An sassauta dokar hana fita a Kano don Azumi

Wannan shafi na kawo muku bayanai kai tsaye dangane da annobar korona da ke ci gaba da yi wa duniya fyadar 'ya'yan kadanya.

Rahoto kai-tsaye

Usman Minjibir, Umar Mikail and Awwal Ahmad Janyau

  1. Adadin masu cutar korona a Najeriya ya kai 782 - NCDC

    Hukumar dakile cutuka masu yaduwa ta Najeriya ta ce an samu karin mutum 117 da suka sake kamuwa da cutar korona cikin sa'a 24 da ta wuce a kasar.

    Don haka adadin masu fama da cutar a kasar ya kai 782 a daren Talata, kimanin wata biyu da bullar cutar Najeriya.

    Fiye da rabi na sabbin alkaluman wadanda suka kamu, suna cikin jihar Legas a cewar alkaluman hukumar NCDC. Sai Abuja mai mutum 29, inda jihar Kano ta biye musu da mutum 14.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  2. Covid-19: Halin da ake ciki a Spaniya kan hana zirga-zirga

    Spain

    Asalin hoton, Getty Images

    Yau ne majalisar dokokin Spaniya za ta yanke shawara kan tsawaita matakin zaman gida, ba shiga ba fita da aka sanya tun tsakiyar watan Maris da mako biyu.

    Spaniya daya ce daga cikin kasashen da ke da yawan masu cutar korona a duniya baya ga Amurka. Kuma kimanin mutane sama da dubu ashirin da daya ne suka mutu.

    Sai dai yawan mace-macen da ake samu a rana daya na raguwa a 'yan makwannin nan. A makon da ya gabata, an bar wasu masana'antu komawa aiki.

  3. Coronavirus: Za a sassauta dokar kulle a Congo

    Ana dab da fara sassauta matakan kulle a jamhuriyar dimokradiyyar Congo yau Laraba a Kinshasa, babban birnin kasar inda cutar ta fi kamari a kasar.

    Sai dai hukumomi sun ce za a bar mazauna yankin fita daga gidajensu.

    Wakilin BBC ya ce a tsukin lokacin zaman gidan kadai an iya gano masu cutar korona har 30 tare da bibiyar kashi tamanin na wadanda suka yi mu'amala da masu cutar.

    Bankuna da wuraren sayar da abinci da wasu harkokin kasuwancin za su sake budewa amma sassaucin bai shafi mutanen da ke cikin unguwannin da ke da cunkoso ba.

    Mutum 350 ne suka kamu da cutar korona sannan mutum 25 sun mutu amma ana fargabar cewa sai hukumomin lafiya sun yi da gaske wajen yaki da bazuwar cutar.

  4. Covid-19: Farashin mai a Turai da Amurka na ci gaba da yin warwas

    Oil price

    Asalin hoton, Getty Images

    Kasuwannin man Amurka da Turai na ci gaba da fuskantar koma baya yayin da annobar korona ta janyo raguwar bukatar man.

    Man Amurka West Texas Intermediate ya fadi kasa warwas kafin ya farfado idan aka bude kasuwannin Asia.

    Farashin man Turai, Brent shi ma ya fuskanci irin wannan faduwar a karon farko cikin kusan shekara ashirin. Ana fargaba kan rashin wuraren ajiyar danyen man.

    Sai dai Shugaba Trump ya sha alwashin samar da wasu kudade domin agazawa man kasar da ma masu samar da iskar gas.

  5. 'Cutar korona ka iya yaduwa idan lokacin mura ya zo'

    Coronavirus

    Asalin hoton, Getty Images

    Wani kwararre a fannin cutuka a Amurka ya ce karin masu dauke da cutar korona na iya kazanta kan yawan mutanen da suka kamu a yanzu saboda zai zo daidai da lokacin mura.

    Robert Redfield, daraktan cibiyar dakile da kare yaduwar cutuka ta Amurka ya yi gargadin daidai lokacin da wasu jihohin kasar ke shirye-shiryen bude harkokin kasuwancinsu.

    Ya ce samun barkewar nau'in cutukan numfashi biyu na kara yin barazana ga tsarin lafiyar Amurka.

    Dakta Redfield ya kara da cewa kamata ya yi a yi amfani da watannin da ke tafe wajen shiryawa abubuwan da za su gabato sannan kuma dole ne a ci gaba da ba da tazara.

    A jiya Talata ne, kididdiga daga jami'ar Johns Hopkins ta nuna cewa sama da Amurkawa dubu biyu da dari bakwai sun mutu sanadin covid-19 cikin sama da kwana daya - daya daga cikin rashe-rashe mafi muni da aka taba yi a kasar.

  6. Zan dakatar da baki daga shiga Amurka na dan lokaci - Trump

    Trump

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaba Trump ya ce zai dakatar da bakin da suke neman takardar izinin zama a kasar shiga Amurka na wani dan lokaci, matakin da ya ce zai kare ayyukan Amurkawa yayin da ake yaki da annobar korona.

    A wani jawabi da ya yi a fadar White House , Mista Trump ya ce ba daidai bane Amurkawan da suka mutu sanadin annobar a maye gurabensu da bakin da suka shiga Amurka daga wata kasar.

    BBC ta rawaito cewa haramcin na tsawon kwana sittin ne bayan nan kuma za a kara nazari a kai la'akari da halin da tattalin arziki yake ciki a lokacin Trump din dai yana magana ne kwana daya bayan ya wallafa wani sako a Twitter cewa zai dakatar da shiga kasar.

    'Yan jam'iyyar Demokrat dai sun nuna basu ji dadin lamarin ba inda a ranar Litinin suka zargi shugaban kasar da kokarin karkatar da hankulan mutane daga yadda Trump din ke yaki da bazuwar korona.

  7. Coronavirus: 'Zai wuya a bai wa 'yan Najeriya wutar lantarki kyauta'

    Electiricity

    Asalin hoton, Getty Images

    Ministan wuta na Najeriya, Saleh Mamman ya ce batun da ake yi na yiwuwar bai wa 'yan kasar wutar lantarki kyauta har tsawon wata biyu saboda dokar hana fita a Najeriya ba abu ne mai yiwuwa ba.

    Ministan ya shaida wa BBC cewa "A duk wata kamfanonin wutar na karbar naira bilyan 50 daga hannun jama'a saboda haka gwamnati ba za ta iya biyan na wata biyu ba wato naira bilyan 100."

    Ya kara da cewa "'Yan Najeriya suna suka tara domin akwai masu halin da ke zaune a Maitama da Asokoro sannan kuma akwai talakawa a kauyuka saboda haka wa za a bai wa wa za a hana?"

    'Yan majalisar Najeriya ne dai suka nemi da a bai wa 'yan kasar damar shan wuta kyauta har ta tsawon wata biyu domin samun sukunin zaman gida yayin da gwamnati ta sa dokar hana zirga-zirga.

  8. Farawa

    Masu bibiyarmu barkanku da warhaka. Barka da sake saduwa a shafinmu da ke kawo muku labarai kai tsaye bisa irin wainar da ake toyawa a sassan duniya dangane da annobar korona. Da fatan za ku kasance da mu a koyaushe.