Karshen rahotannin
Masu bibiyarmu karshen rahotannin kenan a wannan shafi.
Umar Mikail ne yake muku sallam tare da fatan za ku kasance da mu gobe idan Allah ya kai mu.
Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wannan shafi yana kawo muku bayanai kai tsaye dangane da annobar korona da ke ci gaba da yi wa duniya fyadar 'ya'yan kadanya.
Usman Minjibir and Umar Mikail
Masu bibiyarmu karshen rahotannin kenan a wannan shafi.
Umar Mikail ne yake muku sallam tare da fatan za ku kasance da mu gobe idan Allah ya kai mu.
Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya yi ganawa ta musamman da shugabannin 'yan kasuwa a jihar da zummar daukar matakan hana tashin farashin kayayyaki.
Gwamna Ganduje ya ce ya dauki matakin ne saboda kasancewar da ma al'adace ta 'yan kasuwa idan azumi Ramadana ya zo su tashi farashin kayayyaki, "amma kasancewar ana cikin annoba ba za mu lamunci hakan ba".
A ranar Talata ne Shugaba Buhari ya saka dokar hana fita a Jihar Kano ta tsawon mako biyu bayan wadda Ganduje ya saka ta mako daya ta kare a ranar Alhamis da zummar dakile yaduwar annobar korona.
"Na tabbatar wa da 'yan kasuwar cewa zan kai korafinsu ga Aliko Dangote da Abdussamad Isiyaka Rabi'u kan farashin sikari," in ji Ganduje, a wani sakon Twitter.
"Yayin da annobar ke ci gaba da ratsawa, yana da matukar mahimmanci mu hada kai domin tsira tare."
Ya zuwa karfe 12:05 na daren 30 ga watan Afrilu, Kano ta tabbatar da mutum 139 da suka harbu da cutar korona tare da mutuwar mutum biyar.
Hukumar dakile yaduwar cutuka a Afirka (Africa CDC) ta zayyana wasu gwaje-gwajen magani da kuma rigakafin annobar korona da ake yi a wasu kasashen nahiyar.
Kasashe 52 na nahiyar ne suka bayar da rahoton bullar cutar, inda fiye da mutum 37,000 ke jinya.
Africa CDC ta ce in aka kwatanta da sauran sassan duniya, babu gwaje-wajen da yawa a nahiyar sai dai:
A Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya wato Central African Republic, rahotanni sun bayyana cewa an kashe akalla mutum 37 sakamakon wani hari da aka kai a garin Ndele da ke arewacin kasar.
Tawaga uku ta 'yan tawaye ce ta far wa babbar kasuwar garin, inda daga baya suka hari sauran sassa tare da kafa sansani a wata cocin Katolika.
Dakarun tabbatar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya da kuma na wata kungiya da ta taba yin iko da garin sun gaza dakatar da maharan.
Kungiyoyi da dama ne suke ayyukansu a kasar tun bayan tumbuke Shugaba Francois Bozize shekara bakwai da ta gabata.
Rundunar 'ƴan sanda a Jihar Legas ta kama mutum 65 tare da manajan wani otel bisa zargin karya dokar hana fita a birnin.
Ana zarginsu da sharholiya a otel ɗin da sunan halartar zagayowar ranar haihuwar abokinsu.
Gwamnatin tarayya ta sa dokar hana taruka ne a jihohin Legas da Ogun da kuma Abuja, babban birnin ƙasar a yunƙurin karya lagon cutar korona a yankunan.
Ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, Jihar Legas ta tabbatar da samun mutum 947 da suka harbu da cutar korona - 20 sun mutu sannan 187 sun warke.
Hukumomin leken asirin Amuka sun ce sun gano cewa ba dan Adam ne ya kirkiri cutar korona ba sannan kuma ba sauya kwayar halitta aka yi ba, a wani bayanin farko da suka fitar.
Sun ce har yanzu suna ci gaba da bincike kan ko cutar na da alaka da yin hulda da dabbobi ko kuma wani abu da ya faru a wani dakin gwaji na kasar China.
Sai dai sun yi watsi da labarin kanzon kuregen da ake yadawa cewa China ce ta kirkiri cutar sannan ta yada wa duniya.
Shugaba Donald Trump ya sha yin yakin cacar baki da China game da asalin annobar da ta lakume ran fiye da mutum dubu 200 a duniya.
Wata kungiyar farar hula ta duniya ta yi gargadin cewa annobar korona ka iya janyo karuwar bautar da kananan yara a kasashen Ghana da Ivory Coast.
Kungiyar Fairtrade Africa da ke taimaka wa masu kananan sana'o'i ta ce ta samu rahoton kananan yaran da ke aiki a gonakin cocoa a Ivory Coast, amma wannan abu ne mai wahalar tabbatarwa saboda dokar ta hana fita.
Rufe makarantun da aka yi ya sanya yara da dama na fuskantar aikin da ya fi karfinsu a gonaki.
Takaita zirga-zirga zai jawo bibiyar yadda ake bautar da yara a kauyuka yayin girbe cocoa zai zama abu mai matukar wuya.
Sama da yara miliyan biyu ne ake hasashen suna aiki a masanan'antun sarrafa cocoa - wadanda ke samar da cocoa ga manyan masana'antun duniya.
Kamar yadda labari ya gabata, Firaministan Rasha, Mikhail Mishustinya ya kamu da cutar korona.
Babu dadewa kuma sai ga shi gidan talabijin na kasar ya nuna shi yana yi wa Shugaba Vladimir Putin bayani game da gwajin cutar.
"Mai girma Mista Putin, yanzun nan ta bayyana cewa gwajin da aka yi mani na korona ya nuna na kamu da cutar," a cewar Mista Mishustin.
Sai kuma ya bayyana wa shugaban cewa yanzu zai killace kansa. Mista Putin ya yi masa fatan samun sauki cikin gaggawa.
"Abin da ya faru da kai zai iya faruwa da kowa, kuma na sha fada," in ji Putin.
"Kai mutum ne mai kokari. Ina gode maka bisa ayyukan da muka yi zuwa yanzu."ar."
Gwamnatin Jihar Legas ta ce wani matashin dan shekara 25 ya mutu sakamakon cutar korona, abin da ya kawo jumillar adadin wadanda suka mutu a jihar zuwa 20.
Ma'aikatar lafiya a jihar ta ce matashin ya rasu ne bayan an kai shi asibiti cikin halin rai kwakwai-mutu-kwakwai, a cikin wata sanarawa da ta wallafa a shafinta na Twitter.
A wani sakon daban, ma'aikatar lafiyar ta ce adadin wadanda suka kamu da cutar a Legas sun zama 947 jumilla bayan an samu karuwar mutum 87 da suka harbu a cikin awa 24 da ta gabata.
Sai dai wasu mutum 49 sun warke daga cutar kuma an sallame su.
Ya zuwa ranar 29 ga watan Afrilu, mutum 187 aka sallama sannan 20 suka mutu, sai kuma 722 da ke dauke da cutar a yanzu.
Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kongo ta tabbatar da samun mutum na farko da ya kamu da cutar korona a gidan yari.
Akalla mutum hudu ne suka kamu da cutar sannan aka killace wasu da dama a gidan yarin Ndolo da ke babban birnin kasar Kinshasa.
Gidan yarin mai cunkoso na dauke da fursunoni ninki hudu na adadin abin da ya kamata ya dauka.
An bayyana Paris St Germain a matsayin wadda ta lashe gasar Faransa ta 2019-20, bayan da gwamnatin kasar ke tsoron yada cutar korona.
Gwamnatin Faransa ce ta ce ba za a koma wasanni ba cikin sauri har sai watan Satumba don gudun yada annobar, dalilin da ya sa ta soke wasannin shekarar nan.
PSG ce kan gaba a teburi da tazarar maki 12 da kwantan wasa, a lokacin da aka dakatar da gasar ranar 13 ga watan Maris don gudun yada cutar korona.
A farkon makon nan Firai Ministan Faransa, Edouard Philippe ya sanar da soke kakar wasanni ta 2019-20.
Shugabar Babban Bankin Turai ta yi gargadin cewa tattalin arzikin nahiyar na raguwa cikin sauri da ba a taba tunani ba saboda annobar korona.
Christine Lagarde ta shaida wa manema labarai cewa, tattalin arzikin zai iya kara raguwa sosai da kamar kaso 12 cikin 100 a wannan shekara.
Alkaluman farko sun nuna tattalin arzikin Turan ya fadi da kashi uku cikin 100 a watanni ukun farko na 2020 - yayin da matakan kulle suka fara aiki a baya-bayan nan.
Jami'ai a Jamus - wadda ta fuskanci karuwar marasa aikin yi a watan Afrilu - na gargadi cewa za a iya fuskantar koma bayan tattalin arziki mai muni, wanda ba a taba fuskanta ba tun bayan yakin duniya na biyu.
Kungiyar Kwadago a Najeriya NLC ta ce ba za ta lamunci duk wani yunkuri na rage wani kaso daga cikin albashin 'ya'yanta ba, ba tare da tattaunawa da kungiyar ko kuma yardarta ba.
Shugaban NLC na kasar, Kwamared Ayuba Wabba ya ce duk da cewa sun fahimci halin da tattalin arzikin duniya ya fada, to amma dole abi ka'idoji wajen daukar duk wani mataki da zai kai ga taba albashin ma'aikata.
Wannan na zuwa ne a dai-dai lokacin da wasu kamfanoni na kasashen duniya suka fara rage wani kaso daga cikin albashin ma'aikatansu.
A ranar Juma'a ne dai ma'aikata a fadin duniya ke bikin tuna ranar ma'aikata ta duniya da ake yi duk ranar 1 ga watan Mayu.
Gwamnati a Lebanon, ta amince da wani shirin ceto tattalin arziki, yayin da masu zanga-zanga suka sake bayyana a titunan kasar a wannan mako duk da annobar korona.
A kwanaki ukun da suka gabata fushin jama'a ya rikide ya koma tashin hankali a birnin Tripoli, bayan da jama'a suka yi ta kai wa bankuna farmaki, saboda bisa zargin kara angiza matsalar tattalin arziki da rike musu kudadensu.
Wasu ƴan kasar da dama da ke da ra'ayin yin garambawul a tsarin siyasa da harkokin kudi, na cewa dokar kullen da aka kafa don yaki da korona, ta sake dagula al'amura matuka gaya.
Kungiyar bayar da agaji ta Red Cross, ta ce tana fargabar cewa adadin wadanda suka kamu da cutar korona a Somalia ya zarta wanda hukumomi suka bayar.
Babban mai sanya ido na hukumar kan harkokin lafiya a kasar ya ce za a samu mutane da yawa da za a gano suna dauke da cutar a 'yan makwanni masu zuwa.
An dai ce fannin lafiyar kasar ya gamu da koma baya, saboda shekaru 30 da aka kwashe ana fama da tashe-tashen hankula. Yawancin asibitoci babu wutar lantarki da kayan aiki.
Galibin jama'a a kasar ba sa aiwatar da matakan kariya don kaucewa kamuwa da korona, saboda rayuwa da suke yi a yankuna masu cunkoson jama'a.
Kasar Faransa ta gamu da faduwar tattalin arziki mafi muni da ba ta taba samu ba tun bayan yakin duniya na biyu.
A watannin farkon wannan shekara karfin tattalin arzikin cikin gida ya yi kasa da kashi biyar da digo takwas, abin da ba a taba gani ba tun lokacin da aka yi irin wannan bincike a 1949.
Hukumar kididdiga ta kasar Faransa, ta ce babban makasudin hakan shi ne kafa dokar kulle da gwamnatin kasar ta yi tun watan Maris.
Wakilin BBC ya ce tattalin arzikin Spaniya ma ya yi kasa da fiye da kashi biyar, ko da yake na Italiya bai kai haka ba.
Kasa da awanni 24 da suka gabata ne ita ma Amurka ta fitar da wasu bayanai da ke nuna faduwar tattalin arzikinta, a watanni uku na farkon wannan shekara ta 2020.
Tattalin arzikin kasashen Tarayyar Turai ya yi kasa da kashi uku da rabi a watanni uku na farkon wannan shekarar, a cewar wasu alkalumman farko-farko da hukumomi suka fitar.
Wannan dai shi ne koma baya mafi girma tun bayan matsalar faduwar darajar kudi da aka samu a 2009.
Karfin tattali arzikin cikn gida ne ya fi faduwa kasa wanwar a kasashen 19 na Turai da ke amfani da nau’in kudi na Euro.
Shugabar Babban Bankin Turai Christine Lagarde, ta ce dole ne kasashen nahiyar su yi aiki tare don warware wannan matsala.
Ta ce an rufe dukkanin bangarorin tattalin arziki, don haka za a ci gaba da ganin abin da hakan zai haifar, yanzu aka soma ganin wadannan alkalumma masu tsauri.
Jamus ta sami karuwar masu rasa aiyukansu a watan Afrilu, adadin da ya karu da mutum dubu300 daga watan Maris zuwa yanzu, duk da tsarin da aka yi don kare ayyuka a lokacin kullen.
Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya bai wa wani marigayi mukami a gwamnati.
Buhari ya nada marigayi Tobias Chukwuemeka Okwuru a matsayin mamban kwamitin wata ma'aikata watanni biyu bayan mutumin ya rasu.
Sunan Mr Okwuru na kunshe a wata takarda da Shugaba Buhari ya aike wa Majalisar Dattawan kasar ranar Talata ta neman amincewarsu da jerin mutum 37 da ya bai wa mukaman, a watan Fabrairu.
Mai taimaka wa Shugaba Buhari kan yada labarai, Lauretta Onochie, ta ce Mista Okwuru yana raye lokacin da shugaba Buhari ya nada shi "har ya zo ya gyara takardarsa ta neman daukar aiki".
"Mutumin ya rasu ne a dai-dai lokacin da yake jiran sanatoci su tantance shi kuma ba a sanar da gwamnatin tarayya ba."
Wannan dai ba shi ne karon farko da gwamnatin Shugaba Buhari take yin irin wannan nade-naden matattu mukamai ba. Ko a 2017 sai da shugaban ya nada mutum biyar da suka dade da mutuwa a matsayin mambobin kwmaitocin ma'aikatun gwamnati.
Sama da mutum dubu ne suka mutu a Rasha yayin da wasu dubu 100 suka kamu tun bayan barkewar cutar korona a kasar.
Sabuwar kididdigar ta biyo bayan yawaitar karuwar masu kamuwa da cutar - sama da dubu 700.
A farkon makon nan ne, Shugaba Putin ya sanar da tsawaita dokar hana fita a kasar zuwa 12 ga watan Mayu mai zuwa.
'Yan sandan Rasha sun ce za su ci gaba da tsaurara matakan da aka dauka na yaki da cutar a fadik kasar.
Ana dai ci gaba da nuna damuwa game da mummunan tasirin dokar hana zirga-zirga kan tattalin arziki a kasar.
Gwamnatin Sri Lanka ta kakaba dokar hana fita a fadin kasar bayan samun sabbin mutum biyu da suka kamu da cutar korona, cikin rundunar jami'an tsaronta.
Dokar kullen da za ta fara aiki daga karfe 8 na yamma na kasar za ta kare ranar 4 ga watan Mayu mai kamawa.
Sama da soji 225 wadanda mafi yawansu na ruwa ne, da ke zaune a wajen Colombo babban birnin kasar an same su dauke da cutar a makon jiya, bayan yin gwaji.
Sojin ruwan na bibiyar mutanen da ake zaton sun kamu da cutar wadanda suka ki killace kansu.
Ya zuwa yanzu dai, sama da mutum 650 ne aka tabbatar suna dauke da cutar a kasar kuma tuni mutum bakwai suka mutu.