Mun zo karshen rahotanni a wannan shafi
Jama'armu nan muka kawo karshen rahotannin kai-tsaye.
Ku kasance tare da mu gobe idan Alllah ya kai mu.
Umar Mikail ke wa masu azumi fatan su yi sahur lafiya - wadanda ba sa yi kuma su sha barci lafiya.
Wannan shafi yana kawo muku bayanai kai tsaye dangane da annobar korona da ke ci gaba da yi wa duniya fyadar 'ya'yan kadanya.
Buhari Muhammad Fagge and Umar Mikail
Jama'armu nan muka kawo karshen rahotannin kai-tsaye.
Ku kasance tare da mu gobe idan Alllah ya kai mu.
Umar Mikail ke wa masu azumi fatan su yi sahur lafiya - wadanda ba sa yi kuma su sha barci lafiya.

Asalin hoton, @StateHouseKenya
Shugaban kasar Kenya, Uhuru Kenyatta ya kare matakin da ya dauka na tura furanni zuwa ga ma'aikatan lafiya na Birtaniya.
Ya ce hakan wata dama ce ta yin talla, sai dai ya sha kakkausar suka daga 'yan kasarsa bisa barnar kudi ya yi yayin da Kenya take fama da karancin gadajen kula da masu jinyar cutar korona.
Ya zuwa yanzu, wadanda suka harbu da cutar korona a Kenya sun kai 396, 17 sun mutu, sai kuma 144 da suka warke.

Asalin hoton, Reuters
A wannan makon ne kasar Brazil ta kai wani mataki maras dadin ji a yawan adadin wadanda suka harbu da cutar korona da kuma wadanda ta kashe, inda suka zarta na China - wurin da annobar ta faro.
Lamarin yana kara rincabewa kuma da alama yanayin zai kara munana a makonni masu zuwa.
Hotunan da ke fitowa daga birnin Manaus, mafi girma a yankin Amazon, na da tayar da hankali.
Mutane na haka katon kabari domin binne mamata da yawa a ciki, kuma shi da kansa shugaban birnin ya ce abin ya yi kama da fim din dodo.

Asalin hoton, Getty Images
Hukumuar kula da ingancin abinci da magunguna ta Amurka FDA ta bayar da umarnin fara amfani da kwayar remdesivir a matsayin maganin cutar korona, a cewar Shugaba Donald Trump.
Trump ya ce shugaban kamfanin Gilead, wanda ya samar da kwayar, ya bayyana yunkurin a matsayin mai matukar amfani kuma irinsa na farko, sannan zai bayar da kyautar kwalabar allurar miliyan daya.
Mataimakin Trump, Mike Pence ya ce za a fara raba maganin zuwa asibitoci a ranar Litinin.
Maganin wanda tun farko aka samar domin magance cutar Ebola, na rage yawan alamun cutar daga 15 zuwa 11 a wani gwaji da Amurka ta yi a asibitoci a fadin duniya.
Kasashen Afirka da suka hada da Najeriya da Masar da Tanzania da Afirka ta Kudu, su ma suna kan yin gwajin wasu magungunan cutar, a cewar hukumar Africa CDC mai yaki da cutuka masu yaduwa a Afirka.

Asalin hoton, Getty Images
'Yan wasan kungiyar FC Cologne ta kasar Jamus guda uku sun harbu da cutar korona, kamar yadda kulob din ya tabbatar.
Kungiyar ta Bundeliga ta ce an yi wa baki dayan tawagarta gwajin korona a ranar Alhamis.
Mutum ukun da suka kamu ba su nuna alamun cutar ba tukunna, a cewar kungiyar, amma za su shafe kwana 14 a killace a gidajensu. Ta ce za a ci gaba da atasaye.
Kulob din bai bayyana wadanda suka harbu da cutar da ake yi wa lakabi da Covid-19 ba.

Asalin hoton, Getty Images
Adadin wadanda suka rasa rayukansu a asibitoci da gidajen kula da gajiyayyu a Faransa ya karu da 218, a cewar gwamnatin kasar.
An samu kari kadan a kan adadin rana kafin wannan, sai dai adadin masu rasuwr na kullum yana raguwa a cikin mako biyu a jere da suka gabata.
Kasar ce ta hudu a jerin wadanda suka fi samun mace-mace a Nahiyar Turai - bayan Italiya da Birtaniya da Spaniya.
Faransa za ta fara sassauta tsauraran dokokin hana fita daga ranar 11 ga watan Mayu, duk da cewa saka takunkumi zai ci gaba da zama wajibi a motocin haya da kuma makarantun sakandare.

Asalin hoton, Reuters
Dan takarar jam'iyyar Democrat da ke fatan karawa da Shugaba Donald Trump a zaben shuganacin Amurka Joe Biden, ya musanta zargin cin zarafin wata tsohuwar mai taimaka masa shekara talatin baya.
Mista Biden ya ce zargin da Tara Reade ta yi masa na yunkurin lalata da ita tsabar karya ce.
Tara Reade na daya daga mata tara da a bara suka yi zargin cewa tsohon mataimakin shugaban kasar da cin zarafinsu.
Zargin na ta shi ne na farko da ya hada da batun lalata.
Joe Biden ya ce yana cikin wadanda suka tabbatar da kare 'yan cin mata Amurkawa, ta hanyar goyon bayan dokar hana cin zarafin mata ta shekarun 1990, kuma zai kammala wannan aiki na sa idan ya zama shugaban kasa.
Hiukumar Lafiya ta Duniya ta tanadi ma'aikata 3,000 a Jihar Kano da za su yi aikin dakile yaduwar cutar korona a jihar.
Shugaban kwamitin gwamnatin tarayya mai yaki da korona, Boss Mustapha ne ya bayyana haka ranar Juma'a a wurin taron manema labarai da kwamitinsa ke yi kullum a Abuja.
Boss Mustapha ya ce wadannan ma'aikata za su shiga cikin al'ummar ne a jihar da nufin tattaro bayanan abubuwan da ke wakana a tsakanin jama'a.
Ya kuma ce tun bayan da aka kafa cibiyar gwajin cutar a Kano al'amura suka fara kyautata ta hanyar gano masu dauke da cutar.
"Majalisar Dinkin Duniya tare da hadin gwiwar Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) na tattara wata tawagar mutum 3,000 daga cibiyoyin lafiya a matakin farko da za ta tattaro bayanai a tsakanin al'umma."

Asalin hoton, KDSG
Gwamnatin jihar Kaduna ta ce daga karfe shida na yamma har zuwa shida na safe babu wanda za a bari ya shiga cikin jihar.
Sanarwar da gwamnati na fitar na cewa da zarar dare ya yi - to babu shiga babu fita a Kaduna ga kowa hadda masu ayyuka na musamman.
A cewar gwamnatin dokar za ta fara aiki ne daga ranar 1 ga watan Mayu.
Sanarwar ta ce matakin ya biyo bayan matsalolin tsaro da ake fuskanta a cikin dare inda bata gari suke ayyukan da aka haramta.
Haka kuma a cewar gwamnatin jihar Kaduna, matakin zai taimaka wajen dakile yaduwar cutar korona a jihar.
Wannan na nufin cewa idan dare yayi to matafiya so koma inda suka fito ko kuma su jira a kan iyakar jihar zuwa wayewar gari domin samun damar shiga cikin jihar.

Asalin hoton, KDSG
Rundunar sojojin Najeriya ta bayyana cewa ta halaka 'yan kungiyar Boko Haram da dama a Parisu da ke Jihar Borno.
Rundunar ta ce dakarun musamman na Operation Lafiya Dole ne suka kai hari ta sama bayan ta samu wasu bayanan sirri da ke cewa 'yan kungiyar na ci gaba da amfani da wasu sansanoni a cikin dajin Sambisa.
Sai dai ba ta bayyana adadin wadanda suka halaka ba a harin, wanda ta kai ranar Alhamis. An lalata maboyar dakarun da dama, a cewar sojojin.
Wani bidiyo da hedikwatar sojojin da ke Abuja ta wallafa a shafinta na Twitter ya nuna yadda ta gudanar harin.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X

Asalin hoton, RSF
'Yan sanda a Sweden sun ce sun gano gawar dan jaridar nan na Pakistan Sajid Hussain, wata biyu bayan ya bata a kusa da birnin Uppsala.
Mista Hussain, wanda shi ne editan Baloch - wata jaridar intanet a Pakistan a 2012 - bayan barazanar kisa da ya fuskanta. Ya kuma samu mafakar siyasa a Sweden.
Tun da farko kungiyar Reporters Without Borders ta yi zargin an sace shi ne bisa umarnin hukumar leken asiri ta Pakistan - ISI.
Sai dai mai nmagana da yawun 'yan sandan Sweden ya shaida wa BBC cewa a binciken da suka fara yi ba su gano ko akwai saba doka a kisan nasa ba.
Mista Hussain ya sha yin rubutu game da yadda mutane ke bacewa dare daya a yankin Balochistan na Pakistan, wanda ya sha fama da rikicin 'yan kishin kasa.
Zimbabwe ta kara yin afuwa ga wasu firsunoni, a wani mataki na fadada matakan kariya daga annobar korona.
Kamar yadda gwamnati ta sanar, a wannan karon afuwar za ta hada da mutanen da aka yi musu daurin rai da rai wadanda suka shafe shara 20 a daure.
Duk da an saki wasu mutum 1,500 a watan Maris amma har yanzu gidan yarin kasar a cunkushe ya ke, da sama da mutum 20,000 a gidan da aka gina zai dauki mutum 17,000.
Haka kuma an yi wa matan da aka yanke wa hukunci kan aikata manyan laifuka afuwa. Za a saki kananan yaran da ke gidan da kuma masu fama da rashin lafiya.
Mazan da suka kwashe kashi daya cikin uku na zaman kasonsu suma za a sake su.
Zimbabwe ta yi afuwa ga gwamman mutane a wannan shekarar domin rage cunkoso a gidajen yari, amma har yanzu ana ci gaba da fuskantar cunkoson da kuma kazanta.
Kamar yadda jami'ai suka bayyana, ana samun raguwar yaduwar cutar korona a Zimbabwe, amma akwai fargabar asibitocin kasar ba za su iya daukar karin adadin masu cutar da ake samu ba.

Asalin hoton, UNICEF
Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa miliyoyin kananan yara na cikin hadarin gaza samun allurar riga-kafi, saboda gaza gudanar da ayyuka kamar yadda ya kamata dalilin cutar korona.
Annobar ta yi matukar tasiri ga harkokin kamfanonin jiragen sama, a hankali ta rage harkokin kamfanonin kasuwancin da kuma na bayar da agaji.
Wannan na nufin cewa kasashen duniya da dama na fuskantar hadarin karewar wannan alluara mai mahimmanci, kamar yadda Asusun Tallafawa Kananan Yara na MDD ya bayyana.
Majalisar ta nemi gwamnatoci da kamfanoni su ba da damar safarar riga kafin.

Asalin hoton, Ghali Naabba/Twitter
Tsohon shugaban majalisar wakilan Najeriya Ghali Umar Naabba ya musanta jita-jitar da ake yadawa a kafafen sada zumunta cewa ya rasu.
A wani hoton bidiyo da ya wallafa a shafukansa na Twitter da Instagram Ghali Naabba ya ce "Ina tabbatarwa da masoyana da kuma dukkan 'yan Najeriya da ma duniya gaba daya ma cewa ina nan lafiyata kalau da raina ban mutu ba"
A cikin bidiyon wanda ya nada cikin harshen Hausa da turancin Ingilishi ya ce abin takaici ne irin yadda ake yada wannan mummunan lanbari a kansa a 'yan kwanaki nan.
"A halin yanzu ina nan London, abinda ya kawo ni na gama yau sati uku ke nan ko hutu"
Ya ce rashin jirgi ne ma ya hana shi komwa Najeriya, sannan da zarar an samu hanya zai koma gida.
Ya ce yana so masoyansa da 'yan Najeriya baki daya su sani cewa, mutuwa na kan kowa kuma in tazo babu makawa sai an tafi.
A wannan makon nan ne aka fara yada jita-jitar cewa tsohon shugaban majalisar wakilan ya rasu, duk da cewa rahotanni sun bayyana cewa ba shi da wata rashin lafiya da ke damun shi.

Asalin hoton, Getty Images
Adadin wadanda suka mutu a Iran saboda korona ya karu da 69 cikin kwana daya, wanda ya mai da adadin wadanda suka mutu a kasar zuwa 6,091 tun daga barkewar cutar.
Kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito mai magana da yawun ministan lafiya na kasar Kianush Jahanpur ya fada cikin wata sanarwa da ya yi a gidan talabijin na kasar a ranar Juma'a.
An samu raguwa duk da adi kadance ta mutuwar idan aka kwatanta da wadanda aka sanar 71 kafin Juma'ar.
Yawan wadanda ke dauke da cutar a kasar yanzu ya kai 95,646, inda aka samu karin mutum 1,006 kan adadin a ranar Alhamis.
Iran da ke da yawan mutane miliyan 80, ta fi kowacce kasa yawan wadanda suka mutu a yankin gabas ta tsakiya.

Asalin hoton, Getty Images
Firaiministan Japan Shinzo Abe ya ce zai iya tsawaita dokar ta baci a kasar har na tsawon wata guda.
Mista Abe ya ce zai bayyana matsayarsa ta karshe kan batun, bayan yayi nazari kan shawarwarin da masa suka ba shi, wadanda ke cewa duk da ana samun raguwar masu dauke da cutar amma har yanzu yanayin bai yi kyau ba kamar yadda kasar take fata.
Dokar ta bacin da ake ciki yanzu za ta kare ne a ranar 6 ga watan Mayu. Mista Abe ya ce zai bayyana matsayarsa ta karshe a ranar Litinin.
"Saboda kokarin da 'yan kasarmu suka yi, mun yi nasarar dakile karuwar yawan masu cutar kamar yadda muka gani a baya," ya shaida wa manema labarai.
"Amma yanayin da tsarin kiwon lafiya yake ciki ya sa dole mu yi kira ga 'yan kasarmu wajen kara bamu hadin kai."
Japan da ke da yawan mutane miliyan 126, na da mutanen da ke da korona sama da 14,000 kuma tuni 430 suka mutu dalilin cutar, kamar yadda jami'ar Johns Hopkins ta bayyana.

Asalin hoton, Getty Images
Gwamnatin Faransa ta fitar da taswira kan yadda za ta fara sassauta dokar hana fitar da ta kakaba a kasar domin yaki da cutar korona.
Taswirar tana nuna yankunan da cutar ta fi muni da kuma inda asibitoci ke fama da aikin da ya fi karfinsu.
An rarraba yankunan zuwa masu launin ja da ruwan dorawa da kuma kore, ciki har da inda cutar ta fi kamari.
Za a iya janye dokar a yankunan da ke da launin kore, in ji gwamnati.
Akwai mutum 289 da suka mutu a Faransa a ranar Alhamis, wanda ya kai adadin mutanen da suka mutu a kasar zuwa 24,376.

Asalin hoton, Getty Images
A Spaniya adadin wadanda suka mutu ya karu zuwa 24,824 a ranar Juma'a, yayin da mutum 281 suka mutu saboda cutar korona. Wasu 268 sun mutu a ranar Alhamis.
Ministan lafiya na kasar ya ce adadin masu dauke da cutar korona yanzu ya karu zuwa 215,216 a kasar, adadin da a ranar Alhamis ya ke a 213,435.
Spaniya na daya daga cikin kasashen da cutar korona ta yi wa mummunan tasiri, a baya-bayan nan ta sanar da wasu tsare-tsare hudu da take yi na saukaka dokar hana fita da ta kakaba nan da karshen watan Yuni.

Asalin hoton, Getty Images
Ministan lafiya na Najeriya ya yi roko ga masu gine-ginen da babu mutane ciki, da su ba wa gwamnati aro domin mayar da su cibiyoyin killace wadanda ke gida da aka gwada suna da korona.
Dr Osagie Ehanire ya ce za a iya bai wa gwamnatin jihohi gudunmawar gine-ginen da babu kowa ciki don amfani da su na wani dan lokaci.
Bayanin nasa na zuwa ne bayan da daraktan hukumar yaki da cutuka masu yaduwa ta kasar ya ce, jami'ansu na fama da matsalar karancin dagajen da za a aje marasa lafiya a wasu yankuna a kasar.
Ya kara da cewa akwai bukatar mayar da hankali kan jihar Kano da kuma birnin tarayyar Abuja, amma Legas inda nan ce cutar ta fara billa a kasar "ita ce babban kalubalensu".
Ya ce tawagarsa na duba wasu hanyoyin da za a iya amfani da su ciki har da gidajen raino, amma yanzu haka suna aiki tare da gwamnatocin jijoji domin kawo karshen wannan matsala.

Asalin hoton, AFP
Babbar jam'iyyar adawa a Tanzaniya Chadema, ta shaida wa 'yan majalisarta su killace kansu na akalla mako biyu, kuma su daina zuwa ginin majalisar da ke babban birnin kasar Dodoma da kuma cibiyar kasuwancin kasar Dar es Salaam.
Chadema ta kuma shawarci kakakin majalisar da a dakatar da duka wani zaman majalisar, a matsayin wani matakin kariya daga yaduwar annobar korona.
'Yan majalisa uku ne suka mutu cikin kasa da mako biyu a kasar, duk da cewa mutuwar tasu ba ta da alaka da cutar korona.
Kazalika gwamnatin kasar na fuskantar suka kan cewa ba ta dauki matsalar cutar da muhimmanci ba, da kuma rashin kakaba dokoki masu tsauri na takaita yaduwar cutar.
Akawai mutum 480 da ke dauke da cutar korona a Tanzaniya ya zuwa yanzu, 16 kuma sun mutu.