnin, sai dai jami'ai sun ce mutane ba sa biyayya ga umarnin.
Rundunar 'yan sandan jihar ta ce a karshen makon nan za a soma tursasa wa mutane sanya makarin na fuska.
A cewarta, za a killace duk wanda ya fito ba tare da makarin fuska ba tsawon kwana 14 sannan za a horas da shi.
Ya zuwa yanzu jihar Ogun ta tabbatar da cewa mutum fiye da 100 sun harbu da cutar korona.
Hukumar da ke kula da Masallatan Harami ta wallafa hotuna mutane sun bin dokar nesa-nesa da juna lokacin gudanar da salloli a masallatan na Harami da ke kasar Saudiyya.
Kasar ta Saudiyya dai ta tabbatar mutum 33,731 sun kamu da cutar korona, yayin da mutum 7,798 suka warke, amma mutum 219 sun mutu.