Adadin masu cutar korona a Sipaniya ya yi kasa
Adadin wadanda ke mutuwa saboda cutar korona a Spaniya ya yi kasa da dari hudu, a karon farko tun bayan da Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana ta a matsayin annoba a ranar 11 ga watan Maris.
Wannan dai ita ce rana ta biyu da adadin ke ci gaba da raguwa a jere, bayan da yawan wadanda suka mutu a kasar ya zarta 20,000 tun bayan barkewar cutar.
Da yake jawabi ga taron manema labarai, babban jami'in lafiya na Spaniya Fernando Simon, ya ce alkalumman sun kara musu kwarin guiwa.
Ya ce "yau a karon farko cikin lokaci mai tsawo, an samu mutane 399 da suka mutu, wadannan alkalumma sun ba mu kwarin guiwa, duk da yake ba abu ne mai dadi kulluyaumin a rika zancen wadanda suka mutu ba."
A gefe guda babban bankin Spaniya ya ce tattalin arzikin kasar ya yi kasa da kaso biyar a watanni hudu na farkon wannan shekara.