Buhari ya yi wa Sarkin Daura addu’ar samun lafiya

Wannan shafi na kawo muku bayanai kai tsaye dangane da annobar korona da ke yi wa duniya fyaden 'ya'yan kadanya.

Rahoto kai-tsaye

Usman Minjibir, Awwal Ahmad Janyau and Nasidi Adamu Yahaya

  1. 'Idan aka yi gwaji za a samu masu korona a jihar Kogi'

    Kogi

    Asalin hoton, Yahaya Bello/Twitter

    A Najeriya, Kogi na cikin jihohi guda biyu da kawo yanzu ba a samu rahoton bullar cutar korona ba.

    Mahukunta a jihar sun ce matakan da suke dauka, na taka rawa wajen kare jihar.

    Sai dai wasu kungiyoyin fararen hula na zargin cewa korona ta shiga Kogi, amma ba za a san haka ba tun da ba a gwada mutane.

    Jihar Kogi dai na tsakiyar Najeriya ne, inda kusan dole mutanen arewaci da kudanci su ratsa ta jihar ta Kogi yayin da suke son zuwa ko barin daya daga cikin yankunan biyu.

    Yanzu dai jihar Kogi da Cross River ba a samu mai dauke da cutar korona ba.

  2. Dalilin da ya sa masu korona suka yi zanga-zanga a Gombe

    Gombe

    Asalin hoton, Gombe State Government

    Hukumomi a jihar Gombe da ke arewa maso gabashin Najeriya sun yi karin haske kan wata zanga-zanga da masu dauke da cutar korona suka yi a daya daga cikin cibiyoyin kula da su a jihar.

    A jiya ne dai masu dauke da kwayar cutar suka fice daga cibiyar da ke garin Kwadon, kana suka tare babbar hanya da ke kusa, suna kukan rashin samun kulawa yadda ya kamata daga hukumomi.

    Kwamishinan Lafiya na jihar ta Gombe, Dr Ahmed Muhammad Gana ya ce "wasu daga cikin masu dauke da cutar sun yi korafin cewa akwai mai cutar kurji wanda ya fashe yake zubar da ruwa, a cikinsu inda suke son a dauke ta daga cikinsu. Mun garzaya mun je wurin domin dauke matar amma sai muka gan su sun tare hanya suna zanga-zanga."

    Rahotanni kuma sun nuna cewa wasu daga cikin jama'ar garin sun fito inda suka gwamutsu da masu cutar a lokacin zanga-zangar.

  3. Burtaniya ta sha gaban kasashen Turai a mutuwar korona

    Burtaniya ta sha gaban dukkan kasashen Turai wajen yawan mutanen da suka mutu sakamakon cutar korona.

    Alkaluma na baya-bayan nan na cewa Burtaniya ta zarce Italiya, wadda a baya ita ce ke kan gaba, inda fiye da mutum 29,000 zuwa jiya Talata suka mutu.

    Sai dai Ofishin Kididdiga na Kasar ya ce yawan mamatan ya zarce wanda ake fitarwa a hukumance.

  4. Coronavirus ta sa an rufe gidan talbijin na NTA da ke Katsina

    NTA

    Asalin hoton, FACEBOOK/NTA

    Sakamakon fargabar bullar cutar korona a gidan talbijin na kasa reshen jihar Katsina, NTA Katsina, shugaban gidan talbijin din na kasa, Malam Yakubu Ibn Muhammad ya yi umarni da a rufe tashar sannan a yi mata feshi kafin a sake bude ta.

    Bayanai da BBC ta samu daga ma'aikatan na NTA Katsina sun cewa Janar Manajan tashar, Ayinde Soaga ya kamu da cutar ta korona inda tuni aka killace shi.

    Har wa yau, majiyar ta kara tabbatar wa da BBC cewa "yanzu haka akwai jerin sunayen ma'aikata 19 zuwa 20 da ake sa ran za a yi wa gwaji domin sanin halin da suke ciki sakamakon mu'amila da suka yi da shugaban nasu."

    Mista Soaga ne dai mai kula da yada labarai na kwmaitin yaki da cutar korona da jihar Katsina ta kafa.

    Jihar Katsina dai na da mutum 92 da ke dauke cutar ta korona ya zuwa daren jiya Talata, kamar yadda hukumar NCDC mai dakile yaduwar cututtuka ta sanar.

  5. Amurka za ta rushe kwamitin annobar korona

    Donald Trump

    Asalin hoton, Getty Images

    Fadar White House na shirin rushe kwamitin yaki da cutar korona da ke tsara ayyukan kai dauki ga annobar a tsawon wata guda, duk da karuwar mutanen da suke kamuwa.

    Shugaba Trump ya ce kwamitin ya yi gagarumin aiki amma ana bukatar wanda zai maye gurbinsa don sake bude harkoki a Amurka cikin aminci.

    “Mike Pence da kwamitin kar-ta-kwanan sun yi gagarumin kokari amma yanzu muna duban wani al'amari ne daban, al'amarin kuma shi ne sake bude harkoki cikin aminci. Don haka ne mai yiwuwa mu kafa wani kwamitin na daban."

    Fadar White House na ci gaba da fuskantar matsin lamba don ta sake bude tattalin arziki a wannan shekarar zabe, sai dai har yanzu dumbin mutane suna mutuwa saboda cutar.

    Amurkawa sama da 2, 300 ne suka mutu cikin sa'a 24 da ta wuce, daya daga cikin adadi mafi yawa na mace-macen da aka samu tun bayan fara annobar

  6. Coronavirus: Gwamnatin Lebanon ta kwashe jama'arta daga Kano

    Lebanon

    Asalin hoton, Getty Images

    Gwamnatin kasar Labanon ta kwashe ‘yan kasarta sama da 100 da ke zaune a Najeriya saboda fargabar yaduwar cutar korona.

    Yawancin wadanda aka kwashen dai mazauna jihar Kano ne wadda ke ci gaba da jan hankalin al'umma sakamakon karin adadin masu dauke da cutar korona da ake samu da kuma mace macen al’umma da har yanzu ba a kai ga gano dalili ba.

    A ranar Talata ne dai kungiyar likitocin reshen jihar ta Kano ta ce likitoci 34 sun kamu da cutar korona inda daya daga ciki ya rasu.

    Ya zuwa daren Talata dai, hukumar NCDC mai dakile yaduwar cututtuka ta Najeriya ta ce adadin masu cutar korona a jihar ta Kano ya kusa 400.

  7. Budewa

    Masu bibiyarmu barkanku da safiya. Da fatan kun tashi lafiya. Ku ci gaba da kasance wa da bbchausa.com domin samun labarai da dumi-duminsu kan annobar korona a fadin duniya.