Coronavirus: Fursunoni sun kona gidan yari a Sierra Leone
Fursunoni a Sierra Leone sun yi yunkurin ballewa daga gidan yari sakamakon wasu da suke zargin na da cutar korona da aka kai jarun din.
An kashe mai tsaron fursunonin guda daya yayin hatsaniyar inda kuma mutane da dama suka samu raunuka a gidan yarin da ke kan titin Pandemba Road a birnin Freetown. An dai kone gidan yarin.
Gidan yarin Pandemba Road na cin mutum 300 bisa ka'ida amma yanzu haka yana da fursunoni 1,000.
An dakatar da yanke hukunce-hukunce tun bayan rufe kotuna sakamakon matakin hana bazuwar cutar korona da kasar da dauka.
Yanzu haka dai Sierra Leone 104 sannan mutum hudu sun mutu..