Masu dauke da cutar korona sun tsere a Borno

Wannan shafi na kawo muku bayanai kai tsaye dangane da annobar korona da ke ci gaba da yaduwa a fadin duniya, inda mutum fiye da milyan biyu da dubu dari shida suka kamu sannan fiye da 200,000 suka mutu.

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail and Awwal Ahmad Janyau

  1. Isra'ila ta sassauta dokar zaman gida

    Isra'ila

    Asalin hoton, AFP

    Isra'ila ta bai wa wuraren kasuwanci damar budewa a ranar Lahadi sannan ta ce tana tunanin bude makarantu ma.

    Shagunan da ke kan titi za su iya budewa amma ban da manyan kantuna wato shopping malls da kuma kasuwanni.

    Bisa tanadin sabuwar dokar kullen, wuraren sayar da abinci na da damar sayar da abincin ga masu tafiya, ba wadanda za su ci a wurin ba, da kuma kai wa gida-gida.

    Sai dai hukumomi sun ce za a iya sauya dokar matukar aka ci gaba da samun adadi mai yawa na mutanen da ke kamuwa da cutar.

    Mutum kusan 15,398 ne suka kamu da cutar korona a kasar sannan 199 suka mutu.

  2. A jita-jitar kasuwar saye da musayar 'yan kwallo ta yau...

    Paul Pogba

    Asalin hoton, EPA

    • Kungiyar PSG ta nemi sayen Paul Pogba na Manchester United, mai shekara 27 - kuma a cikin yarjejeniyar dauko shi har da bayar da Angel di Maria, mai shekara 32, wanda bai tabuka abin kirki ba a Old Trafford a shekarar 2015. (Mail)
    • Cristiano Ronaldo, mai shekara 35, ya sha alwashin ci gaba da zama a Juventus zuwa 2022 a yayin da ake rade-radin cewa zai koma Manchester United. (Sun)
    • Mahaifin Pierre-Emerick Aubameyang ya bai wa dan wasan na Gabon mai shekara 20 shawarar sabunta kwantaraginsa a Arsenal a wani sakon Instagram da ya wallafa dauke da hoton dan wasan yana sanya hannu kan kwangilarsa ta farko a kungiyar. (Mirror)
    • Borussia Dortmund ta yi amannar cewa za ta iya rarrashin dan wasan Ingila Jadon Sancho, mai shekara 20, ya ci gaba da zama a kungiyar duk da hasashen da ake yi cewa ya amince ya koma Manchester United. (Teamtalk)
  3. Saudiyya ta sassauta dokar kulle

    Saudiyya

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, Fiye da mutum 16,000 ne aka tabbatar sun kamu da cutar korona a Saudiyya

    Kasar Saudiyya ta sassauta wasu daga cikin matakan hana zirga-zirga da ta saka a ranar Lahadi.

    Dokar hana fita ta ba-dare-ba-rana da aka saka, an dage ta daga karfe 9:00 na safe zuwa 5:00 agogon kasar.

    Daga ranar Laraba kuma shaguna za su samu damar budewa sannan wasu ma'aikatun su dawo bakin aiki.

    Sassaucin wanda zai kai har mako biyu na watan watan Ramadana, bai hada da wuraren da za a samu taruwar jama'a ba kamar wuraren cin abinci da na yin atasaye.

    Biranen Makkah da Madinah za su ci gaba da kasancewa cikin dokar hana zirga-zirga.

    Fiye da mutum 16,000 ne aka tabbatar sun kamu da cutar korona a kasar sannan wasu 136 suka mutu.

  4. Mutum hudu sun kamu da korona a Kano

    Ma'aikatar Lafiya ta Jihar Kano ta ce wasu mutum hudu sun kamu da cutar korona, abin da ya kawo jumillar adadin wadanda suka kamun zuwa 77 a jihar.

    A wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na Twitter, ma'aikatar lafiyar ta ce ya zuwa karfe 12:30 na daren Lahadi 26 ga watan Afrilu, mutum 77 ne suka harbu da cutar korona, mutum daya ya mutu.

    Tun a ranar Laraba ne rahotanni suka bayyana cewa an rufe dakin gwajin cutar korona da ke Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano da ke birnin Kano, kuma sai da aka yi kwana biyu a jere hukumar NCDC ba ta bayar da rahoton sabbin mutanen da suka kamu ba daga Kano.

    Dr Sani Aliyu, babban jami'i a kwamitin gwamnatin tarayya da ke yaki da yaduwar korona, ya ce an rufe cibiyar gwajin ne bayan wasu ma'aikatan lafiya sun harbu da cutar.

    Tuni gwamnatin ta ce ta tura tawaga ta musamman zuwa Kano domin farfado da ayyuka a cibiyar.

    Masana harkar lafiya suna ta kiraye-kiraye ga gwamnatin tarayya da kai wa jihar dauki, ko kuma ta zama cibiyar cutar ta korona, a cewar Farfesa Usman Yusuf.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  5. Maraba da Watan Ramadana

    Duk da cewa yau kwana na uku kenan a cikin watan Azumin Ramadana da al'ummar Musulmi ke yi duk shekara, mun shirya muku wannan bidiyon ta maraba da shigowa watan mai alfarma.

    Halima Umar Saleh, mai kula da wannan shafi na bbchausa.com, da kuma Fatima Othman, 'yar jarida mai shirya bidiyo, su ne da wannan aiki.

    Ku latsa hoton kasa kawai ku sha kallo

    Bayanan bidiyo, Maraba da Watan Ramadan, ga wasu abubuwa dangane da shi
  6. Cutar korona ta kashe mutum fiye da dubu 200 a duniya

    Gawar cutar korona

    Asalin hoton, Getty Images

    Fiye da mutum dubu 200 ne suka mutu a fadin duniya sakamakon annobar cutar korona, a cewar alkaluma daga Jami'ar Johns Hopkins, mai bin sahun yaduwar cutar.

    Mutum sama da miliyan biyu da dubu 800 ne kuma suka harbu da cutar da ake kira da Covid-19 a harshen Ingilishi.

    Wannan na zuwa ne bayan fiye da mutum 50,000 sun mutu a Amurka, yayin da annobar mafi muni ke ci gaba da tagayyara al'amura.

    A ranar 11 ga watan Janairu ne wata kafar yada labaran China ta ruwaito mutum na farko da cutar kashe. Tuni kasashe da yankuna fiye da 210 suka bayar da rahoton bullar cutar.

  7. Barka

    Masu bibiyarmu barkanku da safiyar Lahadi 26 ga watan Afrilu.

    Umar Mikail ke muku barka da shigowa shafin namu mai kawo labarai kai-tsaye.

    Da fatan za ku kasance tare da mu har zuwa dare.