Wannan shafi na kawo muku bayanai kai tsaye dangane da annobar korona da ke ci gaba da yaduwa a fadin duniya, inda mutum fiye da milyan biyu da dubu dari shida suka kamu sannan fiye da 200,000 suka mutu.
Rahoto kai-tsaye
Umar Mikail and Awwal Ahmad Janyau
Rufewa
Da fatan an sha ruwa lafiya. A nan za mu dakatar da kawo labarai da rahotanni kai-tsaye musamman kan abubuwan da ke faruwa game da cutar korona daga sassan duniya.
Sai ku kasance da mu Idan Allah Ya kai mu gobe, inda za mu ci gaba da kawo ma ku labarai da rahotanni kai-tsaye.
Masu dauke da cutar korona sun tsere a Borno
Gwamnatin Borno ta ce tana neman wasu mutum biyu mace da namiji da suka tsere bayan gwaji ya tabbatar da suna dauke da cutar korona.
Sanarwar da Isa Gusau, kakakin gwamnatin jihar ya fitar ta ce namijin mai shekara 24, tun da hukumomin lafiya suka kira shi, ya kashe wayarsa, tare da kashe ta mahaifiyarsa da ake tuntubarsa.
Matar da aka bayyana shekarunta 42 ita ma ta gudu, a cewar sanarwar.
Kwamishinan lafiya na jihar Dr Kwayabura ya yi kira ga duk wanda gwaji ya tabbatar da yana dauke da cutar kada ya dauka mutuwa zai yi domin mutane da yawa sun warke daga cutar, ya gabatar da kansa a killace shi domin kada ya baza cutar ga jama'a.
Asalin hoton, @ProfZulum
Elrufa'i ya tsawaita dokar hana fita a Kaduna
Gwamnatin Kaduna da ke arewacin Najeriya ta tsawaita dokar hana fita tsawon wata daya a yunkurinta na dakile bazuwar cutar korona a jihar.
Gwamnatin jihar ta sanar a shafinta na Twitter cewa gwanna Malam Nasir Elrufa'i ya tsawaita dokar ne bisa shawarwarin da kwamitin jihar kan cutar korona ya bayar karkashin jagorancin Mataimakiyar gwamnan jihar, Dr Hadiza Balarabe.
Sanarwar ta ce dokar za ta fara aiki daga ranar Lahadi 26 ga Afrilu.
A ranar 26 ga watan Maris ne gwamnatin Kaduna ta sanar da dokar hana fita a jihar.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.
Karshen labarin da aka sa a X
Coronavirus: Yawan masu mutuwa a Turai sun ragu
An fara samun
saukin annobar cutar korona a kasashen Turai guda uku da cutar ta fi yi wa
illa.
An samu raguwar
masu mutuwa a Faransa da Italiya da Spain, kasashen Turai da cutar korona ta fi yi wa
illa.
A karon farko adadin wadanda
suka mutu a rana daya ba su kai mutum 300 ba, adadi mafi kankanta da aka gani
sama da wata daya.
Sai dai a
Birtaniya har yanzu wadanda ke mutuwa a rana daya sun haura 400.
Faransa da Spain
da Italiya sun sassauta dokar hana fita, inda Spain ta ba yara kanana damar
shakatawa na tsawon sa’a daya karkashin kulawar iyayensu.
Jami'an lafiya sun dauki gawar da aka gani gefen titi a Kano
Asalin hoton, Adamu Yaya
Asalin hoton, Adamu Yaya
Asalin hoton, Adamu Yaya
‘An rufe asibitoci masu zaman kansu a Kano’
Rahotanni daga
Kano sun ce hukumomi a jihar sun sanar da rufe asibitoci da cibiyoyin binciken
lafiya masu zaman kansu a fadin jihar.
Jaridar
Kano Focusa labarin da ta wallafa ta ce hukumar da ke kula da asibitoti masu zaman kansu ta
jihar Kano ce ta sanar da daukar matakin.
Kuma shugaban
hukumar Usman Tijjani ya ce an dauki matakin ne domin dakile yaduwar cutar corona
a tsakanin al’umma.
‘Yan kwanakin nan mace-macen al'umma sai karuwa suke a Kano wanda ake alakantawa da cutar korona.
Asalin hoton, Salihu Tanko Yakasai
Jamus za ta fara amfani da manhajar gano masu cutar korona
Asalin hoton, Getty Images
Kasar Jamus za ta fara amfani da tsarin wata sabuwar
manhaja da za ta adana bayanan mutane a wayoyinsu na salula maimakon babban
rumbun tattara bayanai.
Manhajar
wadda Google da Apple suka samar tana amfani ne da bulutut inda za ta sanar da masu amfani da salula nan take idan sun yi mu’amula da mai dauke da cutar
korona.
Ana ganin manhajar
tana da muhimmanci a yakin da ake da annobar korona yayin da kasashe kamar
Jamus suka sassauta dokar hana fita.
Jamus ta goyi
bayan manhajar da masana kimiya kimanin 130 a Turai suka samar. Amma masu suka
na ganin manhajar za ta ba gwamnatoci damar yin kutse ga bayanan mutune wanda
zai iya sa su dinga bibiyar abin da mutane ke yi da sa ido.
Legas ta tilasta wa mutane amfani da abin rufe hanci
Hukumomi a Legas kudancin Najeriya sun tilasta wa mutanen jihar amfani da abin rufe baki da hanci domin dakile yaduwar cutar korona.
Gwamnan jihar ya ce rufe fuska da hanci tare da yawaita wanke hannu, hanyoyi ne da idan an kiyaye za su takaita yaduwar cutar.
Gwamna Babajide Sanwo-Olu ya ce yanzu amfani da abin rufe baki da hanci ya zama wajibi ga al'ummar jihar
Cutar korona zuwa yanzu ta kama mutum 1,182 tare da kashe 35 a Najeriya, kuma jihar Legas ce cutar ta fi bazuwa inda ta kama 689 da kashe 19.
Gwamna Sanwo-Olu ya ce za a ci tarar duk wanda ya ki saka abin rufe fuska a taron jama'a, inda ya ce za a samar da shi wanda zai wadaci kowa.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.
Karshen labarin da aka sa a X
Labarai da dumi-dumi, Cutar korona ta kara kashe mutum 413 a Birtaniya
Hukumomin Birtaniya sun ce an kara samun mutum 413 da cutar korona ta kashe a asibitocin kasa, inda yanzu yawan wadanda suka mutu a kasar suka kai 20,732.
Babu cutar korona a jihohi bakwai na Najeriya
Asalin hoton, Getty Images
Duk da cewa cutar korona ta bazu a jihohin Najeriya bayan fara bullarta a Legas kudancin kasar ranar 27 ga watan Fabrairun 2020 amma har yanzu akwai jihohin da cutar ba ta bulla ba.
Zuwa yanzu cutar ta yadu a jihohi 26 na Najeriya hadi da Abuja. Kuma yanzu alkalumman hukumar NCDC sun nuna yawan wadanda suka kamu da cutar sun kai 1,182 yayin da 222 suka warke, 35 kuma suka mutu.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.
Karshen labarin da aka sa a X
Sauran jihohin da har yanzu ba a samu bullar cutar ba sun hada da:
1. Bayelsa
2. Cross River
3. Ebonyi
4. Kebbi
5. Kogi
6. Nassarawa
7. Yobe
An fara sassauta dokar hana fita a Turai
Asalin hoton, Getty Images
Kasashen Turai da dama sun fara sassauta dokar hana fita da suka kafa domin dakile yaduwar cutar korona.
Spain da cutar ta kashe fiye da mutum 20,000, an ba yara damar fita zuwa harabar gida su yi wasa karkashin kulawar babba na tsawon sa'a daya.
An bude kananan shagunan 'yan kasuwa a Jamus da Italiya da Faransa.
Birtaniya ta ce lokaci bai yi ba da za ta sassauta dokar hana fita.
A Italiya, makarantu za su ci gaba da kasancewa a rufe har zuwa watan Satumba.
An wayi gari da gawa yashe a gefen titi a Kano
Asalin hoton, Getty Images
Wasu al'ummar jihar Kano sun wayi gari tare da wani kwance a gefen titi, wanda ake tunanin gawa ce.
Mazauna kusa da barikin sojoji na Bukavu da ke Kofar Ruwa a Kano sun ce sun samu wani mutum yashe a gefen titi, kuma suna tunanin ya shafe sama da sa'a 24.
Wani mazauni unguwar ya shaida wa BBC cewa tun a ranar Juma'a suka ga mutumin yana zaune a bakin Titin Katsina.
Ya ce "misalin karfe 11:00 na ranar Asabar ne kuma mutane suka fara taruwa a kansa kuma suka yi amannar cewa ya rasu, kuma nan take suka tuntubi jami'an tsaro amma ba su samu nasara ba."
"Da farko mun tuntubi 'yan kwana-kwana a Bacirawa sai suka ce yankin bai shafe su ba," in ji shi.
BBC ta tuntubi kakakin rundunar 'yan sandan jihar Kano, kuma ya ce sun samu labarin gawar, amma ya ce kula da gawar ba hakkinsu ba ne, hakkin jami'an lafiya ne.
Mutanen unguwar sun ce sun kai rahoto ofishin 'yan sanda na Dala, inda aka shaida ma su cewa sai dai su tuntubi ma'aikatar lafiya. "Mun kira lambobin hukumar NCDC amma lambar ta ki shiga," in ji Benjamin daya daga cikin mazauna unguwar.
Ya kara da cewa daga baya sun je Asibitin Murtala, sun je wurin me Unguwar Dala amma babu wanda ya je wurin gawar. Kuma har zuwa karfe 12:30 a yau Asabar gawar na nan yashe a gefen titi.
A 'yan kwanakin nan an samu mace-mace a Kano da mazauna jihar ke cewa ba a saba gani ba.
Rahotanni sun nuna cewa an yi rashin manyan mutane da suka hada da manyan malaman jami'a da tsofaffin ma'aikatan gwamnatin jiha da na tarayya.
Gwamnatin Iran za ta bari a soma sallah a masallatai
Asalin hoton, Getty Images
Iran na shirin bude masallatai sannan ta bari a
gudanar da sallar Juma’a, a cikin shirin kasar na kawar da cutar Korona wacce
ta barke a kasar.
Wata sanarwa daga oifishin shugaba Hassan Rouhani ba
ta fayacce lokacin da za a bar masallatan sun soma yin sallolin jam’i ba.
Sai dai hakan na cikin shirin gwamnati na sassauta
dokokin da aka kafa wajen dakile yaduwar cutar Korona.
A cikin ‘yan makonnin nan an bar kananan shaguna su
soma cin kasuwa.
Amma makarantu sun ci gaba da kasancewa a rufe sannan
an haramta harkokin wasanni.
Mutuwar Jama'a: Me ke faruwa ne a jihar Kano ?
Asalin hoton, Salihu Tanko Yakasai
Mutuwar mutane a jihar Kano na janyo cece-kuce a tsakanin al'ummar Najeriya ganin cewa kawo yanzu hukumomi basu fito sun bayyana abin da ke haddasa karin mace-macen ba.
Rahotanni sun nuna cewa a ranar Asabar mutane da dama ne suka rasu a cikin jihar abin da ke kara jefa tsoro a tsakanin al'ummar jihar da ma wasu a arewacin kasar.
Jaridar Punch ta wallafa rahoton cewa cikin sa'o'i 10 a ranar Asabar, fitattun mutane 12 ne suka rasu a jihar Kano ciki hadda Farfesa Ibrahim Ayagi da Dr Musa Umar Gwarzo da Musa Tijjani watau Editan Jaridar Triumph.
A ranar Talatar da ta wuce Jaridar Daily Trust ta ce mutane fiye da 150 ne aka birnne a makabartu uku a jihar Kano.
Sai dai gwamnatin jihar a lokacin ta musanta karuwar mace-mace amma ta sha alwashin gudanar da bincike.
Iyayen da ke fama da yara marasa ji lokacin kulle
Asalin hoton, Getty Images
A wurin wasu iyayen zama a gida tare da yaransu kanana na nufin fuskantar barazana da cin mutunci da takura ne za su karu.
Ya suke fama da wannan dokar ta hana fita da takaita zirga-zirga?
Julie ta gano cewa za ka iya sayen doguwar wuka a intanet, yayin da ta ga danta na caccaka wa kujerun gidanta wuka.
A 'yan watannin da suka gabata, sai da ta kira 'yan sanda sau biyu har gidanta, a baya-bayan nan an kulleta a bandaki yayin da danta wanda yake matashi ya yi kokarin karya kofar gidan da wuka don ya fita.
Yanzu duka iyalin na zaune tare a lokacin wannan dokar hana fita, suna fama da zaman kadaitaka, rashin hadin kai da zaman tsoro.
Fiye da mutum dubu 200 ne suka mutu a fadin duniya sakamakon annobar cutar korona, a cewar alkaluma daga Jami'ar Johns Hopkins, mai bin sahun yaduwar cutar. Kazalika mutum sama da miliyan biyu da dubu 800 ne suka harbu da cutar, wadda ake wa lakabi da Covid-19.
Hukumar NCDC mai yaki da yaduwar cutuka a Najeriya ta bayar da rahoton samun mutum hudu da suka kamu da cutar korona a Jihar Kano, abin da ya kawo jumillarsu zuwa 77 da mutuwar mutum daya. Kwana biyu kenan a jere ba a ji rahoton cutar daga Kano ba bayan rufe cibiyar gwajin cutar da aka yi tun ranar Laraba a jihar sakamakon wasu ma'aikatan lafiya da suka harbu da cutar.
Hukumomi a birnin Wuhan na China, inda cutar ta fara bulla, sun ce babu sauran me cutar ko daya yanzu da yake jinya a asibiti. Mai magana da yawun Ma'aikatar Lafiya ta kasa Mi Feng, ya ce an sallami mutum na karshe da ya yi jinya a asibiti a ranar Juma'a.
Kasar Saudiyya ta sassauta wasu daga cikin matakan hana zirga-zirga da ta saka a ranar Lahadi. Dokar hana fita ta ba-dare-ba-rana da aka saka, an dage ta daga karfe 9:00 na safe zuwa 5:00 agogon kasar, kuma sassaucin zai yi aiki har zuwa mako biyu na farkon watan Ramadana.
Jami'ar Bayero za ta kafa cibiyar gwajin cutar Korona
Asalin hoton, Getty Images
Shugaban jam’iar Bayero ta Kano ya ce jami’ar na shirin kafa cibiyar gwajin cutar Korona domin taimakawa gwamnatin jihar wajen kawar da annobar.
Farfesa Muhammad Yahuza Bello ya shaidawa manema labarai cewa cibiyar gwajin ta samu amincewar cibiyar dakile yaduwar cututtuka ta kasa watau NCDC.
A hirarsa da manema labarai a Kano, Farfesa Bello ya ce ana sa ran nan da kwana 10 cibiyar za ta soma aiki.
Ya kara da cewa jami’an hukumar NCDC sun ziyarci cibiyar domin gani da ido aikin da suke yi wanda aka kashe fiye da naira miliyan 50 wajen tsara shi.
“Mu a jami’ar Bayero muna kokarin gannin mun taimaka wajen shawokan wannan matsalar,” in ji shugaban jami’ar.
Akwai jibiyar wajen cutar Korona a Kano wacce ke asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano.
Izuwa ranar 25 ga watan Afrilu, akwai mutum 77 dauke da cutar Korona a Kano a yayin da a fadin Najeriya mutum 1,182 ne suka kamu da cutar ta covid-19.
Direbobi sun zargi jami’an tsaro da kawo tsaiko wajen rarraba kayan abinci
Kungiyar
masu motocin haya na dakon kaya ta NARTO ta yi korafin cewa wasu jami'an tsaro
da ke kan hanya na tsare direbobin da su ke jigilar kayayakin abinci abin da ke
janyo lalacewar kayan abincin.
Kungiyar
ta yi kira ga hukumomin Najeriya musamaman manyan jami'an tsaro da ke sa ido
kan lamuran zirga-zirga da su magance musu wannan matsalar da ke ci masu tuwo a
kwarya.
Mataimakin
shugaban Kungiyar Alhaji Abubakar Sidi Sifawa ya shidawa BBC cewa wasu direbobin
a kan tsare motocinsu na tsawon lokaci
“Korafe-korafe daga direbobi shi ne
cewa kananan jami’an tsaro na gallazawa musu, kuma muna son manyan jami’an
tsaro su ja kunnen dakarun da ke kan hanya,” in ji Alhaji Abubakar.
Ya kara da cewa wasu direbobin sun
dauko kankana da albasa da ma wasu kayayyakin abinci masu lalacewa kuma daga
bisani sai a yi hasararsu.
An
sanya dokar hana fita a jihohi da dama a Najeriya amma gwamnati da amince a ci
gaba da jigilar kayan abinci da kuma magunguna.
'Babu sauran me cutar korona a asibitocin birnin Wuhan', inda annobar ta faro
Asalin hoton, Getty Images
Hukumomi a birnin Wuhan na China, inda annobar cutar korona ta fara bulla, sun ce babu sauran me cutar ko daya yanzu da yake jinya a asibiti.
Mai magana da yawun Ma'aikatar Lafiya ta kasa Mi Feng, ya ce an sallami mutum na karshe da ya yi jinya a asibiti a ranar Juma'a.
Kazalika sun tabbatar cewa ba a samu wani sabo da ya kamu da cutar ba a birnin.
Tun bayan bullar annobar a watan Disamba, China ta bayar da rahoton samun mutum 82, 816 da suka harbu da ita sannan ta ce 4,632 ne suka mutu.
A birnin Wuhan kuwa, mutum 46,452 ne suka kamu - kashi 56% kenan na jumillar marasa lafiyar a kasar.
Sojoji sun kashe 'yan bindiga 89 a Zamfara
Asalin hoton, Nigerian Army
Bayanan hoto, Sojojin sun yi nasarar kwato makamai da dama a cewar rundunar
Rundunar sojin Najeriya ta ce ta kashe 'yan bindiga 89 da ke kai hare-hare a kan farar hula a jihar Zamfara.
Kakakin Rundunar, Manjo Janar John Enenchie, ya ce sun samu taimakon daga jihar Neja wajen kai wa 'yan bindigar farmaki.
A cewarsa kuma sun yi nasarar kwato makamai da daruruwan shanu da aka sace.
Asalin hoton, Nigeria Defence
An kuma ceto mutum biyar da aka yi garkuwa da su.
Sama da shekaru biyar kenan da jihar Zamfara da wasu jihohi makwabta ke fuskantar hare-hare babu kakautawa na 'yan fashi da ke sake kassara arewacin kasar data sha fama da rikicin Boko Haram.