Ba za mu lamunci 'wariyar launin fata' daga China ba – Najeriya

Wannan shafi na kawo muku bayanai kai tsaye dangane da annobar korona da ke ci gaba da yaduwa a fadin duniya.

Rahoto kai-tsaye

Usman Minjibir and Umar Mikail

  1. Rüdiger zai taimaka wa 'yan kasuwar Saliyo da abin rufe fuska

    Antonio Rüdiger

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Iyayen Antonio Rüdiger 'yan kasar Saliyo ne wato Sierra Leone

    Dan wasan bayan Chelsea Antonio Rüdiger ya kaddamar da wata gidauniya ta tara kudi domin saya wa 'yan kasuwa takunkumin rufe fuska a kasar Saliyo wato Sierra Leone.

    Rüdiger ya ce yana fatan za su kare su sannan su dakile yaduwar cutar ta korona.

    Ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa gidauniyar tasa za ta yi hadin gwiwa da gidauniyar Mary-Ann Kaikai da kuma Lunchbox Gift domin samar da takunkumi 60,000.

    Rüdiger wanda iyayensa 'yan Saliyo ne, ya kuma roki abokan wasansa na Premier League da su tara $30,000 (kusan naira miliyan 11).

    Ya kuma gode wa Mesut Özil da N'Golo Kanté da Callum Hudson-Odoi da Olivier Giroud bisa taimakon da suka bayar.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  2. Coronavirus: 'yan wasan Arsenal guda hudu da suka karya dokokin tazara

    Arsenal Players

    Asalin hoton, Getty Images

    'Yan wasan Arsenal guda hudu sun kasance 'yan wasan gasar Premier Ingila na baya-bayan nan da aka kama da laifin karya dokokin gwamnati na samar da tazara a tsakanin jama'a.

    David Luiz da Granit Xhaka sun hadu da juna a wurin shakatawa na London Park, inda aka haska Nicolas Pepe yana yin bal tare da abokansa sannan kuma Alexandre Lacazette an gan shi yana tsaye kusa da wani mutum da ke goge masa mota.

    Tuni dai kulob din ya ja hankalin 'yan wasan nasa guda hudu kan abin da suka aikata.

    Shi ma kulob din Tottenham na da mutum uku da suka karya irin wannan doka ciki kuwa har da kocin kulob din, Jose Mourinho.

    An samu dan wasan Manchester City, Kyler Walker da Jack Grealish na Aston Villa da dan wasan Ingila, Wayne Rooney da laifin taka wannan doka.

  3. Coronavirus ta kashe mutum 22,000 a Sipaniya

    Ma'aikatar lafiyar kasar Sipaniya ta ce annobar korona ta kashe 'yan kasar fiye da 22,000.

    A awa 24 da suka gabata mutu 440 sun mutu sakamakon cutar ta korona, inda adadin masu mutuwar ya zama 22,157.

    Sipaniya dai na daga cikin kasashen da suke a gaba-gaba wajen yawan masu dauke da cutar korona a duniya.

  4. Coronavirus: Dalilin da ya sa na bayar da asibitina - Kwankwaso

    Kwankwaso

    Asalin hoton, Kwankwaso

    Tsohon gwamnan jihar Kano Injinya Rabi'u Musa Kwankwaso ya yi karin bayani kan abin da ya sa ya bayar da gudunmuwar asibiti ga gwamnatin abokin hamayyarsa Abdullahi Umar Ganduje don jinyar masu fama da cutar korona.

    Kwankwaso ya ce "wannan gini an tanade shi ne domin amfanin mambobinmu na Kwankwasiyya da ma dukkan dan jihar Kano. Kuma bayan kammala shi mu shigo da kayan aiki sai ga wannan ciwo ya shigo. Shi ya sa muka sayo kayyakin yaki da korona.

    Akwai ma wasu karin wurare kamar dakunanmu na taro da idan bukatar bayar da su ta taso to za mu bayar da su. Amma muna fata Allah ya takaita."

    Tsohon gwamnan ya kuma yi karin haske kan mahawarar da ake yi dangane da gadajen karfe da aka tanada a asibitin, maimakon irin gadajen da ake amfani da su a asibitoci.

    "Kayan da muka yi oda ba su iso ba. Wadannan gadajen da ma suna cikin wurin."

    Kwankwaso ya ce ya bayar da asibitin ne har zuwa lokacin da aka ga bayan cutar korona.

    Sai dai ya ce har yanzu kwamitin da ke yaki da cutar ta korona bai tabbatar da karbar asibitin ba ko akasin haka.

  5. Sheikh Dahiru Bauchi ya koma yin tafsiri a Bauchi saboda korona

    Dahiri Bauchi

    Asalin hoton, Dahiru Bauchi family

    Yayin da musulmi ke shirin fara azumin watan Ramalan dai tuni dai Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya fara tafsirin Alkur'ani da ya saba gudananarwa duk shekara.

    Sai dai ba kamar a baya ba, Tafsirin na wannan shekarar za a yi shi ne a birnin Bauchi maimamon Kaduna da ya kwashe shekaru 40 yana yi a can.

    Sakamakon matsalar yaduwar cutar korona, a bana malamai da dama sun sauya salon yadda suke tafisirin, inda za su ringa watsa shi ta kafofin sada zumunta, maimakon yadda jama'a suke taruwa a wajen Tafsirin.

    Shehin Malamin Dahiru Bauchi ya shaida wa BBC cewa yanzu haka za a rinka watsa tafsirin a gidajen rediyo da kuma kafafen sada zumunta.

    Sai dai ya ce ba zai hana jama'a zuwa wurin tafsirin nasa ba tun da a jihar Bauchi babu dokar kulle, amma ya ce za a yi kokarin ganin an samar da tazara a tsakanin mahalarta Tafsirin.

  6. Coronavirus: Kano ta maya da almajirai 433 zuwa Katsina

    Almajirai

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumomin jihar Katsina da ke arewacin Najeriya sun ce suna sa ran sake karbar wani rukuni na almajiran jihar daga makwabciyar jihar Kano a yau Alhamis.

    Hukumomin dai sun tabbatar da karbar almajirai 419 ‘yan asalin jihar da gwamantin Kano ta mika masu a shekaran jiya.

    Mustapha Muhammed Inuwa wanda shi ne sakataran gwamnatin jihar katsina ya shaida wa BBC cewa zuwa yanzu dai almajiran jihar ta Katsina guda 433 ne su ka isa jihar daga Kanon.

  7. Coronavirus: Al'ummar Kano sun sami dagin Alhamis domin cefane

    Kano

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Hoton wani bangaren Kano da aka dauka a 2006

    Gwamnatin jihar Kano a arewacin Najeriya ta sassauta dokar hana fita da ta sanya a jihar, inda ta ba da damar fita yau Alhamis.

    A wata sanarwa da Salihu Tanko Yakasai da ke taimaka wa gwamnan kan kafofin sada zumunta ya wallafa a shafinsa na Twitter, gwamnan ya ce dokar hana fitar za ta ci gaba da aiki daga karfe 12 na daren Juma'a, kuma za a ci gaba da zama a gida har zuwa wata juma'ar.

    A jiya ne dai aka cika mako guda da fara aiki da dokar hana fita a jihar, don yaki da cutar korona.

    Tuni dai wasu shugabanni a Kanon suka fara kira ga gwamnatin tarayya da ta kai wa jihar dauki kan yunkurin da jihar ke yi na yaki da cutar korona.

    Sanatan Kano ta Kudu Barau Jibrin ya fitar da wata takarda yana rokon gwamnatin tarayya ta kai wa Kano dauki tun kafin lamarin ya kara muni.

  8. Coronavirus: Al'ummar jihar Bornon Najeriya sun wayi gari a dokar hana fita

    Farfesa Umara Zulum

    Asalin hoton, Twitter

    Al’ummar jihar Borno mai fama da hare-haren Boko Haram sun wayi gari yau cikin dokar hana fita wadda gwamnatin jihar ta saka domin hana yaduwar cutar Corona.

    Hukumomin jihar sun dauki wannan matakin ne bayan rasuwar mutum na farko sakamakon cutar, yayinda 9 zuwa yanzu suka kamu da cutar.

    Gabanin soma aikin dokar cikin daren jiya, jama’a sun rika tururuwa zuwa kasuwanni domin sayen kayan amfanin yau da kullum.

  9. Coronavirus: Vietnam za ta dage dokar kulle

    Vietnam

    Asalin hoton, Getty Images

    Vietnam za ta dage dokar hana fita a fadin kasar bayan shafe mako guda ba tare da samun mutu ko guda daya ba da ya sake kamuwa da cutar korona.

    Mutane 268 ne kawai suka kamu da cutar, sannan ba a samu mutuwa ko guda ba, abin da ya sa ake yaba salon gwamnatin Kwamunusancin kasar kan yadda ta shawo kan yaduwar annobar tsakanin al'ummarta da masu yawan kimanin miliyan 100.

    Vietnam dai ta nuna jajircewar siyasa, tsari da hadin-kan al'umma da suka kubutar da ita daga munin wannan annoba, da ka iya tasiri ga fannin lafiyarta mai rashin inganci.

  10. Coronavirus: An cire mutumin da ba ya son gwaji da maganin maleriya daga mukaminsa

    Shugaban hukumar da ke sa ido kan cigaban da ake samu a kokarin samar da rigakafin cutar korona a Amurka, ya ce an cire shi daga mukaminsa, saboda kin amincewa a yi amfanin da wasu magungunan maleriya guda biyu kamar yadda Shugaba Trump ya bukata a matsayin maganin cutar korona.

    Dakta Rick Bright, ya ce ware shi ana tsaka da wannan annoba da sako siyasa da bai wa san zuciya fifiko za su jefa rayuwar Amurkawa a cikin hadari.

    Shugaba Trump dai ya sha jadada batun amfanin da Chloroquine a matsayin maganin cutar korona, inda har ya kai ga yana cewa zai gwada shan maganin da kansa.

    Dr, Bright ya ce yayin da yake nazari ta kowanne fanni, ya ki amince wa a yi wa Amurkawa maganin da babu sahalewar kwararru kamar yadda gwamnatin Trump ta dage a kai ko take ganin shi ne mafita.

  11. Coronavirus: Yanayin da ake ciki a California

    California governor

    Asalin hoton, Getty Images

    Jami'ai a California sun ce mutuwar farko sakamakon Covid-19 a Amurka ta faru ne tun a farkon watan Fabarairu.

    Kusan mako uku kenan, kafin Amurka ta sanar da cewa ta samu mutum na farko da ya mutu a jihar Washington.

    Jami'ar lafiyar gundumar Santa Clara, Sara Cody, ta ce mutuwar wannan mata a ranar 6 ga watan Fabarairu watakil ba shi ne kawai mutuwar da ake kuskuren tunanin mura ba ce - sannan ana ta samun yaduwar cutar tsakanin al'umma tun kafin lokacin da aka yi tunani a baya.

    Gwamnan California, Gavin Newsom, ya umarci a binciki mace-mace da suka auku tun daga watan Disambar bara, watakil a samu mai alaka da cutar korona.

    Adadin mamata sakamkon wannan cuta ya rubanya a cikin mako guda, inda ya zarfe dubu 46.

  12. Coronavirus: Kwararru na bincike kan ko sinadarin Nicotine ka iya zama garkuwa

    Kwararu a fanin kimiya a Faransa na bincike kan ko amfani da Nicotine zai taimaka wajen kare mutane daga cutar korona.

    Sun kadammar da binciken ne bayan kididdiga daga asibitin Paris ta nuna masu shan sigari ba su fiya kwanciya idan sun kamu da cutar ba.

    Daraktan hukumar lafiya ta Faransa, Jerome Salomon, ya ce bayanan akwai abin mamaki a ciki, sannan ya bukaci a zurfafa bincike.

    Sai dai masanan sun jadada cewa la'akari da hadarin shan sigari, ba zai yiwu mutane su rungumi zukar sigari ba, amma za su yi amfani da sinadarin nicotine da ke ciki a bincikensu.

  13. Shugabannin Tarayyar EU za su bayar da tallafi ga kasashen da korona ta fi yi wa illa

    EU Leaders

    Asalin hoton, Getty Images

    Ana saran shugabanni kungiyar Tarayyar Turai za su sanya hannu a shirin tallafa wa kasashen da cutar korona ta fi yi wa illa, a wani taron da za su gudanar ta bidiyo nan gaba kadan.

    Wakiliyar BBC ta ce ana kuma saran za su cimma matsaya guda wajen daukan matakan soma sassauta dokar hana fita a kasashensu.

    Tallafin ceton na euro biliyan sama da 500, ta amince da shirin ne bayan muhawarar da aka tafka tsakanin kasashe masu arziki da ke arewaci na Tarayyar EU, da wadanda tattalin arzikinsu ke da rauni a kudanci da wannan annoba ta fi kassarawa

  14. Farawa

    Coronavirus

    Asalin hoton, Getty Images

    Masu bibiyarmu barkan ku da warhaka. Ya ya muka ji da darurar annobar korona? Allah ya kare mu baki daya sannan wadanda suka rasu kuma Allah ya jikan su. Da fatan yau ma za ku ci gaba da kasancewa da shafin bbchausa.com domin samun labarai kai tsaye sannan kuma da dumi-duminsu kan annobar ta korona. Mun gode.