Wannan shafi na kawo muku bayanai kai tsaye dangane da annobar korona da ke ci gaba da yaduwa a fadin duniya, inda mutum fiye da milyan biyu da dubu dari shida suka kamu sannan fiye da 206,000 suka mutu.
Rahoto kai-tsaye
Awwal Ahmad Janyau and Umar Mikail
Buhari ya ce za a yi binciken mace-macen Kano
Asalin hoton, AFP
Bayanan hoto, Masu ginar kabari a Kano sun ce sun binne mutane da dama a jihar
Shugaban Najeriya
ya bayyana damuwa kan mace-macen da aka samu a jihar Kano da ke arewacin kasar.
Shugaban ya ce ya
aika da tawaga domin gudanar da bincike tare da kulle jihar na tsawon mako
biyu.
Kalaman
shugaban na zuwa bayan yawan mace-macen da ake samu a kano fiye da kowane
lokaci a baya.
Al’ummar jihar
na cikin hali na rashin
tabbas kan abin da ya haifar da mace-macen yayin da ake cikin wannan yanayi na
annobar korona.
Wasu na tunanin cutar korona ce ta shiga al’umma kuma ta
ke yi wa jihar illa.
A cikin mako guda fitattun mutane da masu shekaru sun kwanta
dama a kusan dukkanin unguwannin jihar.
Amma hukumomi
a jihar sun ce mace-macen da aka samu bay a da alaka da cutar korona. Sun ce
cutuka kamar hawan jini da ciwon suga da sankarau da zazzabin maleriya na iya
haifar mace-macen.
Kano ita ce ta uku cikin jerin jihohin Najeriya da ke fama da cutar korona.
MDD ta yi gargadi kan yadda jami'an tsaro ke wuce gona da iri
Asalin hoton, Getty Images
Majalisar Dinkin
Duniya ta yi gargadi ga kasashe kan gujewa amfani da karfi a wannan yanayi da
ake ciki na annobar cutar korona.
Ofishin kare hakkin
bil’adama na Majalisar Dinkin Duniya ya ce ya kamata gwamnatoci “su fahimci cewa
cutar ce barazana, ba mutane ba.”
Afirka ta kudu da
Kenya da Uganda da Rwanda suna cikin kasashen da jami’an tsaro ke amfani da
tsauraran matakai domin tabbatar da dokar hana wa mutane fita.
Kwamishinar hukumar
kare hakkin bil’adama ta Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci kasashe su kaucewa
yin amfani da karfi a matsayin makami a matsayi kafa iko kan jama’a.
Ta ce harbi da tsarewa
ko zagin mutane don sun karya dokar hana fita saboda sun fita neman na abinci, matakai
ne da suka saba doka da ba za a lamunce ba.
Majalisar
Dinkin Duniya ta ce sama da mutum 17,000 aka kama a Afirka ta kudu saboda sun
saba dokar hana fita.
A
Kenya, kungiyoyin kare hakkin bil’adama 27 ne suka rubutawa gwamnati wasika
suna neman ta dakatar da hukunta wadanda suka saba dokar hana fita.
Zuwa
yanzu mutum 32,100 aka bayyana cewa cutar korona ta kama a kasashen Afirka 52,
inda mutum 1,428 suka mutu yayin da kuma 9,741 suka warke.
Ko kun san Buhari ya tilasta wa kowa saka takunkumin fuska?
Yayin jawabinsa karo na uku ga 'yan Najeriya bayan kafa dokar hana fita a jihohin Legas da Ogun da kuma Abuja domin dakile yaduwar cutar korona, Shugaba Muhammadu Buhari ya ce gwamnatinsa za ta tabbatar da amfani da takunkumi ko abin rufe fuska a bainar jama'a da kuma ci gaba da ba da tazara da tsaftar jiki.
Shugaban ya kuma bukaci gwamnatocin jihohi da kamfanoni da masu zuciyar taimakawa jama'a su tallafa wajen samar da abin rufe fuska ga al'ummar kasa.
Tuni gwamnatin Legas, jihar da masu dauke da cutar suka fi yawa a Najeriya ta tilasta wa mutanen jihar amfani da abin rufe fuska musamman a cikin taron jama'a.
Asalin hoton, @BashirAhmaad
Jami'ar Oxford ta yi nisa da aikin samar da rigakafin cutar korona
Shin ko za a iya samun miliyoyin allurai na rigakafin cutar korona zuwa watan Satumba?
Dala alama dai nesa ta zo kusa sabanin yadda muke diga ayar tambaya, amma cibiyar Jenner ta Jami'ar Oxford ta ce ta samar da ingantaccen rigakafin cutar korona, kuma ta shirya gudanar da gwajinsa ga mutane 6,000 kafin karshen watan Mayu.
An gudanar da gwajin rigakafin ga birai guda shida a wata cibiyar lafiya ta Amurka, kamar yadda New York Times ta ruwaito.
Rahoton ya ce bayan saka wa biran kwayar cutar, kuma yanzu suna cikin koshin lafiya bayan kwanaki 28. Kuma sauran ba a ba rigakafin ba su da lafiya.
Yadda aka gina katanga a Indiya don dakile cutar corona
Asalin hoton, Getty Images
Wata gunduma da ke cikin yankin jihar Tamil Nadu a kudancin Indiya ta gina katanga domin killace iyakokinta tsakaninta da jihohin da ta ke makwabtaka da ita a matsayin matakai na dakile yaduwa cutar korona.
An gina katangar mai tsawon kafa 5 a dukkanin kofofin shiga yankin guda biyu a ranar Lahadi domin hana zirga-zirgar ababen hawa tsakanin yankin Tamil Nadu da kuma Andhra Pradesh.
Jami'ai a yankin sun ce an dauki matakin ne domin tantance 'yan ci-rani da ke shiga jihar yin kwadago ba tare da izini ba.
Mahukunta a jihar sun ce matakin na wuccin gadi ne domin sa ido ga zirga-zirgar mutane tsakanin jihohin biyu.
Sakacin China ya haifar da bazuwar cutar korona - Trump
Shugaba Donald Trump ya ce China na iya hana kwayar cutar korona bazuwa zuwa sauran sassan duniya, inda ya ce za a gudanar da muhimmin bincike don gano matakan da gwamnatin kasar ta dauka.
Ya ce kamata ya yi China ta hana annobar bazuwa daga tushenta.
Mista Trump ya fadi haka ne a yayin da yake jawabi a wani taron manema labarai na farko tun bayan sakon Twitter da ya fitar a karshen mako yana cewa ba shi da lokaci da kuzarin kula su.
Shugaban Amurkan ya kuma ce bai ga dalilin karuwar kiraye-kirayen layukan wayar Amurka na neman agaji game da sinadaran wanke datti ba.
Trump ya sha suka bayan ya nuna cewa ana iya yin allurar sinadaran wanke dattin a matsayin maganin kashe cutar korona.
Asalin hoton, Getty Images
Kwana uku a jere babu bayanan korona a Kano
An shafe kwana uku babu bayanan cutar
korona daga jihar Kano daga alkalumman da Hukumar dakile cutuka masu yaduwa a Najeriya
ke fitarwa a kullum.
Tun da cutar korona ta fara bulla a Kano a ranar 11 ga Afrilu,
yawan masu dauke da cutar ke karuwa, inda jihar ta kasance ta uku cikin jerin jihohin
da cutar ta fi bazuwa a Najeriya.
Kusan kwana uku da NCDC ke fitar da alkalumma babu
bayanai game da Kano kan cutar korona.
Ko da yake Hukumomi a jihar Kano sun
sanar da karin mutum biyu da cutar korona ta kashe a jihar ranar Litinin
Yanzu mutum uku cutar korona ta kashe a jihar, kamar
yadda ma'aikatar lafiya a jihar ta sanar a shafinta na Twitter a ranar Litinin.
Sai dai alkalumman yawan wadanda suka kamu da cutar
korona ba su sauya ba daga mutum 77 da hukumar yaki da cutuka masu yaduwa a
kasar ta sanar ranar Lahadi.
Yawan mace-macen da ake gani a jihar a
‘yan kwanakin nan sun tayar da hankalin jihar da ma Najeriya baki daya.
A cikin mako guda
fitattun mutane da masu shekaru na kwanta dama a kusan dukkanin unguwannin
jihar, inda ake fargabar cewa cutar korona ce ke ci gaba da bazuwa a jihar.
Cikin wadanda aka
rasa daga Asabar zuwa Lahadi akwai farfesoshi guda hudu wanda na baya-bayannan
shi ne Farfesa Balarabe Maikaba, na tsangayar nazarin aikin jarida a jami'ar
Bayero da ke Kano.
Sai dai, cibiyar
gwaji guda daya da ake da ita a jihar ta rufe, kuma rahotanni sun bayyana cewa
ana fuskantar matsaloli wajen tura samfur zuwa Abuja daga Kano.
A wata hira da BBC
Gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje ya ce babban abin da aka dogara da shi a
kokarin dakile korona a jihar shi ne gwaji, wanda ya ce an shafe kwanaki biyar
zuwa shida wadanda aka dauki samufurinsu ba su san matsayinsu ba.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.
Karshen labarin da aka sa a X
Jawabin Buhari a takaice
Asalin hoton, Bashir Ahmad
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gabatar da jawabi karo na uku ga 'yan Najeriya kan halin da kasar take ciki da kuma matakan da gwamnatinsa ke dauka kan annobar cutar korona.
Ga jawabin shugaban a takaice kan matakan da ya dauka.
Legas da Abuja da Ogun za su ci gaba da kasancewa cikin kulle na tsawon mako daya
Za a sassauta dokar hana fita daga ranar 4 ga Mayu
Za a bude harakokin kasuwanci daga 8 na safe zuwa 6 na yamma daga ranar 4 ga Mayu
Dokar hana fitar dare za ta fara aiki 8 na dare zuwa 6 na safe daga ranar 4 ga Mayu
Dokar hana taron jama'a da tarukan addini za ta ci gaba
An hana tafiye-tafiye daga jiha zuwa jiha
An kafa dokar hana fita ta tsawon mako biyu a Kano
Coronavirus: Mutum 11 sun kara kamuwa a Borno
Sabbin alkalumman Hukumar dakile cutuka masu yaduwa a Najeriya sun ce an kara samun mutum 11 da suka kamu da cutar korona a jihar Borno mai fama da rikicin Boko Haram.
Yanzu adadin mutum 41 suka kamu da cutar a jihar da ke yankin arewa maso gabas.
Gwamnatin Borno ta fito ta nemi afuwar mutanen da ta ce sun tsere bayan gwaji ya tabbatar da suna dauke da cutar korona.
Borno na daya daga cikin jihohin da ake bayyana fargabar barkewar cutar korona, musamman rikicin Boko Haram da ta yi fama da shi na tsawon shekaru wanda ya raba sama da mutum miliyan biyu da gidajensu.
Budewa
Barkanmu da safiyar Talata 28 ga watan Afrilu.Kuma muna maku barka da azumi da fatan kuna cikin koshin lafiya.
Awwal Janyau ne ke muku maraba a wannan shafinnmu da muke kawo labarai da rahotanni kai-tsaye kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya