Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Tambuwal ya hana mahaifin Rahamaniyya shiga Sokoto

Wannan shafin na kawo muku abubuwan da ke faruwa a duniya baki daya dangane da annobar coronavirus.

Rahoto kai-tsaye

Usman Minjibir, Awwal Ahmad Janyau, Umar Mikail and Buhari Muhammad Fagge

  1. Za a kaddamar gwajin cutar korona a New York

    Gwamnan New York Andrew Cuomo ya ce zai kaddamar da shirin gwajin cutar korona a mako mai zuwa domin gano yawan mutanen da suka kamu da cutar a jihar.

    Mista Cuomo ya bayyana cewa hukumar kula da abinci da magunguna ta kasar ta amince da hakan.

    A hannu guda kuma, Shugaba Trump ya ce yana shirin yin amfani da wata doka domin samar da tsinken gwada samfurin mutum a wani asibiti da ke kasar.

    Gwamnonin akasarin jihohin Amurka sun nemi gwamnatin tarayya ta taimaka wajen samar da wadatattun kayayyaki.

    Adadin mutanen da suka mutu a Amurka sanadiyyar kwayar cutar ya karu da kusan dubu biyu jiya Lahadi - mutum sama da dubu arba'in da biyu kenan sun mutu a Amurka jimilla kuma New York ce ke da kusan rabin mutanen.

  2. Coronavirus: Burtaniya za ta fara amfani da jinin masu cutar domin waraka

    Burtaniya na kokarin ganin ta yi amfani da samfirin jinin mutanen da suka warke daga cutar korona a matsayin magani ga mutanen da suka kamu da cutar.

    Hukumar Insorar Lafiyar Burtaniya na son ganin mutanen da suka warke daga cutar da su bayar da gudunmowar jininsu domin yin gwaji.

    Ana fatan sinadaran kariya da suka yaki cutar a jikin mutanen da suka warke ka iya taimaka wa wajen gusar da kwayar cutar.

    Tuni dai aka fara aiwatar da nazarin samun maganin cutar, inda fiye da asibitoci 1500 ke cikin shirin a Amurka.

  3. Coronavirus: Yadda za a yi sallolin watan Ramadan a Pakistan

    Bayan matsin lamba daga malaman addini a kasar Pakistan, gwamnatin kasar ta amince a gudanar da salloli a jam'i a watan ramadan mai kamawa duk da irin damuwar da ake da ita dangane da cutar korona.

    To sai dai gwamnatin da malaman na addini sun cimma yarjejeniya cewa ba za a bar mutanen da suka wuce shekara 50 da haihuwa ba da kananan yara da kuma masu alamun mura shiga cikin jama'a ba.

    Har wa yau, an amince cewa za a cire duk wata shimfida kuma dole a rinka goge masallacin da sindaran wankje wuri a kai a kai.

    Gwamnatin ta yi gargadin cewa da zarar an karya doka duk kankantarta to za ta rufe masallatan ne. Sannan kuma idan aka samu karin masu cutar korona to gwamnati na da damar sauya matsaya kan barin taruwar jama'a.

  4. Budewa

    Masu bibiyarmu barkan ku da wannan safiya a a cikin wannan shiri da muke kawo bayanai kai tsaye dangane da halin da ake ciki a kan annobar korona da ta zama ruwan dare dama duniya. Da fatan za ku kasance da mu. Madalla!