Ba za mu lamunci 'wariyar launin fata' daga China ba – Najeriya
Wannan shafi na kawo muku bayanai kai tsaye dangane da annobar korona da ke ci gaba da yaduwa a fadin duniya.
Rahoto kai-tsaye
Usman Minjibir and Umar Mikail
Karshen rahotannin kenan a wannan shafin
Jama'a Umar Mikail ne ya kasance da ku tun daga karfe 4:00 na yamma agogon Nijar da Najeriya, kuma karshen rahotannin na kai-tsaye kenan.
Kafin mu sake haduwa gobe Juma'a idan Allah ya kai mu, za ku iya ci gaba da warkajami a babban shafinmu ko kuma ku yi kasa kawai domin karanta abubuwan da suka faru a duniya a yau.
Da fatan za a yi sahur lafiya ga masu azumi. Mu zama lafiya.
Jawabin Sarkin Musulmin Najeriya
Ku kalli jawabin Sarkin Musulmin Najeriya, Muhammad Sa'ad Abubakar III game da ganin Watan Azumin Ramadana na Shekarar Hijira 1441, daidai da Shekarar Miladiyya 2020.
Bayanan bidiyo, Jawabin ganin watan Ramadana daga Sarkin Musulmi Sa'ad Abubakar III
Labarai da dumi-dumi, An ga watan Azumin Ramadana a Najeriya
Sarkin Musulmi Muhammad Sa'ad Abubakar III ya sanar da ganin watan Azumin watan Ramadana a Najeriya.
"Gobe Juma'a 24 ga watan Afrilu ce 1 ga watan Ramadana," in ji shi, a jawabin ganin watan kai-tsaye a fadarsa da ke Jihar Sokoto a arewa maso yammacin Najeriya.
Ba za mu lamunci 'wariyar launin fata' ba daga China – Najeriya
Asalin hoton, @GeoffreyOnyeama
Bayanan hoto, Geoffrey Onyeama ya ce Najeriya ba za ta lamunci kowacce irin wariya ba
Gwamnatin Najeriya ta ce ba za ta lamunci "wariyar launin fata ba" da ake nuna wa 'yan Najeriya a kasar China sakamakon matakan da ake dauka na yaki da cutar korona.
Ministan Harkokin Wajen Najeriya Geoffrey Onyeama ne ya bayyana hakan ranar Alhamis a wurin taron manema labarai da kwamitin yaki da cutar korona ke gabatarwa kullum a Abuja, babban birnin kasar.
"Mun jaddada karara ga China cewa ba za mu taba lamuntar wariyar launin fata ba da ake nuna wa 'yan Najeriya da sauran bakaken fata," a cewar ministan. Ya kara da cewa "wannan makura ce a gare mu".
A 'yan kwanakin nan ne rahotanni suka fara bayyana cewa hukumomi a China na fitar da bakaken fata 'yan Afirka daga gidajensu da otel-otel domin tsare su a cibiyoyin killace masu korona duk da cewa ba sa dauke da cutar.
Lamarin ya fi kamari a birnin Guangzhou da ake hadahadar kasuwnci. Dubban 'yan Afirka ne ke sayo kaya daga birnin zuwa kasashensu.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.
Karshen labarin da aka sa a X
An gwada allurar rigakafin korona a kan mutum biyu
An fara yi wa mutane gwajin cutar korona a Oxford da ke Birtaniya.
An fara yi wa wasu mutum biyu 'yan sa-kai allurar, wadanda su ne na farko a cikin mutum 800 da aka zaba domin yin gwajin.
Sai dai rabinsu za a yi wa allurar korona, rabi kuma a yi musu wadda ke bayar da kariya daga cutar sankarau, ba korona ba.
Wadanda aka yi a kansu ba za su san wacce allurar daga ciki aka yi musu ba amma likitocin za su sani.
Ma'aikatan lafiya 40 ne suka kamu da korona a Najeriya
Asalin hoton, Getty Images
Ministan Lafiya a Najeriya, Dr Osagie Ehanire ya ce ma'aikatan lafiya kusan 40 ne suka kamu da cutar korona a kasar, yayin da suke aikin kula da masu cutar.
Dr Ehanire ya bayyana haka ne ranar Alhamis a wurin taron manema labarai da kwamitin yaki da korona ke gudanarwa kullum kan irin matakan da ake dauka na yaki da cutar.
Saboda haka ya roki ma'aikatan lafiyar da su tabbata sun kare kansu a lokacin da suke kula da masu cutar a kodayaushe.
Ya ce: "Ina yaba wa dukkan ma'aikatan lafiyarmu da ke kan gaba a yaki da annobar korona, gwamnati za ta ci gaba da taikmaka muku da duk kayan aikin da ake bukata na kare kai."
Ministan ya ce an samu karin mutum 91 da suka harbu da cutar ya zuwa daren Laraba. Ya kuma alakanta hakan da karuwar yawan adadin mutanen da ake yi wa gwajin a kullum.
Ya ce duk da cewa cibiyoyin lafiya a Najeriya suna iya gwada mutum 1,000 ne a kullum, mutum 600 ne kawai ake samu domin yi wa gwajin.
Masu neman tallafi na marasa aikin yi a Amurka sun kai miliyan 26.4
Asalin hoton, EPA
Wasu Amurkawa miliyan 4.4 ne suka nemi a ba su tallafin da ake bai wa marasa aikin yi a makon da ya gabata, yayin da annobar korona ke ci gaba da lalata tattalin arzikin mutane.
Sabbin alkaluman sun sa jumillar adadin ya zama miliyan 26.4 tun daga tsakiyar watan Maris - kashi 15 cikin 100 kenan na ma'aikatan Amurka baki daya.
Sai dai bayanan baya-bayan nan sun nuna cewa adadin yana raguwa a cikin mako uku a jere, abin da ke kara karfin gwiwar cewa fargabar rashin aikin yin ta kusa zuwa karshe.
Za a yi wa 'yan sanda 8,000 gwajin korona a Ghana
Asalin hoton, AFP
Bayanan hoto, Jami'an tsaro fiye da 30,000 aka tura sassa daban-daban na Ghana domin tabbatar da dokar hana fita
'Yan sanda fiye da mutum 8,000 ne da aka tura su sassan kasar domin tabbatar da dokar hana fita za a yi wa gwajin cutar korona.
An sassauta dokar da aka yi tsawon mako uku ana ciki a ranar Alhamis, wadda Shugaba Akufo-Addo ya saka.
Sai dai har yanzu makarantu za su ci gaba da kasancewa a rufe, haramcin taruka nan sannan kuma iyakokin kasar na kulle.
A jimlace, jami'an tsaro fiye da 30,000 ne aka tura sassa daban-daban domin tabbatar da dokar a kasar.
An sassuta dokar hana fita a Filato, har yanzu babu korona a jihar
Asalin hoton, @PLSGov
Gwamnan Jihar Filato Simon Lalong ya sassauta dokar hana fita a jihar na tsawon kwana uku, wadda aka saka domin dakile yaduwar cutar korona.
Gwamnan ya bayyana haka ne a wani jawabi da ya yi wa al'ummar jihar ranar Alhamis, inda aka bai wa jama'a damar fita daga karfe 12:00 na daren Alhamis 23 ga watan Afrilu zuwa Lahadi 26.
Kazalika gwamnan ya ce an kama tare da gurfanar da mutum 769 da suka karya dokar, inda jumillarsu ya kama 1,607. An gano su ne ta hanyar kafa kyamarorin tsaro, in ji gwamnan.
Ya kara da cewa nan gaba kadan za a sanar da al'ummar jihar lokacin da za a tsawaita dokar, a ci gaba da yaki da yaduwar cutar.
An yi wa mutum 231 gwajin cutar korona sannan aka killace 221, yayin da aka sallami 33 daga cibiyar killacewar, a cewar gwamnan.
Hakan yana nufin har zuwa lokacin hada wannan rahoto, ba a samu mai dauke da cutar ba a Jihar Filato.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.
Karshen labarin da aka sa a X
An nada Buhari jagoran yaki da cutar korona
Asalin hoton, Nigeria Presidency
Shugabannin kasashe mambobin kungiyar Habaka Tattalin Arzikin Afirka ta Yamma, ECOWAS sun nada Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya a matsayin jagoran yaki da cutar korona a yankin.
An zabe shi ne a ranar Alhamis a wani taro da suka gudanar ta bidiyo karkashin jagorancin Shugaban Nijar kuma shugaban kungiyar Mahamadou Issoufou, kamar yadda fadar shugaban ta bayyana a shafinta na Twitter.
Buhari zai jagoranci bullowa tare da aiwatar da dukkanin matakan da za a dauka kan yaki da cutar a yankin da ya kunshi kasashe 15, ciki har da Najeriya da Nijar da Ghana da Gambia da Mali da Senegal da Saliyo.
Sauran sun hada da Benin da Ivory Coast da Liberia da Cape Verde da Togo da Burkina Faso da Guinea da Guinea Bissau.
"A cikin kowanne irin yanayi kamar wannan, akwai damarmaki," in ji Shugaba Buhari.
"Saboda haka wajibi ne mu nemo wadannan damarmaki da wannan yanayin maras dadi zai ba mu ta hanyar aiwatar da matakai, wadanda kafin yanzu, zai yi wuya mu iya daukarsu."
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.
Karshen labarin da aka sa a X
Labarai da dumi-dumi, An ga watan Azumin Ramadana a Saudiyya
Kasar Saudiyya ta bayar da sanarwar ganin watan azumin Ramadana.
Shafin Facebook na Masallacin Harami ne ya bayyana hakan a wani sako da ya wallafa, tare da nuna sallar Magariba kai-tsaye daga masallacin.
Labarai da dumi-dumi, Karin mutum 616 sun mutu a Birtaniya
Jumillar mutum 18,738 ne suka mutu a asibitocin Birtaniya sakamakon annobar cutar korona ya zuwa karfe 5:00 na yammacin Laraba, a cewar Sashen Lafiya na kasar.
Adadin ya kai haka ne bayan an samu karin mutum 616 da suka mutu a rana kafin wancan.
Sai dai adadin bai hadar da na wadanda suka mutu a unguwanni da gidajen gajiyayyu ba.
Coronavirus: China ta musanta zargin yin rufa-rufa
Asalin hoton, Getty Images
Jakadan China a London, ya bayyana zargin da ake yi wa kasarsa na yin rufa-rufa a kan cutar korona a matsayin kanzon kurege.
Liu Xiaoming ya ce China ta rika yin komi a fili tun farkon barkewar annobar, don haka zargin da ake musu ba shi da tushe.
Wakilin BBC ya ce Ambasadan ya ce China, ta bayar da tallafin fan miliyan 50 ga Hukumar Lafiya ta Duniya don yaki da cutar bayan barkewarta.
Shugaban Amurka Donald Trump ya sha sukar China kan barkewar cutar da ta samo asali daga birnin Wuhan, inda yanzu haka Amurka na shirin gabatar da China a gaban kotu saboda yadda take tafiyar da cutar.
Coronavirus: Za a ci gaba da buga gasar Bundesliga
Shugaban hukumar shirya gasar cin kofin kwallon kafa ta Jamus, ya ce hukumar a shirye take don ci gaba da buga gasar Bundesliga bayan da cutar korona ta tilasta dakatar da ita.
Akwai bukatar gwamnatin Jamus da gwamnatocin jihohi 16 su amince da bukatar ci gaba da wasannin a ranar 9 ga watan Mayu kamar yadda hukumar ta nema a yi.
Idan har aka amince, za a rika yi wa 'yan wasa gwajin cutar kafin su shiga fili, sannan za a rika yin wasanni ba tare da 'yan kallo ba.
Yanzu zai zamanto gasar Bundesliga ce ta farko da a ka ci gaba da gudanarwa a Turai bayan dakatar da ita saboda cutar korona.
Coronavirus: Tattalin arzikin Turai na durkushewa
Asalin hoton, Getty Images
Wani bincike kan harkokin kasuwanci a Turai ya nuna yadda tattalin arzikin nahiyar ke durkushewa sannu a hankali a wannan lokaci na annobar korona.
Sakamakon biciken a kasashen da ke amfani da nauin kudi na Euro da kuma Birtaniya a wannan watan kadai, ya nuna cewa al’amura sun yi muni fiye da yadda aka yi hasashe tun da farko.
Kana an samu rasa ayyukan da ba a taba gani ba, tun bayan aiwatar da irin wannan bincike a shekarun 1990.
Bangarorin masana'antu da na ayyukan yau da kullum sun gamu da durkushewar da ba a taba tsammani ba.
Yawancin manajojin kamfanonin kasuwanci da suka tofa albarkacin bakinsu a kan wannan bincike sun dora alhakin tabarbarewar al'amura a kan cutar korona, da kuma dokar zaman gida da aka kakaba a kasashe daban-daban da ke Turan.
Mutum 1,158 sun kamu da cutar korona a kwana daya a Saudiyya
Kasar saudiyya ta samu mutum 1,158 da ke dauke da cutar korona a kwana daya, inda yanzu haka take da masu cutar 13,930, in ji ma'aikatar Lafiyar kasar.
Ma'aikatar ta sanar da samun mutum 7 da suka mutu sannan 113 sun warke.
Yanzu kenan mutum 121 ne suka mutu sannan 1,925.
Covid-19: Gwamnonin Najeriya za su rufe iyakokin jihohin kasar 36
Asalin hoton, Twitter
Kungiyar gwamnonin Najeriya ta amince da rufe iyakokin jihohin 36 domin hana zirga-zirga a tsakanin jihohin na mako biyu, a wani mataki na dakile bazuwar cutar korona a kasar.
Najeriya dai na da mutum 873 da ke dauke da cutar ta korona inda mutum 28 suka mutu.
A wata ganawa da suka ta kafar intanet, gwamnonin sun nemi gwamnatin tarayya da ta sakar musu al'amarin yaki da annobar Covid-19.
Gwamnonin dai da ra'ayin cewa barin iyakokin jihohi ne ke kara ta'azzara yaduwar cutar a kasar.
Yanzu dai abin da ya rage shi ne ko Shugaba Buhari zai sa dokar kulle a baki daya jihohin kasar, ba kawai jihohin Legas da Ogun da kuma birnin Abuja.
Hukumar Lafiya ta Duniya ta yi gargadin cewa yawan wadanda ke mutuwa
saboda zazzabin cizon sauro a kasashen da ke kudu da hamadar sahara na iya
ninkawa a wannan shekara da ake fama da annobar korona.
Binciken da WHO ta yi ya nuna
kusan mutum dubu 760 a yankin na iya mutuwa sakamakon cutar
da ke da alaka da cizon sauro a wannan shekara kadai.
Hukumar ta ce rufe iyakoki da hana zirga-zirga da aka yi a wasu kasashe don dakile yaduwar korona na
iya kawo cikas ga samar da magunguna da raba maganin kashe kwari da gidajen
sauro da kan taimaka wajen hana kamuwa da cutar.
A don haka ne ma hukumar ke
kira da babbar murya ga kasashen da ke kudu da hamadar sahara su kara zage
dantse wajen raba irin wadannan kayayyaki ga jama’a don kare lafiyarsu.
Kasashe da ke hamadar sahara sun hada da Najeriya da Jamhuriyar Nijar da Kamaru da Ghana da Sudan.
Coronavirus: Asusun Lamuni na Duniya zai bai wa Congo $363m
Asalin hoton, Getty Images
Asusun Lamuni na Duniya, IMF ya amince da bai wa jmahuriyar Dimokradiyyar Kongo tallafin dala milyan 363 domin yakar cutar korona.
Asusun ya ce ya yi hakan ne saboda 'irin kaduwar da' Congo ta yi sakamakon cutar ta korona.
Jmahuriyar Dimokradiyar Kongo dai ita ce gaba-gaba wajen samar da sinadarin wayoyi da motoci masu amfani da lantarki.
To sai dai duk da albarkatun kasar, 'yan kasar na fama da kangin talauci inda suka yi shura a nahiyar Afirka.
Kawo yanzu dai Jmahuriyar Kongo na da mutum 350 da ke dauke da cutar korona inda 25 suka mutu.
Labarai da dumi-dumi, Rabin wadanda suka mutu a Turai 'yan gidan gajiyayyu
Kusan rabin wadanda cutar korona ta yi ajalinsu a Nahiyar Turai mazauna gidajen kulawa da gajiyayyu ne, a cewar shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya a nahiyar.
Dr Hans Kluge ya fada wa wani taron manema labarai ranar Ahamis cewa akwai "damuwa matuka" a kan wadanda ke zaune a gidajen gajiyayyu na tsawon lokaci.
Ya ce: "Bisa ga bayanai daga kasashen Turai, kusan rabin wadanda suka mutu sakamakon cutar korona mazauna gidajen kula da gajiyayyu ne da ke zaune na tsawon lokaci. Wannan bala'i ne ga 'yan Adam baki daya."