Rüdiger zai taimaka wa 'yan kasuwar Saliyo da abin rufe fuska
Dan wasan bayan Chelsea Antonio Rüdiger ya kaddamar da wata gidauniya ta tara kudi domin saya wa 'yan kasuwa takunkumin rufe fuska a kasar Saliyo wato Sierra Leone.
Rüdiger ya ce yana fatan za su kare su sannan su dakile yaduwar cutar ta korona.
Ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa gidauniyar tasa za ta yi hadin gwiwa da gidauniyar Mary-Ann Kaikai da kuma Lunchbox Gift domin samar da takunkumi 60,000.
Rüdiger wanda iyayensa 'yan Saliyo ne, ya kuma roki abokan wasansa na Premier League da su tara $30,000 (kusan naira miliyan 11).
Ya kuma gode wa Mesut Özil da N'Golo Kanté da Callum Hudson-Odoi da Olivier Giroud bisa taimakon da suka bayar.