Dan gidan tsohon mataimakin shugaban Najeriya Mohammed Atiku Abubakar, ya warke daga cutar korona.
A wata zantawa da ya yi da jaridar PREMIUM TIMES ta kasar a ranar Litinin, Muhammad ya ce " yanzu aka yi mani gwaji na biyu a jere kuma yana nuna ba na dauke da cutar".
Ya kara da cewa "An fara shirye-shiryen sallama ta, ina fatan haduwa da iyalina a maraicen yau."
Muhammad shi ne mutum na farko da aka ba da rahoton yana dauke da cutar a Abuja a ranar 19 ga watan Maris din da ya gabata, wato kwana 40 kenan a cibiyar da ake killace masu dauke da cutar korona da ke Abuja.
Masana sun ce Muhammad mai shekaar 31 na daya daga cikin mutanen da suka dade ba su warke ba, tun bayan samun bullar cutar da aka yi a kasar ranar 27 ga watan Fabirariru a jihar Legas.
Hukumar dake yaki da cutuka masu yaduwa a Najeriya NCDC ta ruwaito cewa akwai sama da mutum 1,000 dake dauke da cutar, yayin da tuni ta hallaka mutum 40, 239 kuma suka warke.