Gwamnan Jihar Filato Simon Lalong ya sassauta dokar hana fita a jihar na tsawon kwana uku, wadda aka saka domin dakile yaduwar cutar korona.
Gwamnan ya bayyana haka ne a wani jawabi da ya yi wa al'ummar jihar ranar Alhamis, inda aka bai wa jama'a damar fita daga karfe 12:00 na daren Alhamis 23 ga watan Afrilu zuwa Lahadi 26.
Kazalika gwamnan ya ce an kama tare da gurfanar da mutum 769 da suka karya dokar, inda jumillarsu ya kama 1,607. An gano su ne ta hanyar kafa kyamarorin tsaro, in ji gwamnan.
Ya kara da cewa nan gaba kadan za a sanar da al'ummar jihar lokacin da za a tsawaita dokar, a ci gaba da yaki da yaduwar cutar.
An yi wa mutum 231 gwajin cutar korona sannan aka killace 221, yayin da aka sallami 33 daga cibiyar killacewar, a cewar gwamnan.
Hakan yana nufin har zuwa lokacin hada wannan rahoto, ba a samu mai dauke da cutar ba a Jihar Filato.