'Mutum 92 ne suka mutu cikin kwana takwas a Jigawa'

Wannan shafi yana kawo muku labarai da rahotannin abubuwan da ke faruwa a duniya game da cutar korona da ma wasu labarai da suka shafi rayuwarku.

Rahoto kai-tsaye

Nasidi Adamu Yahaya, Umar Mikail and Buhari Muhammad Fagge

  1. Baƙaƙen fata sun fi kasadar mutuwa a Birtaniya sakamakon korona

    Wani bakar fata

    Asalin hoton, Getty Images

    Bakaken fata maza da mata sun fi saurin mutuwa sama da 'yan uwansu fararen fata sakamakon cutar korona, a cewar wani bincike daga ofishin kididdiga na Birtaniya.

    Binciken ya duba mace-macen da aka yi ne ta hanyar kwatanta su da bayanan launin fatar 'yan kasa da aka tattara a kididdigar shekarar 2011.

    An duba shekaru, inda mutane ke zaune da kuma yanayin halin da suke ciki, rashin samun dama da kuma kiwon lafiya. Bayan duba wadannan abubuwa, yiyuwar mutuwa tsakanin bakaken fata maza da mata ta zarta ta tsakanin farare da kashi 90 cikin 100.

    Maza da mata da suka fito daga kasashen Bangladesh da Pakistan ma suna cikin hadari sosai sama da fararen fata, duk da cewa nasu hadarin ya fara ne daga kashi 30 zuwa 80 cikin 100.

    Sai dai bayanan da aka tattaro daga kididdigar ba za su iya tamntance hakikanin dalilan da ke jawo girman hadurran ba saboda ba su duba yanayin kiwon lafiyar da mutanen ke ciki ba a yanzu, kamar yanayin cukowa a muhallansu, ko kuma bambancin da ke tsakanin wata unguwar zuwa wata da ka iya kara girman hadarin mutuwa daga cutar.

  2. Kai-tsaye: Shirin korona, ina mafita.

    Za ku iya kallon shirinmu na Korona, ina mafita kai-tsaye ta shafinmu na Facebook.

    Muna kawo muku shirin ne daga Litinin zuwa Alhamis na kowacce rana tsakanin karfe 12:00-1:00 na rana.

  3. Kun san adadin mutanen da korona ta kashe a Kano ?

    A hukumance, gwamnatin jihar Kano ta ce cutar korona ta hallaka mutum 13 ya zuwa ranar 6 ga watan Mayu.

    Alkaluman da ma’aikatar lafiya ta jihar ta wallafa a shafinta na Twitter sun nuna cewa mutum biyar ne suka mutu sakamakon cutar a ranar Laraba.

    Sai dai kuma an sallami karin mutum uku daga cibiyar killace mutane a yayin da adadin masu cutar ya kai mutum 427.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  4. Coronavirus: Kamfanonin jiragen saman Najeriya na asarar N20bn duk wata

    Kamfanonin jiragen saman Najeriya suna yin asarar kusan naira biliyan 20 duk watan duniya sakamakon dokar kullen da aka sanya a kasar.

    Shugaban kamfanin jiragen saman Aero Contractor, Kyaftin Ado Sanusi ne ya tabbatar da hakan a tattaunawarsa da BBC.

    A cewarsa, "A gaskiya bamu taba ganin irin wannan asara a harkar jiragen sama a duk duniya ba. Saboda idan ka duba za ka ga cikin wata biyu bamu sayar da tikiti ba. A kan kowanne wata, asarar da aka yi ta kai tsakanin biliyan 15 zuwa 20."

    A ranar Laraba ne gwamnatin kasar ta tsawaita matakin dakatar da zirga-zirgar jiragen sama a kasar da mako huɗu.

    Latsa alamar lasifika ta hoton da ke ƙasa domin sauraron cikakkyar hirar da wakilinmu Umar Shehu Elleman, ya yi da shi:

    Bayanan sautiCoronavirus: Kamfanonin jiragen sama na asarar N20bn duk wata a Najeriya
  5. Coronavirus: Yadda za ku wanke hannayenku

    Ku kalli wanna bidiyon na tsawon dakika 56 domin ganin yadda za ku rika wanke hannayenku a wannan lokaci na annobar korona.

    Bayanan bidiyo, Yadda za ku wanke hannayenku
  6. Kwamishinan da Ganduje ya tuɓe 'ya kamu da cutar korona'

    Tsohon kwamishinan ayyukan jihar Kano da ke Najeriya, wanda Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya tube sakamakon 'yin murna' da mutuwar shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasar, Abba Kyari, ya ce ya kamu da cutar korona.

    A waki sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook ranar Alhamis, Injiniya Mu'azu Magaji, ya ce yanzu haka yana cibiyar killace masu dauke da cutar korona a ke Kano.

    Mu'az Magaji

    Asalin hoton, Mu'az Magaji

    Bayanan hoto, An sauke Mu'az Magaji daga mukaminsa ne bayan 'ya yi murnar rasuwar Abba Kyari'

    A cewarsa, "Da safiyar nan sakamakon gwajin da hukumar yaki da cututtuka masu yaduwa ta Najeriya (NCDC) ta yi min ya fito. An tabbatar ina dauke da Covid-19... kuma an kai ni cibiyar kula da masu dauke da cutar. A taya ni da addu'a.

    A watan jiya ne Injiniya Mu'azu Magaji ya janyo ce-ce-ku-ce a Najeriya bayan ya yi kalaman da wasu ke gani na nuna murna ne da rasuwar Abba Kyari, wanda ya mutu sakamakon kamuwa da cutar korona.

    Sai dai kwamishinan -- wanda bai musanta cewa ba shi ya wallafa bayanan ba -- ya yi nadama a cikin wata sanarwa da ya fitar, inda ya ce rashin fahimtar bayanan da ya wallafa a Facebook aka yi, har ta kai ga daukar matakin tube shi daga mukaminsa na kwamishina.

    "Ina neman gafara ga duk wani abin da ya haifar da rudani, da martani, dukkaninmu muna cikin mawuyacin lokaci na damuwa inda damuwa da kunci ke sa da wahala a iya bambance fahimta da rashin fahimta."

    "Na yi nadama kan duk wani bakin ciki da na janyo wa iyalan marigayi shugaban ma'aikata a fadar shugaban kasa da kuma maigida na Gwamna Abdullahi Umar Ganduje," a cewar tsohon kwamishinan.

    Mu'az Magaji

    Asalin hoton, Facebook/Mu'az Magaji

  7. Ambaliyar ruwa ta kashe mutum sama da 200 a Kenya

    Ana sa ran za a ci gaba da sheƙa ruwan sama kamar da bakin-ƙwarya

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, Ana sa ran za a ci gaba da sheƙa ruwan sama kamar da bakin-ƙwarya

    Ambaliyar ruwa da zaftarewar laka sun yi sanadin mutuwar aƙalla mutum 200 a Kenya tun da aka soma mamakon ruwan sama a ƙasar a watan jiya.

    Kazalika mutum fiye da 100,000 sun rasa gidajensu sakamakon ambaliyar ruwan.

    Sanarwar da fadar shugaban ƙasar ta fitar ta ce an yi asarar dubban hekta na amfanin gona.

    Ana sa ran za a ci gaba da sheƙa ruwan sama kamar da bakin-ƙwarya

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, An umarci mutanen da ke zaune a yankuna da ke kusa da madatsan ruwan da su bar gidajensu

    Ana sa ran za a ci gaba da sheƙa ruwan sama kamar da bakin-ƙwarya nan da makonnin da ke tafe.

    Hakazalika ana fargabar madatsan ruwan da ke samar da hasken wutar lantarki za su ɓalle. An shaida wa mutanen da ke zaune a yankuna da ke kusa da madatsan ruwan da su bar gidajensu don komawa wasu yankunan.

    Gwamnatin Kenya ta ce ambaliyar ruwa za ta kawo koma-baya a yunkurin da ake yi na daƙile cutar korona, wacce ta yi ajalin mutum 26 a kasar.

  8. Kasuwar 'yan ƙwallon ƙafa: Ighalo, Gomes, Kurzawa, Rashica, Bakayoko

    Manchester United tana son tsawaita zaman aron dan wasan Najeriya Odion Ighalo, mai shekara 30, wanda ta karbo dagaShanghai Shenhua, a cewar jaridar Standard.

    Fatan Arsenal na dauko dan wasan Faransa Layvin Kurzawa daga Paris St-Germain ya samu tagomashi saboda suna da tabbaci cewa Barcelona ba za ta dauki dan wasan mai shekara 27 ba.(Le10 Sport - in French)

    Liverpool,Southampton da kuma RB Leipzigsuna son dauko dan wasan Werder Bremen Milot Rashica, mai shekara 23, a yayin da kwantaragin dan kasar ta Kosova take shirin karewa a watan Yuni.(Bild - in German)

    Odion Ighalo

    Asalin hoton, Getty Images

  9. Cutar korona ta kashe mutum sama da 100 a Najeriya

    Hukumar yaki da cututtuka masu yaɗuwa a Najeriya, NCDC, ta ce mutum 103 ne suka mutu sakamakon cutar korona a ƙasar.

    A sakon da ta wallafa a shafinta na Twitter a daren Alhamis, NCDC ta ƙara da cewa cutar ta korona ta kama 3145 jumulla. A cewarta, mutum 534 ne suka warke daga cutar kawo yanzu.

    Cikin mutanen da suka mutu, mutum 31 daga Lagos suke, mutum 13 daga Kano, Abuja tana da mutum 4.

  10. Buɗewa

      • Marubuci, Nasidi Adamu Yahya
      • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Hausa, Abuja

    Nasidi Adamu Yahaya ne yake yi muku barka da warhaka.

    Muna fatan ku kasance tare da mu tsawon wannan rana domin sanin halin da duniya take ciki.

    Za mu kawo muku labarai da rahotannin da suka shafi rayuwarku, musamman kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Nijar da makwabtansu, har ma da sassan duniya.