Baƙaƙen fata sun fi kasadar mutuwa a Birtaniya sakamakon korona
Bakaken fata maza da mata sun fi saurin mutuwa sama da 'yan uwansu fararen fata sakamakon cutar korona, a cewar wani bincike daga ofishin kididdiga na Birtaniya.
Binciken ya duba mace-macen da aka yi ne ta hanyar kwatanta su da bayanan launin fatar 'yan kasa da aka tattara a kididdigar shekarar 2011.
An duba shekaru, inda mutane ke zaune da kuma yanayin halin da suke ciki, rashin samun dama da kuma kiwon lafiya. Bayan duba wadannan abubuwa, yiyuwar mutuwa tsakanin bakaken fata maza da mata ta zarta ta tsakanin farare da kashi 90 cikin 100.
Maza da mata da suka fito daga kasashen Bangladesh da Pakistan ma suna cikin hadari sosai sama da fararen fata, duk da cewa nasu hadarin ya fara ne daga kashi 30 zuwa 80 cikin 100.
Sai dai bayanan da aka tattaro daga kididdigar ba za su iya tamntance hakikanin dalilan da ke jawo girman hadurran ba saboda ba su duba yanayin kiwon lafiyar da mutanen ke ciki ba a yanzu, kamar yanayin cukowa a muhallansu, ko kuma bambancin da ke tsakanin wata unguwar zuwa wata da ka iya kara girman hadarin mutuwa daga cutar.