An amince da Remdesivir a matsayin maganin korona

Wannan shafi yana kawo muku bayanai kai tsaye dangane da annobar korona da ke ci gaba da yi wa duniya fyadar 'ya'yan kadanya.

Rahoto kai-tsaye

Buhari Muhammad Fagge and Umar Mikail

  1. Sudan ta haramta kaciyar mata

    Getty

    Asalin hoton, Getty Images

    Sudan ta sanya yi wa mata kaciya cikin jerin manyan laifuka a kasar, tare da tanadin daurin shekara uku ga duk wanda aka kama na aikata al'adar, kamar yadda sabuwar dokar da aka sauya ta zayyana.

    Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito cewa an tabbatar da sauya dokar zuwa cikin jerin manyan laifuka ne a ranar 22 ga watan Afrilu.

    Sudan na daya daga cikin kasashen Afrika da aka yi amanna da kaciyar mata a kusan baki dayan kasar.

    Akalla kasashen Afirika 27 ne ke yin wannan al'ada ta kaciyar mata a nahiyar, kamar yadda Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana.

    Amma tuni wasu kasashen da dama suka haramta wannan al'ada wadanda suka hadar da Kenya da Mali da Liberia da Benin da Burkina Faso da kuma Central African Republic.

    Sauran sun hada da Chadi da Côte d'Ivoire da Djibouti da Masar da Eritrea da Habasha da Ghana da Guinea da Guinea-Bissau da Niger sai kuma Najeriya.

  2. Trump bai yarda da rahoton hukumomin leken asirinsa ba kan asalin korona

    Donald Trump

    Asalin hoton, Getty Images

    Da alama Shugaban Amurka Donald Trump bai yarda da binciken da hukumomin leken asirin Amurka suka yi ba na cewa China ba ta krikiri cutar korona da gangan ba.

    Shugaban ya hakikance cewa yana da hujja cutar ta samo asali ne daga wani dakin gwaji a kasar ta China, abin da ya ci karo da rahoton binciken da hukumomin kasarsa suka bayar ranar Alhamis.

    Tun farko ofishin babban darakta a hukumar leken asirin Amurka ya ce har yanzu suna ci gaba da bincike kan yadda cutar ta samo asali, amma ya ce "ba kirkirar ta aka yi ko kuma sauya kwayar halitta".

    China ta yi watsi da maganar cewa daga dakin gwajinta annobar ta faro sannan ta soki salon Amurka na yaki da cutar.

    Tun daga sanda ta bayyana a China a shekarar da ta gabata, kwayar cutar korona da ake yi wa lakabi da Covid-19 ta kashe fiye da mutum 230,000 a duniya, ciki har da 63,000 a Amurka.

  3. Watakila a samu koma-baya a yakin da ake yi da annobar korana Kano

    Korona

    Asalin hoton, Getty Images

    Watakila a samu koma-baya a yakin da ake yi da annobar korana a jihar Kano sakamakon ja da baya da likitoci suka yi a asibitin koyarwa na Mallam Aminu Kano da ke Kano.

    Likitocin dai suna kukan rashin kayan kariya, lamarin da suka ce yana jefa su cikin hadarin harbuwa da cutar korona.

    Likitocin, wadanda ke rukunin masu neman kwarewa a asibitin koyarwa na Mallam Aminu Kano sun samu kan su a wani mawuyacin hali a Kano, musamman yadda dawainiya ta karu ta kula da marasa lafiyar da ke kwarara asibitin.

    Kuma lamarin ya ta`azzara a dan tsakanin nan da aka samu karuwar mutuwar mutane masu yawan shekaru.

    Shugaban kungiyar likitoci masu neman kwarewar, reshen asibitin Mallam Aminu Kano, Dr Abubakar Nagoma ya ce aikin da suke yi ya karu, ga shi suna fama da karancin kayan kariya.

    “Aiki ya tsaya cak saboda baka san me zaka taba ko ka gani”, inji Dokta Abubakar.

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da gwamnatin jihar Kano, duka sun yi alwashin tallafa yin tsayin-daka wajen ceto rayukan al`ummar jihar Kano daga annobar korona, kuma tallafa wa irin wannan asibitin zai nuna da gaske suke yi.

  4. Fiye da mutum 200 sun kamu da korona a arewacin Najeriya cikin kwana biyu

    Cibiyar killace masu korona a Kano
    Bayanan hoto, Cibiyar killace masu korona a Kano da ke Filin Wasa na Sani Abacha

    Jumillar mutum 208 ne suka harbu da annobar cutar korona a jihohin arewacin Najeriya cikin kwana biyu da suka gabata, kamar yadda alkaluman hukumar NCDC mai dakile yaduwar cutuka a Najeriya suka nuna.

    Alkaluman ranar Laraba sun nuna cewa mutum 85 ne suka harbu a jihohin Kano da Gombe da Kaduna da Katsina da Sokoto da Borno da Adamawa da kuma Yobe, wadda ta samu bullar cutar a karon farko.

    Sai kuma alkaluman ranar Alhamis da suka bayyana mutum 123 da suka harbu da ita a jihohi takwas da suka hada Kano da Gombe da Bauchi da Sokoto da Borno da Kaduna da Nasarawa da Kebbi.

    Jihar Kano ce kan gaba a arewacin Najeriya a yawan masu dauke da cutar, inda ya zuwa 30 ga watan Afrilu take da mutum 219. Hakan ya sa ta zama ta biyu a kasar baki daya, inda take bin Legas, wadda ke da 976.

    NCDC ta ce jumillar mutum 1932 ne suka harbu da cutar a Najeriya ya zuwa yanzu tare da mutuwar mutum 58, da kuma 319 da suka warke.

    Cutar ta bulla a jihohin Najeriya 34 ciki har da Abuja - jihohin Kogi da Cross River ne ba ta fantsama ba zuwa yanzu.

  5. Likitoci sun yi watsi da hujjar gwamnatin Kaduna ta rage wa ma'aikata albashi

    Nasir El-Rufai

    Asalin hoton, @govkaduna

    Likitoci a jihar Kaduna ta Najeriya sun yi watsi da hujjojin da gwamnatin jihar ta bayar na rage wa ma’aikatan jihar albashi da kashi 25%.

    A farkon makon nan ne gwamnatin ta sanar da yin ragin albashin ga ma’aikatan da ke daukar albashin da ya haura naira dubu 67 zuwa sama domin samun abin da za a tallafa wa masu karamin karfi.

    Dr. Emmanual Joseph shugaban kungiyar likitocin ta kasa reshen Kaduna ya ce hgar an fara yankar albashinsu na watan Afrilu.

    "Sun fara (yankar albashi) ba su yi mana magana ba," in ji shi. "Maimakon gwamnati ta yaba mana kan aikin da muke yi sai ta zo da dorina ta yi mana duka."

    Ya ci gaba da cewa: "Babbar kungiyarmu ta kasa ta rubuta musu cewa ba mu yarda da wannan magana ba. Muna jiran martanin gwamnatin tukunna kafin mu dauki mataki na gaba."

  6. Coronavirus: Wadanda suka warke a duniya sun zarta miliyan daya

    Coronavirus

    Asalin hoton, Getty Images

    Adadin wadanda suka warke daga annobar cutar korona a fadin duniya sun zarta miliyan daya, a cewar sabbin alkaluman Jami'ar Johns Hopkins da ke Amurka.

    Mutum 1,014,931 ne jami'ar ta ce sun warke, kuma Amurka ce kan gaba a yawan wadanda suka warke din da kuma wadanda suka kamu da cutar.

    • Amurka: 153,947 (cikin jumillar mutum 1,070,026)
    • Jamus: 123,500 (cikin jumillar mutum 163,009)
    • Spaniya: 112,050 (cikin jumillar mutum 213,435)
    • China 78,523 (cikin jumillar mutum 83,956)
    • Italiya 75,945 (cikin jumillar mutum 205,463)
  7. Masu cutar korona a Najeriya sun doshi 2,000

    Coronavirus

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumar da ke dakile cutuka masu yaduwa a Najeriya ta ce mutum 204 sun sake kamuwa da cutar korona cikin sabbin alkaluman da ta fitar na ranar Alhamis, don haka jumillar masu cutar ya zama 1,932 a Najeriya.

    Cikin wani sakon Twitter da ta fitar a daren Alhamis da karfe 11:50, hukumar NCDC ta ce mutum bakwai Allah Ya yi wa rasuwa cikin sa'a 24 da ta wuce sakamakon korona a kasar.

    Sai dai, wani abin farin ciki shi ne masu cutar 12 ne suka warke a ranar Alhamis.

    Har yanzu jihar Legas, inda korona ta fara bulla a Najeriya ce ke kan gaba a yawan mutanen da suka kamu da cutar ta korona, inda a yanzu take da mutum 976.

    A yanzu dai Kogi da Cross river ne kawai a Najeriya annobar ba ta kai gare su ba.

  8. Barka

    Jama'a barkanmu da wannan babbar rana ta Juma'a kuma ranarmu - mu ma'aikata mana - da fatan kun tashi lafiya.

    Umar Mikail ke muku barka da shigowa sabon shafinmu da ke kawo labarai kai-tsaye.

    Ku biyo mu don sanin abubuwan da ke faruwa a sassan duniya baki daya, musamman game da annobar korona.