Za a kaddamar gwajin cutar korona a New York

Asalin hoton, Getty Images
Gwamnan New York Andrew Cuomo ya ce zai kaddamar da shirin gwajin cutar korona a mako mai zuwa domin gano yawan mutanen da suka kamu da cutar a jihar.
Mista Cuomo ya bayyana cewa hukumar kula da abinci da magunguna ta kasar ta amince da hakan.
A hannu guda kuma, Shugaba Trump ya ce yana shirin yin amfani da wata doka domin samar da tsinken gwada samfurin mutum a wani asibiti da ke kasar.
Gwamnonin akasarin jihohin Amurka sun nemi gwamnatin tarayya ta taimaka wajen samar da wadatattun kayayyaki.
Adadin mutanen da suka mutu a Amurka sanadiyyar kwayar cutar ya karu da kusan dubu biyu jiya Lahadi - mutum sama da dubu arba'in da biyu kenan sun mutu a Amurka jimilla kuma New York ce ke da kusan rabin mutanen.

