Wannan shafi na kawo muku bayanai kai tsaye dangane da annobar korona da ke yi wa duniya fyaden 'ya'yan kadanya.
Rahoto kai-tsaye
Usman Minjibir, Awwal Ahmad Janyau and Nasidi Adamu Yahaya
Rufewa
A nan muka zo karshen labarai da rahotannin da muke kawo muku a wannan shafi. Sai ku tare mu gobe da safe inda za mu ci gaba da kawo muku labaran da suka shafi rayuwarku. Kafin nan, za ku iya zuwa kasa domin karanta labaran da muka wallafa. Za kuma ku iya bibiyarmu a shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawara da bayyana ra'ayoyinku.
Mun gode
Gwamna Zulum ya tsawaita dokar kulle a Borno
Gwamnan jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya, Farfesa Babagana Zulum, ya tsawaita dokar kullen da aka sanya a jihar.
A jawabin da ya yi wa mazauna jihar ranar Laraba da maraince, Gwamna Zulum, ya ce an tsawaita dokar kullen ne da mako daya.
Ya ce tun da farko an sanya dokar ne domin dakile yaduwar cutar korona, yana mai cewa ko da yake matakin ba shi da dadi amma ya zama wajibi.
"Ina tsawaita dokar kulle da mako daya amma za a sassauta dokar gobe Alhamis, 7 ga wata da Juma'a, 8 ga wata da kuma Litinin, 11 ga watan Mayu, 2020 inda za a fito daga karfe 8 na safe zuwa 5 na yamma domin mutane su samu damar yin harkokin kasuwanci da bude kasuwanni yadda iyalai za su samu damar sayen abinci," in ji Gwamna Zulum.
Ya kara da cewa za su yi nazari kan matakin ranar 31 ga watan Mayu sannan kwamitin da ke aiki don dakile yaduwar cutar korona zai sanar da sabbin matakai na gaba.
Mutum 106 ne suka kamu da cutar korona a jihar ta Borno ya zuwa ranar Talata, 5 ga watan Mayu, 2020.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.
Karshen labarin da aka sa a X
Labarai da dumi-dumi, Matawalle ya nada sabon Sarkin Ƙauran Namoda
Gwamnan jihar Zamfara da ke arewacin Najeriya, Bello Mohammed (Matawallen Maradun), ya amince da nadin Alhaji Sanusi Mohammed a matsayin sabon SarkinƘauran Namoda.
Sanarwar da kakakin gwamnan, Zailani Bappa, ya aike wa manema labarai ranar Laraba ta ce gwamnan ya amince da nadin ne bayan shawarar da Majalisar Masarautar Ƙauran Namoda ta ba shi.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.
Karshen labarin da aka sa a X
Buhari ya yi wa Sarkin Daura addu’ar samun lafiya
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi addu'ar samun saukin rashin lafiyar da Sarkin Daura, Alhaji Umar Farouk Umar yake fama da ita.
Wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasar Malama Garba Shehu ya aike wa manema labarai ranar Laraba ta ambato shugaban kasar yana cewa ya "samu labarin rashin lafiyar ba-zata ta sarkin cike da tashin hankali kuma yana yi masa fatan samun sauki cikin gaggawa."
"Ina bin sahun masarautar Daura da dukkan al'ummar jihar Katsina wajen yi wa Sarki Alhaji Umar Farouk Umar addu'ar samun sauki cikin gaggawa," in ji Shugaba Buhari.
A ranar Talata ne aka kwantar da Sarkin na Daura a asibitin gwamnati da ke Katsina sakamakon larurar da ba a bayyana ba.
Wata majiya a fadar, wadda ba ta son a ambaci sunanta, ta shaida wa BBC cewa an fitar da Sarkin ne daga fadarsa da misalin karfe dayan dare na Talata inda aka garzaya da shi zuwa birnin Katsina.
Majiyar ta kara da cewa an kai Sarkin na Daura bangaren kulawar gaggawa na asibitin gwamnatin jihar. To sai an ce Sarkin yana samun sauki.
Kimanin kwanaki uku kenan dai da killace fadar Sarkin Daura bisa fargabar barkewar cutar korona a cikinta.
Gwamna Aminu Masari na Katsina dai ya ce tuni aka dauki samfurin majinar mutum 89 daga fadar domin yin gwaji.
Asalin hoton, Facebook/Sarkin Daura supported group
Masu cutar korona sun tsere daga cibiyar kula da su a Oyo
Gwamnan jihar Oyo da ke kudu maso yammacin Najeriya, Seyi Makinde, ya ce biyu daga cikin mutum 33 da ke dauke da cutar korona sun tsere daga cibiyar kula da su.
Gwamnan ya bayana haka ne a sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter ranar Laraba.
"Mun karbi karin sakamakon mutane 19 da ake jiran sakamakon gwajinsu na COVID-19. Sakamakon daya daga cikinsu ya nuna cewa ya kamu da cutar ranar 03/05/2020.Mutumin yana Ibadan.
"Sannan cikin mutanen da aka yi wa gwaji ranar 5 ga watan Mayu, mutum biyar sun kamu da ita," a cewar Gwamna Makinde.
Ya kara da cewa,"Daga cikin mutum 33 da ke dauke da cutar wadanda gwamnatin jiha ke kula da su, biyu sun tsere, watakila zuwa gidajensu. Yanzu hakan ya sa muna da masu dauke da cutar korona 31 a Oyo.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.
Karshen labarin da aka sa a X
Haihuwa a jirgi ta kawo tsaikun dawo da ‘yan Najeriya
Jirgin da ya kwaso ƴan Najeriya daga Dubai ya koma bayan wata mata ta haihu a cikin jirgin jim kadan da tashinsa zuwa Legas.
Sanarwar da hukumar da ke kula da ƴan Najeriya mazauna ƙasashen waje ta fitar, ta ce matar ta haifi namiji a cikin jirgin Emirates da ke ɗauke da ƴan Najeriya, minti 30 bayan ya baro Dubai.
Wannan ne ya tilastawa jirgin koma wa zuwa Dubai saboda matar, a cewar sanarwar.
Ta kara da cewa, matar tana asibiti yanzu haka ana kula da lafiyarta da ta jaririnta waɗanda ke cikin koshin lafiya.
Sanarwar ta ce an sauya jirgin, kuma yana kan hanya zuwa Legas ɗauke da ƴan Najeriya 265.
A ranar Talata ne ma'aikatar ƙasashen waje ta Najeriya ta ce za ta fara kwashe ƴan kasar da suka maƙale a wasu ƙasashe sakamakon hana tafiye-tafiye saboda annobar korona.
Ta ce za a kwaso tawagar farko ta 'yan Najeriya 265 ne daga Dubai a ranar Laraba, sannan kuma a kwaso mutum 300 daga Landan.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.
Karshen labarin da aka sa a X
Najeriya ta tsawaita hana zirga-zirgar jiragen sama
Gwamnatin Najeriya ta tsawaita hana zirga-zirgar jiragen sama na tsawon wata ɗaya.
Sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha ne ya sanar da matakin kamar yadda Lauretta Onochie mai taimakawa shugaba Buhari kan kafofin sadarwa na Intanet ta wallafa jawabinsa a Twitter.
Boss Mustapha da ke jagorantar kwamitin shugaban kasa kan cutar korona, yayin da yake jawabi a taron manema labarai a ranar Laraba ya ce bayan tantance halin da ake ciki a harakar zirga-zirgar jiragen sama, "mun yanke shawara bisa gaskiyar abubuwa da shawarwarin masana, an tsawaita dukkanin zirga-zirgar jiragen sama na tsawon mako hudu.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.
Karshen labarin da aka sa a X
Gwamnati ta tilasta wa ‘yan kasuwa rage farashin suga a Kano
Gwamnatin Kano ta tilasta wa ƴan kasuwa a jahar Kano sassauta farashin kayan
masarufi bayan sun yi tashin gwauron zabi a
kasuwanni jahar.
Gwamnatin ta ce ta
yi wa ƴan kasuwar dirar mikiya ne inda ta kama kayayyakin da wasu ƴan kasuwa
suka ɓoye musamman na abinci.
Muhuyi Magaji
Rimin Gado shugaban hukumar karɓar ƙorafe-ƙorafe na jihar Kano ya shaida wa BBC
cewa sun kama kayayyakin abinci da suka hada da fulawa da taliya da suga.
An dai samu tashin farashin kayan masarufi musamman suga wanda farashin sa
ya kai sama da naira dubu 20, tun bayan da aka rufe kasuwanin jahar sakamakon
bullar cutar korona a Kano.
Saurari rahoton
wakilin BBC Khalifa Shehu Dokaji
Bayanan sautiRahoton wakilin BBC Khalifa Shehu Dokaji
Ana ce-ce-ku-ce kan ko shugaban Liberia na da korona
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Shugaban Liberia George Weah
Ana ce-ce-ku-ce a Manrovia babban birnin Liberia kan yadda shugaban kasar George Weah ya ƙi yin gwajin cutar korona da kuma killace kansa bayan ministansa na watsa labarai ya harbu da cutar.
Gwaji ya tabbatar da Eugene Nagbe ya kamu da korona, kwana uku bayan an gan shi a zaune kusa da shugaba Weah.
Yayin da wasu ke ganin ya kamata shugaban ya je a gwada shi kuma ya killace kansa, amma an gan shi a cikin jama'a yana raba abin rufe hanci da baki.
Shugaban cibiyar lafiyar al'umma Dr Mosoka Fallah ya kasa amsa tambayar cewa ya ba shugaban kasar shawara a tafi a gwada shi yayin da yake bayani kan halin da ake ciki kan cutar korona a wani shirin rediyo.
Ya ce tambayar ta shafi siyasa, ba zai iya amsawa ba.
Fadar shugaban ta tabbatar da cewa ba a yi masa gwaji ba bayan mu'amularsa da ministansa.
Kotu ta yanke wa wani hukuncin kisa ta Intanet a Najeriya
Asalin hoton, Getty Images
Wata kotu a Najeriya ta yanke hukuncin kisa karon farko ta Intanet a Legas bayan rufe kotuna don gudun yaduwar cutar korona.
An yanke wa Olalekan Hameed hukuncin kisa ta hanyar rataya, a zaman kotun da aka gudanar tsawon sa'a uku ta kafar bidiyo a Zoom.
Mai shari'a Mojisola Dada ne ya zartar da hukuncin kan Olalekan Hameed kan laifin kashe mahaifiyar mai gidansa da yake yi wa aikin direba.
Masu rajin kare hakkin dan adam dai sun soki hukuncin, duk da cewa da farko sun yi maraba da sabon tsarin gabatar da shari'a ta intanet saboda cutar korona.
Yadda Barcelona da Real Madrid suka dawo atisaye
Asalin hoton, fcbarcelona
An fara yi wa ƴan wasan Barcelona da Real Madrid gwajin cutar korona a
ranar Laraba yayin da ƴan wasan za su fara yin atisaye domin shirin wasannin
La Liga da za a dawo a watan gobe.
Lionel Messi da Antoine
Griezmann suna cikin ƴan wasan da Barcelona ta wallafa hotunansu
a Facebook lokacin da suka fito atisaye ranar Laraba.
Asalin hoton, fcbarcelona
Asalin hoton, fcbarcelona
Asalin hoton, fcbarcelona
Real Madrid ta wallafa a Twitter cewa ƴan wasanta na shirin dawo wa
atisaye.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.
Karshen labarin da aka sa a X
Ƴan wasan Madrid ma da suka hada da Eden Hazard da Karim Benzema, an diba
lafiyarsu kafin fita atisaye.
Za a ɗauki sa’a 48 kafin fitowar sakamakon gwaji. Gwajin kuma na cikin
matakan farko da ake son ƙungiyoyi su kiyaye kafin dawo wa atisaye.
Cutar korona ta kashe mutum sama da 20,000 a Spain, kuma ɗaya daga cikin ƙasashen Turai da cutar ta fi bazuwa.
Najeriya za ta kwaso 'yan kasarta daga kasashen waje
Ma'aikatar kasashen waje ta Najeriya ta ce za ta fara kwashe 'yan kasar da suka makale a wasu kasashe sakamakon hana tafiye-tafiye saboda annobar korona.
Za a kwaso tawagar farko ta 'yan Najeriya 265 ne daga Dubai a ranar Larabar nan, sannan kuma a kwashi mutum 300 daga Landan.
Ma'aikatar ta kuma kara da cewa ana sa ran karin wasu 'yan Najeriya su koma kasar daga New York na Amurka.
Sai dai kuma ma'aikatar ta ce dole ne mutanen da za a mayar kasar sai an killace su na mako biyu
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.
Karshen labarin da aka sa a X
A karon farko mutum uku sun warke daga cutar korona a Kano
A karon farko an samu mutum uku da suka warke daga cutar korona inda kuma ma'aikatar lafiyar kasar ta ce ta sallame su.
Hakan dai na dauke a wata sanarwa da ma'aikatar lafiyar jihar ta wallafa a shafinta na Twitter.
Sanarwa ta kuma kara da cewa a daren Talata an samu karin mutum 32 da suka kamu da cutar a fadin jihar.
Adadin masu cutar korona a jihar Kano yanzu ya kai 397, kamar yadda ma'aikatar ta sanar.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.
Karshen labarin da aka sa a X
Masari ya kafa dokar hana fita a Malumfashi
Gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari ya kafa dokar hana fita a ƙaramar hukumar Malumfashi sakamakon ɓullar cutar korona a yankin.
Gwamnan ya wallafa a Twitter cewa ɓullar cutar a Malumfashi ne ya ƙara yawan masu korona daga alkalumman da hukumar daƙile cutuka masu yaɗuwa ta fitar NCDC game da Katsina a ranar Talata.
Ya ce dokar kullen a Malumfashi za ta fara aiki daga ƙarshe 7 na safiyar Alhamis har sai yadda hali ya yi.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.
Karshen labarin da aka sa a X
An kwantar da Sarkin Daura
Asalin hoton, Facebook/Sarkin Daura supported group
An kwantar da Sarkin Daura, Umaru Farouk a asibitin gwamnati da ke Katsina ranar Talata sakamakon larurar da ba a fayyace ba.
Wata majiya a fadar wadda ba ta son a ambaci sunanta ta shaida wa BBC cewa an fitar da Sarkin ne daga fadarsa da misalin karfe dayan dare na Talata inda aka garzaya da shi zuwa birnin Katsina.
Majiyar ta kara da cewa an kai Sarkin na Daura bangaren kulawar gaggawa na asibitin gwamnatin jihar. To sai an ce Sarkin yana samun sauki.
Kimanin kwanaki uku kenan dai da killace fadar Sarkin Daura bisa fargabar barkewar cutar korona a cikinta.
Gwamna AMinu Masari na Katsina dai ya ce tuni aka dauki samfurin majinar mutum 89 daga fadar domin yin gwaji.
'Nijar ta karɓi ganyen shayin Madagascar don maganin korona'
Asalin hoton, Getty Images
Rahotanni sun ce Nijar ta karɓi ganyen tazargade da za a iya shayi da shi wanda shugaban Madagascar Andry Rajoelina ya ce yana maganin cutar korona.
Kamfanin dillacin labaran AFP ya ambato jami'i a ma'aikatar lafiya Souley Zaberou na tabbatar da cewa sun karɓi ganyen kyauta daga Madagascar.
Madagascar ta yi iƙirarin cewa ganyen tazargade ya warkar da masu cutar korona cikin kwana 10, kuma tana fatan rabawa sauran kasashen Afirka domin maganin cutar.
Hukumar lafiya ta duniya ta ce gwaji bai tabbatar da ganyen yana maganin korona ba, kuma babu wani binciken masana da ya tabbatar da yana magani.
Nijar na da mutum 755 da suka kamu da korona zuwa yanzu, yayin da cutar ta kashe mutum 37 ciki har da ministan ƙwadago Mohamed Ben Omar, kamar yadda alƙalumma na baya bayanan da suka nuna.
Dililin mayar da Almajirai 80 Nasarawa – Gwamnatin Taraba
Gwamnatin jihar Taraba a arewacin Najeriya ta kare matakinta na mayar da
almajirai sama da 80 ƴan asalin jihar da aka mayar mata daga Nassarawa.
Kwamishin labaran jihar Taraba, Danjuma Adamu ya ce rashin bin ƙa’ida wajen mayar da almajiran ya sa, ba su da zaɓi face su mayar da su inda suka fito.
Ya ce ya kamata
ace an gwada almajiran kafin a ɗauko su zuwa jiharsu ta asali, kamar yadda aka amince
a taron ƙungiyar gwamnoni.
“Ya kamata a gwada
almajiran kuma idan za a mayar da su ya kasance suna ɗauke
da shedar cewa an yi masu gwaji.”
“Rashin bin ƙa’idar
ya sa muka mayar da almajiran inda suka fito jihar Nasarawa,” in ji shi.
Asalin hoton, @SankaraJgh
Bayanan hoto, Gwamnatin Jigawa ta yi wa almajirai 500 gwaji da aka dawo su daga Kano
Fiye da kashi biyu cikin uku na waɗanda aka gudanar da bincike akansu a ƙasashen Afirka 20 sun ce za su faɗa cikin yunwa na rashin abinci da ruwan sha idan har suka ci gaba da kasancewa a gida na tsawon makwanni biyu.
Kusan rabin mutanen da aka yi magana da su sun ce za su shiga cikin matsalar kuɗi.
Binciken na hukumar daƙile cutuka masu yaɗuwa a Afirka, an gudanar da shi ne domin taimakawa gwamnatoci ɗaukar matakan da suka dace wajen shawo kan annobar korona.
Binciken ya yi gargaɗin cewa idan har matakan da aka ɗauka sun saba wa bukatun mutane, akwai barazanar zanga-zanga da rikici.
Rahoton wanda ya yi amfani da alƙalumma wajen samun daidaito ya nuna cewa akwai ƙalubale wajen tabbatar da dokar kulle a nahiyar.
An gudanar da binciken ne a birane 28 na ƙasashen Afirka 20 domin gano tasirin rikicin da kuma halayen mutane lokacin da aka kafa dokar kulle.
Ƙasashen Afirka da dama sun sassauta dokar a yanzu saboda wannan barazanar.