Buhari ya saka dokar hana fita ta mako biyu a Kano

Wannan shafi na kawo muku bayanai kai tsaye dangane da annobar korona da ke ci gaba da yaduwa a fadin duniya, inda mutum fiye da milyan biyu da dubu dari shida suka kamu sannan fiye da 206,000 suka mutu.

Rahoto kai-tsaye

Awwal Ahmad Janyau, Buhari Muhammad Fagge and Umar Mikail

  1. Rahotanni a wannan shafi sun zo karshe

    Jama'a nan muka kawo karshen rahotannin namu na kai-tsaye.

    Mu hadu da ku gobe idan Allah ya kai mu, amma kafin nan za ku iya yin kasa domin karanta abubuwan da suka faru a yau din.

    Umar Mikail ke cewa mu kwana lafiya.

  2. Biloniyan China ya sake bai wa Afirka tallafin kayan yaki da korona

    kayan tallafi daga China

    Asalin hoton, Africa CDC

    Bayanan hoto, Wannan ne karo na uku da Jack Ma ke bai wa Afirka tallafin kayan yaki da annobar korona

    Hukumar yaki da cutuka masu yaduwa ta Afirka (Africa CDC) ta bayyana cewa ta karbi tallafin kayan gwajin cutar korona daga biloniyan dan kasuwar nan na China mai suna Jack Ma.

    A wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na intanet, hukumar ta ce wannan ne karo na uku da dan kasuwar yake bai wa kasashen Afirka tallafin, sannan ta ce kasashe mambobin kungiyar hadin kan Afirka ta AU ne za su amfana da su.

    Daga cikin kayayyakin da aka kawo akwai takunkumin rufe fuska miliyan 4.6, abin tsane ruwa da akwatun kayan gwaji dubu 500, na'urar taimaka wa numfashi 300, kayan kare kai dubu 200, abin kare fuska 2,000.

    Da misalin karfe 3:00 na ranar Litinin ne jirgin Ethiopian Airlines ya sauka dauke da kayan a filin jirgin saman Addis Ababa na Habasha daga birnin Guangzhou na China , a cewar hukumar.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  3. Buhari ya saka dokar hana fita ta mako biyu a Kano

    Muhammadu Buhari

    Asalin hoton, Nigeria Presidency

    Shugaba Buhari ya saka dokar hana fita ta tsawon mako biyu a Jihar Kano.

    Buhari ya ce: "Game da Kano, na bayar da umarnin sanya dokar hana fita tsawon mako biyu da za ta fara aiki nan take. Gwamnatin Tarayya za ta bayar da dukkanin agajin da ake bukata na kayan aiki da kuma tallafi ga mutane domin taimaka wa jihar wurin yaki da annobar korona."

    Ganduje ya ce: "Halin da ake ciki yanzu, wato muna da babbar matsala, kuma zan iya cewa da kai wannan hali a yanzu haka dai gaskiya ba shi da kyau kuma abin tsoro ne."

    Ya zuwa karfe 12:15 na ranar Litinin, Jihar Kano ta tabbatar da samun mutum 77 da ke dauke da cutar da ake yi wa lakabi da Covid-19.

  4. Shugaba Buhari yana jawabi

    Ku garzaya shafinmu na Facebook domin kallon jawabin Shugaba Muhammadu Buhari game da cutar korona a Najeriya.

  5. Dan gidan Atiku ya warke bayan kwana 40 a killace

    Muhammed Abubakar

    Asalin hoton, Twitter/Muhammed

    Dan gidan tsohon mataimakin shugaban Najeriya Mohammed Atiku Abubakar, ya warke daga cutar korona.

    A wata zantawa da ya yi da jaridar PREMIUM TIMES ta kasar a ranar Litinin, Muhammad ya ce " yanzu aka yi mani gwaji na biyu a jere kuma yana nuna ba na dauke da cutar".

    Ya kara da cewa "An fara shirye-shiryen sallama ta, ina fatan haduwa da iyalina a maraicen yau."

    Muhammad shi ne mutum na farko da aka ba da rahoton yana dauke da cutar a Abuja a ranar 19 ga watan Maris din da ya gabata, wato kwana 40 kenan a cibiyar da ake killace masu dauke da cutar korona da ke Abuja.

    Masana sun ce Muhammad mai shekaar 31 na daya daga cikin mutanen da suka dade ba su warke ba, tun bayan samun bullar cutar da aka yi a kasar ranar 27 ga watan Fabirariru a jihar Legas.

    Hukumar dake yaki da cutuka masu yaduwa a Najeriya NCDC ta ruwaito cewa akwai sama da mutum 1,000 dake dauke da cutar, yayin da tuni ta hallaka mutum 40, 239 kuma suka warke.

  6. Almajirai biyar da aka kai Kaduna daga Kano na da cutar korona

    Wasu almajirai biyar da gwamnatin Jihar Kano ta mayar gida zuwa jiharsu ta Kaduna sun kamu da cutar korona, kamar yadda gwamnatin Kaduna ta bayyana a ranar Litinin.

    Da wannan adadi, jumillar wadanda ke dauke da cutar yanzu haka a Kaduna sun zama tara.

    A wata sanarwa gwamnati ta wallafa a shafinta na Twitter, Kwamishinar Lafiya ta Kaduna Dr Amina Mohammed Baloni ta ce tuni aka kai su asibitin kula da cutuka masu yaduwa da ake killace masu cutar.

    Jumillar mutum 15 ne dai suka harbu da korona a Jihar Kaduna ya zuwa yanzu, inda aka sallami shida daga cikinsu, ciki har da Gwamna Nasir El-Rufai.

    Kazalika sanawar ta ce yanzu akwai cibiyoyin gwajin cutar guda biyu a Kaduna, daya a birnin Kaduna da kuma daya a Zariya.

    Ranar Lahadi ne dai Gwamna El-Rufai ya tsawaita dokar hana fita a jihar da kwana 30, a yunkurin gwamnatinsa na yaki da yaduwar cutar.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  7. Burtaniya ta gaza cimma adadin gwajin korona da ta so yi

    Korona

    Asalin hoton, Getty Images

    A bayanin da gwamnatin Burtaniya ke yi kullum kan cutar korona, Sakataren Lafiya Matt Hancock ya bayyana a yau Litinin cewa gwajin cutar korona 37,024 aka iya yi a ranar Lahadi.

    Adadin ya yi kasa da abin da gwamnatin ta yi ikirarin yi na gwajin mutum 100,000 kullum nan da karshen watan Afrilu, yayin da saura kwana hudu watan ya kare.

    Amma a baya-bayan nan, gwamnatin ta rika yin gwajin cutar sau 20,000 a rana guda, inda wanda aka yi a Lahadin ya kusa ninka adadin da ake yi a bya.

    Yanzu kuma gwamnatin ta ce sama da manyan ma'aikata miliyan 10 da kuma iyalansu a Ingila na neman a yi musu gwajin.

  8. Fifa ta bayar da shawarar canja 'yan kwallo biyar a lokacin wasa

    Gabriel Jesus yana karbar Sagio Aguero

    Asalin hoton, Getty Images

    Kungiyoyi za su fara canja 'yan kwallo biyar a wasa amma na wucin gadi don kawo sauki wajen karkare kakar bana da zarar an ci gaba da wasanni kamar yadda Fifa ta bayar da shawara.

    Ana sa ran yin amfani da wannan shawarar na wucin gadi har zuwa karshen kakar 2021.

    Yadda ake son gudanar da tsarin

    • A gasar da aka amince a sauya 'yan kwallo uku, za su iya saka biyar jumulla a lokacin wasa.
    • Za a yi amfani da tsarin canja 'yan wasa biyar kamar yadda ake yi a lokacin da ake sa uku da kuma lokacin hutu.
    • Watakila da yiwuwar saka dan wasa na shida bayan karin lokaci.
    • Za a ci gaba da wannan tsarin ga karawa tsakanin tawagar kasa da kasa har zuwa 31 ga watan Disambar 2021.
  9. Labarai da dumi-dumi, Adadin masu dauke da korona a duniya ya zarce miliyan uku

    A yanzu akwai sama da mutum miliyan uku da ke dauke da cutar korona a fadin duniya, kamar yadda jami'ar Johns Hopkins da ke bibiyar kididdigar korona ta bayyana.

    Sama da mutum 208,000 ne suka mutu dalilin cutar.

  10. An samu ambaliyar ruwa da kuma zaftarewar kasa a Habasha

    Getty

    Asalin hoton, Getty Images

    Mutum hudu sun mutu yayin da daruruwan suka bata sakamakon ruwa kamar da bakin kwarya da ya janyo ambaliya da kuma zaftarewar kasa a yankuna masu yawa a Habasha.

    Yankin da barnar ta fi shafa shi ne gabashin birnin Dire Dawa.

    Mamakon ruwan da aka kwashe lokaci ana yi ya janyo zaizayer kasa a kudancin kasar, wanda ya tilastawa daruruwan mutane barin gidajensu.

    Wannan na zuwa ne daidai lokacin da kasar ke yaki da wannan annoba ta korona.

    Kasar da ke ta biyu a yawan mutane a nahiyar Afrika na da mutanen da suka kamu da cutar 124 - amma yawan annobar da ake samu akai-akai na kara mayar da hannun agogo baya a yakin da kasar ke yi da annobar.

    Kazalika kasar na fada da wani sabon gungun farin dango. Biliyoyin kwari ne dai ke bi ta kasar domin zuwa in da suka nufa, wadanda ke barazana ga harkokin noma da kuma fargabar janyo karancin abinci a kasar.

  11. Faransa ta samu karin mutanen da ke neman tallafi a ko wanne wata

    AFP

    Asalin hoton, AFP

    Hukumomi a Faransa sun ce an samu karuwar mutanen da suka yi rijistar neman tallafin marasa aikin yi a kasar ko wanne wata.

    Adadin mutanen da ke neman tallafi ya karu da kaso bakwai cikin 100, sama da mutum 246,000 - wanda shi ne adadi mafi yawa da aka samu tun 1996 lokacin da aka fara taskance adadin.

    Sama da mutum miliyan 3.7 ne suka yi rijistar neman tallafin a Faransa, sama da miliyan 10 an dakatar da su ne daga aiki na wucin gadi saboda annobar korona.

  12. Uganda ta yi wa fursinoni 800 afuwa domin rage cunkoso a gidajen yari

    Shugaban kasar Uganda Yoweri Museveni ya yi wa firsinoni 833 afuwa domin rage cunkoso a gidajen yari, a wani mataki na yaki da cutar korona a kasar.

    An gabatar wa da shugaba Museveni jerin sunayen wadanda aka yankewa hukunci domin yi musu afuwa, da ya hada da mutanen da aka samu da kananan laifuka kuma suka share kashi uku cikin hudu na wa'adin da aka debe masu.

    Cikin kananan laifukan akwai zaman banza da kuma karya doka da sata ko kuma aikata cin zarafi, da sauran laifukan da kan iya ja a daure mutum daga wata daya zuwa shekara biyu.

    Mata masu ciki da masu shayarwa da kuma tsofaffi na cikin wadanda aka fi yi wa afuwar.

    Wannan adadin dai bai taka kara ya karya ba idan aka kwatanta da yawan fursinonin da ke kasar 63,000.

    Ya zuwa yanzu an tabbatar da wadanda ke dauke da cutar korona a kasar 79 kuma 49 sun warke.

    Babu wanda ke dauke da cutar da ke tsare a wajen kulle masu laifi a kasar.

  13. Gwamnatin Ghana za ta gina asibitotici 90 cikin shekara daya

    Shugaban Ghana

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Ghana Nana Akufo-Addo ya sanar da shirinsa na gina asibitoci sama da 90 cikin shekara daya domin inganta bangaren lafiya a kasar musamman a yanzu da ake fama da annobar korona.

    Shugaban wanda ya sanar da matakin a jawabin da ya gabatar wa ‘yan kasar Ghana a kafar talabijin ya ce cutar korona ta fallasa raunin bangaren lafiya a Ghana.

    Ya ce gwamnati za ta gina asibitoti 88 a unguwanni da guda shida a yankuna da kuma asibitocin cututtuka masu yaduwa guda guda uku a tsakiya da arewacin Ghana.

    Sai dai ‘yan adawa na bayyana shakku kan ikirarin gwamnatin musamman yadda za ta aiwatar da shirin gina asibitocin.

  14. Labarai da dumi-dumi, Buhari zai yi wa 'yan Najeriya jawabi

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai yi wa 'yan kasar jawabi ranar Litinin.

    Mai magana da yawun shugaban Malam Garba Shehu, a sanarwar da ya fitar a Twitter, ya ce shugaban zai gabatar da jawabin ne da misalin karfe 8 na daren Litinin.

    Karo na uku kenan da shugaban zai yi wa 'yan Najeriya jawabi.

    Ana tunanin jawabin shugaban zai mayar da hankali ne kan cutar korona da kuma matakan da gwamnatinsa ke dauka.

    Sannan 'yan kasar za su kasa su ji ko shugaban zai dage dokar hana fita ko tsawaita dokar da ya kafa a Abuja da kuma jihohin Legas da Ogun inda aka shafe makwanni hudu mutane na kulle ba fita

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  15. Almajirai 5 sun kamu da korona a Kaduna

    Hukumomin a Kaduna sun tabbatar da karin mutum biyar da suka kamu da cutar korona.

    Gwamnatin Kaduna ta sanar a shafinta na Twitter cewa almajirai ne da aka dawo da su daga Kano wadanda ma'aikatar lafiya ta tabbatar da suna dauke da cutar korona.

    Sanarwar ta ce an killace almajiran a cibiyar da ake kula da masu cutar korona a jihar.

    Yanzu adadin mutum 9 ke dauke da cutar korona a Kaduna.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  16. Kungiyoyin Seria A za su dawo atisaye

    Za a ba 'yan wasan kungiyoyin gasar Seria A a Italiya damar fitowa atisaye daga ranar 4 ga Mayu, sannan tawagar kungiyoyin za su ci gaba da atisaye daga ranar 18 ga Mayu, kamar yadda Firaministan Italiya ya sanar daga cikin matakan farko na dage dokar hana fita.

    Ana fatan za a dawo da wasannin Seria A tsakanin 27 ga watan Mayu zuwa 2 ga Yuni, inda ake tunanin kammala wasannin kakar bana a watan Agusta.

    Ana kuma fatan za a kammala gasar Premier ta Ingila, yayin da gwamnatin kasar ke kokarin ganin yadda za a ci gaba da wasannin ba tare da 'yan kallo ba.

    Cristiano Ronaldo

    Asalin hoton, Getty Images

  17. Gwamnatin Borno ta nemi afuwar mai cutar korona

    Gwamnatin Borno ta nemi afuwar matar da aka ce ta gudu bayan gwaji ya tabbatar da tana dauke da cutar korona.

    Gwamnatin Borno ta ce matar mai shekara 41 ta gabatar da kanta a asibitin koyarwa na Jami’ar Maiduguri.

    Matar ta ce babu wanda ya tuntube ta daga asibitin koyarwa na jami’ar Maiduguri, ko daga bangaren hukumomin lafiyar jihar inda jami’an asibitin suka nemi afuwa.

    Tun da farko kwamishinan lafiya na jihar Dr. Salisu Kwayabura ya ce an gano daya matashin da ya tsere mai shekara 24.

    A ranar Lahadi ne hukumomin lafiya a Borno suka sanar da cewa suna farautar wasu masu dauke da cutar korona guda biyu mace da namiji da ba gansu ba.

  18. Kwankwanso ya rubutawa Buhari wasika kan mace-macen Kano

    Tsohon gwamnan Kano Sanata Rabiu Musa Kwankwanso ya rubutawa shugaban Najeriya Muhammadu Buhari wasika kan yawan mace-macen da ke faruwa a Kano.

    Sanata Kwankwaso ya bukaci gwamnatin Tarayya ta gaggauta daukar mataki domin ceto rayukan al'umma.

    A cikin wasikar da ya wallafa a shafinsa na Twitter, tsohon gwamnan ya ce ya rubuta wasikar ne saboda a cewarsa abin da ke faruwa a Kano abin tsoro ne musamman yadda mutane ke mutuwa kusan a kullum tun bayan soma yaki da cutar korona a jihar da kuma hana mutane fita.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  19. Coronavirus: Mutum 9,000 sun warke a Afirka - WHO

    Hukumar lafiya ta duniya WHO ta ce sama da mutum 31,000 suka kamu da cutar korona a Afirka.

    Cutar kuma ta kashe mutum 1,400 a nahiyar Afirka.

    Amma sama da mutum 9,000 suka warke kamar yadda reshen hukumar a nahiyar Afirka ya wallafa a Twitter.

    A Afirka ta kudu ne cutar ta fi yaduwa a Afirka, inda mutum 4,546 suka kamu da cutar. Sai kuma Algeria inda mutum 3,382 suka kamu.

    Najeriya ce ta biyar a yawan masu dauke da cutar bayan Kamaru da ke matsayi na uku da kuma Ghana a matsayi na biyar.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  20. Cutar korona ta kashe mutum biyu a Kano

    Hukumomi a jihar Kano sun sanar da karin mutum biyu da cutar korona ta kashe a jihar.

    Yanzu mutum uku cutar korona ta kashe a jihar, kamar yadda ma'aikatar lafiya a jihar ta sanar a shafinta na Twitter a ranar Litinin

    Sai dai alkalumman yawan wadanda suka kamu da cutar korona ba su sauya ba daga mutum 77 da hukumar yaki da cutuka masu yaduwa a kasar ta sanar ranar Lahadi.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X