Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Buhari ya saka dokar hana fita ta mako biyu a Kano
Wannan shafi na kawo muku bayanai kai tsaye dangane da annobar korona da ke ci gaba da yaduwa a fadin duniya, inda mutum fiye da milyan biyu da dubu dari shida suka kamu sannan fiye da 206,000 suka mutu.
Rahoto kai-tsaye
Awwal Ahmad Janyau, Buhari Muhammad Fagge and Umar Mikail
Gwamnatin Legas ta fara raba abin rufe hanci
Gwamnatin Legas a Najeriya ta ce ta fara raba wa mutanen jihar abin rufe baki da hanci yayin da cutar korona ke ci gaba da yaduwa a jihar.
A ranar Lahadi ne gwamnatin Legas ta sanar da tilasta amfani da abin rufe fuska ga al’ummar jihar. Kuma ta ce za a hukunta duk wanda ya bijerewa umurnin musamman a taron jama’a.
Cutar korona ta fi yaduwa a Legas da ke kudancin Najeriya, inda zuwa yanzu mutum 731 ke dauke da cutar a jihar, kusan fiye da rabin yawan wadanda suka kamu a Najeriya.
An bude makarantu a China
Rayuwar yau da kullum ta dawo a China, kasar da aka fara samun barkewar cutar korona da yanzu ta mamaye duniya
An fara bude makarantu a manyan biranen China bayan shafe lokaci suna rufe saboda annobar cutar korona.
Dalibai sun koma makarantu a biranen Beijing, Shanghai da Guangzhou ko da yake ba dukkaninsu ba ne amma daliban da za su rubuta jarabawar shiga jami’a aka amince su dawo karatu.
Sai dai makarantu a Wuhan inda cutar korona ta barke za su ci gaba da kasancewa a rufe.
An gano mai dauke da cutar korona da ya tsere a Borno
Gwamnatin Borno ta ce ta gano mutum daya daga cikin masu dauke da cutar korona da suka tsere.
Kwamishinan lafiya na jihar Dr. Salisu Kwayabura ya ce an gano matashin ne mai shekara 24 da misalin karfe 2 na dare a birnin Maiduguri.
A ranar Lahadi ne hukumomin lafiya a Borno suka sanar da cewa suna farautar wasu masu dauke da cutar korona guda biyu mace da namiji da suka tsere.
Sanarwar da kakakin gwamnatin jihar Borno Isa Gusau ya fitar a ranar Litinin, ta ce bayan baza tawagar jami’ar lafiya da ‘yan sanda, “an samu marar lafiyan cikin mawuyacin hali kuma nan take aka dauke shi cikin abin daukar marar lafiya zuwa cibiyar da ake killace masu cutar korona.
Sai dai kuma daya matar da ta tsere mai shekara 42 bayan gwaji ya tabbatar da tana dauke da cutar korona har yanzu ba a gano ta ba.
Mutum 30 hukumar yaki da cututtuka masu yaduwa ta Najeriya ta tabbatar da suna dauke da cutar korona a jihar Borno.
Yadda aka hukunta limamai da fasto-fasto a Abuja
Hukumomi a Abuja babban birnin tarayyar Najeriya sun hukunta wasu limaman masallatai da fasto-fasto da suka saba dokar hana taron jama’a.
An kama limaman ne guda uku da aka samu suna jagorantar Sallar jam’i a masallatai da kuma fasto guda biyu da aka samu sun tara jama’a a coci, kamar yadda hukumomin Babban Birnin Tarayya Abuja suka sanar a Twitter.
Sanarwar da aka wallafa tare da bidiyo, ta ce dukkaninsu an zartar masu da hukuncin daurin wata daya a gidan yari kan saba dokar hana fita da aka kafa domin dakile yaduwar cutar korona.
Hoton bidiyon ya nuna yadda limaman ke jagorantar Sallar jam'i ba tare da mabiyan sun bayar da tazara ba.
Shin me ya sa ba a samu bayanan korona a Kano ba?
Sabbin alkalumman da Hukumar dakile cutuka masu yaduwa a Najeriya ta fitar daren Lahadi kan cutar korona sun zo wa mutane da mamaki, inda aka ga babu bayanai game da Kano.
Tun da cutar korona ta fara bulla a Kano a ranar 11 ga Afrilu, yawan masu dauke da cutar ke karuwa, inda jihar ta kasance ta uku cikin jihohin da cutar ta fi bazuwa a Najeriya.
Kusan kwana biyu da NCDC ke fitar da alkalumma babu bayanai game da Kano kan cutar korona.
Yawan mace-macen da ake gani a jihar a ‘yan kwanakin nan sun tayar da hankalin jihar da ma Najeriya baki daya.
A cikin mako guda fitattun mutane da masu shekaru na kwanta dama a kusan dukkanin unguwannin jihar, inda ake fargabar cewa cutar korona ce ke ci gaba da bazuwa a jihar.
Cikin wadanda aka rasa daga Asabar zuwa Lahadi akwai farfesoshi guda hudu wanda na baya-bayannan shi ne Farfesa Balarabe Maikaba, na tsangayar nazarin aikin jarida a jami'ar Bayero da ke Kano.
Sai dai, cibiyar gwaji guda daya da ake da ita a jihar ta rufe, kuma rahotanni sun bayyana cewa ana fuskantar matsaloli wajen tura samfur zuwa Abuja daga Kano.
A wata hira da BBC Gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje ya ce babban abin da aka dogara da shi a kokarin dakile Korona a jihar shi ne gwaji, wanda ya ce an shafe kwanaki biyar zuwa shida wadanda aka dauki samufurinsu ba su san matsayinsu ba.
"Kayan da ma ake daukan (samfurin) a kai Abuja sun yi karanci, kuma ba kaya ne wanda gwamnati za ta je kasuwa ta saya ba," a cewar Ganduje.
Ya kara da cewa "Wadanda aka dau samfurinsu ba su san matsayinsu ba. Za su ci gaba da hulda da mutane."
Ba zan yi kasadar dage dokar hana fita ba - Boris Johnson
Firaministan Birtaniya Boris Johnson a jawabinsa na farko ga jama'ar kasa tun bayan murmurewarsa daga cutar korona ya yi gargadin cewa har yanzu kasar na mataki "mafi hatsarin cutar korona."
Mista Johnson ya ce ba zai yi watsi da sadaukar da kai da mutanen Birtaniya suka yi ba, ta hanyar sassauta dokar hana fita.
"Na san abu ne mai wahala. Ina son bunkasa tattalin arziki cikin sauri kamar yadda zan iya,"
"Amma ba zan yi watsi da sadaukarwar da mutanen Birtaniya suka yi ba," in ji shi.
Ya kuma ce yanzu ba za su iya tantance lokacin tabbatar da sauyin ba.
Cutar korona ta bulla a jihohin Kebbi da Ebonyi da Bayelsa da Taraba
Annobar cutar korona na ci gaba da yaduwa a sassan Najeriya, inda a ranar Lahadi karon farko hukumar da ke yaki da cututtuka masu yaduwa ta ce cutar ta bulla a jihohin Kebbi da Taraba da Ebonyi da Bayelsa.
A jihar Taraba mutum shida aka tabbatar da sun kamu da cutar, kuma karon farko da cutar ta bulla a jihar.
An samu mutum guda da ya kamu a jihohin Kebbi da Ebonyi da kuma Bayelsa.
Lokacin da yake sanar da bullar cutar a jiharsa, gwamnan Kebbi Abubakar Atiku Bagudu ya ce mutumin wanda ya kamu da cutar dan shekara 40 ne wanda ya yi balaguro zuwa Legas.
Gwamnan ya ce an killace shi bayan gwaji ya tabbatar da yana dauke da cutar.
Hakan na nufin a yanzu cikin jihohi 36 cutar ta yadu a jihohi 32 na Najeriya hadi da Abuja.
Sauran jihohin da har yanzu ba a samu bullar cutar ba sun hada da:
1. Cross River
2. Kogi
3. Nassarawa
4. Yobe
Cutar korona ta kashe mutum 40 a Najeriya
Hukumar dakile cutuka masu yaduwa ta ce an samu karin mutum 91 da cutar korona ta shafa cikin sa'a 24 da ta wuce a Najeriya.
Cutar ta kuma kara kashe mutum biyar, inda yawan wadanda suka mutu a kasar yanzu suka kai 40.
Yanzu yawan masu dauke da cutar a Najeriya sun kai 1,273, yayin da mutum 239 suka warke daga cutar
Tsohon shugaban hukumar kayyade farashin man fetur ta Najeriya, PPMC, Engineer Sulaiman Achimugu ne na farko da cutar ta kashe a Najeriya.
Marigayin ya rasu ne ranar Litinin 23 ga watan Maris.
Cutar korona ta kama kusan mutum miliyan uku a duniya
Zuwa yanzu yawan wadanda suka kamu da cutr korona a duniya sun kusan kai miliyan uku, kamar yadda alkalumman jami'ar Johns Hopkins da ke bin diddigin annobar korona a duniya suka nuna.
Alkalumman jami'ar sun kuma ce yawan wadanda cutar ta kashe sun kai sama da mutum 206,000.
A yanzu mutum 2,971,831 suka kamu da korona yayin da cutar ta kashe mutum 206,542 a duniya.
Ana tunanin adadin ya zarce haka saboda rashin bayar da rahotanni da kuma karancin gwaje gwaje.
Cutar ta fi yduwa da kisa a Amurka inda mutum 965,910 suka kamu, sai kuma Spain da 226,629 suka kamu da cutar.
Har yanzu kasashe na ci gaba da bincike domin samo maganin rigakafin cutar da ke ci gaba da yaduwa a sassan duniya.
Barka
Barkanmu da safiyar Litinin 26 ga watan Afrilu.Kuma muna maku barka da azumi da fatan kuna cikin koshin lafiya.
Awwal Janyau ne ke muku maraba a wannan shafinnmu da muke kawo labarai da rahotanni kai-tsaye kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya
Da fatan za ku kasance tare da mu har zuwa dare.