Karshen rahotannin kenan a wannan shafi
Jama'a rahotannin namu na kai-tsaye sun zo karshe a wannan rana.
Umar Mikail ke cewa sai kuma gobe idan Allah ya kai mu.
Mu kwana lafiya daga Sashen Hausa na BBC.
Wannan shafin na kawo muku abubuwan da ke faruwa a duniya baki daya dangane da annobar coronavirus.
Usman Minjibir, Awwal Ahmad Janyau, Umar Mikail and Buhari Muhammad Fagge
Jama'a rahotannin namu na kai-tsaye sun zo karshe a wannan rana.
Umar Mikail ke cewa sai kuma gobe idan Allah ya kai mu.
Mu kwana lafiya daga Sashen Hausa na BBC.

Asalin hoton, @AWTambuwal
Gwamnan jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal ya haramtawa Alhaji Musa Bashir mahaifin mai kamfanin man fetir na Rahamaniyya shiga Sokoto saboda cutar koronavirus.
Gwamnan Tambuwal ya shaidawa manema labarai cewa sun ji labarin daya daga cikin ‘ya’yansa gwaji ya tabbatar da yana dauke da cutar korona.
Gwamnan ya ce ya yi magana da shi har sau biyu, “amma ya nuna min yana kan hanya sai ya shigo Sokoto, kuma na ba da umurni a mayar da shi, saboda a cikin iyalin shi akwai mai dauke da cutar Kuma shi ba a yi mashi gwaji ba.”
“Wadanda ke hulda da Alhaji Musa Bashar da ake kira Rahamaniyya su yi magana da shi kada ya kuskura ya shigo Sokoto,” in ji Gwamna Tambuwal.
Sai dai duk da zargin da gwamna Tambuwal ya yi bai bayar da cikakken bayani ba kan hukumar da ta tabbatar masa da cewa daya daga cikin 'ya'yan Alhaji Musa Bashir na dauke da cutar.
Amma Gwamna Tambuwal ya ce zai dauki duk matakin da ya dace domin kare al’ummar jihar Sokoto idan har ya yi watsi da shawarar da aka ba shi.
Cutar korona na ci gaba da yaduwa a jihohin Najeriya, amma har yanzu cutar ba ta tsallaka jihar Sokoto ba.
Tuni gwamnatin Jihar ta dauki matakan dakile cutar daga jihar ta hanyar rufe iyakokinta.
Wasu al'ummar jihar kuma tuni suka fara barazana ga Alhaji Musa Bashir, kan za su dauki mataki akansa idan har ya taka kafarsa cikin Sokoto.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X

Asalin hoton, Prseidency Nigeria
Shugaban kwamitin yaki da cutar korona a Najeriya, Mista Boss Mustapha, ya nemi afuwa saboda saba ka’idojin da aka yi wurin binne marigayi Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, Abba Kyari a ranar Asabar.
Mista Mustapha ya ce abin takaici ne yadda ba a bayar da tazara ba a wajen jana’izar.
Ya nemi afuwar ne a lokacin da kwamitinsa ke bayar da bayanai kan ayyukan da suke yi wajen kawar da korona a Najeriya, yayin wani taron manema labarai na kullum da suke yi a Abuja.
Mutane da dama ne suka halarci jana’izar marigayi Abba Kyari a ranar Asabar, wanda ya rasu sakamakon cutar korona a ranar Juma’a a Jihar Legas.
Yadda aka yi cincirundo ya sa mutane da dama suka soki jami’an gwamnati da suka ki bin dokar ba da tazara da aka kafa domin rage yaduwar cutar korona a Najeriya.
Shugaba Buhari ya gode wa wadanda suka taya shi alhinin rasuwar ta hanyar kiran waya da turo sakonni sannan ya yaba musu bisa bin umarnin guje wa tarukan zaman karbar gaisuwa.

Asalin hoton, Reuters
Dubban 'yan Isra'ila ne suka shirya wata zanga-zangar kin jini salon shugabancin Firaminista Benjamin Netanyahu mai cike da bayar da tazara don guje wa kamuwa da annobar cutar korona.
Sanye da takunkumin rufe fuska, dauke da kwalaye, masu zanga-zangar sun taru a daren Lahadi a Dandalin Rabin da ke birnin Tel Aviv, inda suka bayar da tazarar mita biyu (kafa 6) a tsakaninsu.
Siun yi Allah-wadai da abin da suka kira matakan da suka saba wa dimokuradiyya da shugaban yake dauka kan annobar korona.
An dora wa majalisar Isra'ila alhakin kafa gwamnatin hadaka bayan an gudanar da zabuka har sau uku ba tare da samun wanda ya yi nasara ba, abin da ya jefa kasar cikin rikiicin siyasa.

Asalin hoton, Reuters

Asalin hoton, Reuters
Yayin yake da yake gabatar wani jawabi cikin damuwa kan matakin da Amurka ta dauka, Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya WHO, Tedros Adhanom Ghebreyesus ya jaddada cewa hukumar ba ta da wani bayani da ta boye kan kowacce kasa game da cutar korona.
Shugaban Amurka Donald Trump ya soki yadda WHO ta tunkari annobar, kuma ya dakatar da taimakaon da kasarsa ke bai wa hukumar a makon jiya, yana cewa ta gaza shawo kan annobar yadda ya kamata kuma ta nuna amincewar da ta wuce kima kan China.
Dakta Tedros ya ce wakilan hukumar yaki da cutuka ta Amurka kusan 15 ne ke aiki da WHO tun daga watan Janairu kuma ana bayyana musu duk wani ci gaba da ake samu kan wannan lamari.
"Ba mu da wani abu da muke boyewa a WHO, da zarar wani bayani ya samu muke bayyana shi - saboda magana ce ta rayuka," in ji Dakta Tedros.
Ya kuma yi gargadin cewa kada rikicin siyasa ya lalata kokarin da ake yi na ceto rayuka.
"Kun san daga inda na fito - na san me ake kira yaki. Na san me ake kira talauci. Na san me ake kira annoba. Na san yadda mutane ke shiga cikin mummunan yanayi. Na san yadda ake kashe mutane saboda talauci," in ji Dakta Tedros dan kasar Habasha wato Ethiopia.
"Watakila mutanen da ba su san duka wadannan abubuwan ba sun tashi cikin rayuwa mai sauki. Watakila ba su san me ake kira yaki ba, ba su san me talauci ke nufi ba. Shi ya sa nake cikin matsananciyar damuwa."

Asalin hoton, Nigeria Presidency
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gode wa wadanda suka taya shi alhinin rasuwar Mallam Abba Kyari, Shugaban Ma'ikatan Fadar Shugaban Kasa wanda aka yi jana'izarsa ranar Asabar.
Abba Kyari ya mutu ne a daren ranar Juma'a a JIhar Legas bayan ya yi jinyar cutar korona na 'yan makonni. An binne shi a Makabartar Gudu da ke Abuja, babban birnin kasar.
Shugaba Buhari ya kuma yaba wa mutane bisa abin da ya kira "dabbaka tsare-tsaren hukumomin lafiya" a yakin da ake yi da cutar korona, sakamakon guje wa taron zaman makoki da aka yi.
"Bin umarnin da kuka yi na guje wa taruka ya nuna cewa kuna taka rawa wurin dakile yaduwar annobar korona," in ji Buhari, a wata sanarwa da Garba Shehu mai magana da yawunsa ya fitar a ranar Litinin.
Daga cikin wadanda suka taya shugaban alhinin rasuwar, akwai jam'iiyyar PDP, da Atiku Abubakar, da Sarkin Bauchi Dr. Rilwan Sulaiman Adamu, da Shugaban Majalisar Dattawa Ahmed Lawan, da tsohon Shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo da sauransu.
Shugaba Buhari ya bayyana Abba Kyari a matsayin amininsa na kusa "wanda ya fi su jajircewa".
Faraansa ce kasa ta baya-bayan nan da aka samu mutuwar sama da mutum 20,000 da ke da alaka da cutar korona, karuwar adadin da shugaban hukumar lafiyar kasar ya kira ''gagarumin abin bacin rai''.
Ya zuwa ranar Litinin, mutum 20,265 ne suka mutu sanadiyyar wannan cuta a Faransa - 12,513 daga cikinsu a asibiti, 7,752 suka mutu a gidajen jinya, in ji Jérôme Salomon.
Ya kara da cewa "kasarmu na cikin mummunan yanayi a daren yau".
Gabanin wannan, akwai kasashe uku da suka samu adadin mutuwar da ta haura mutum 20,000 - wadanda suka hada da Spaniya da Italiya da kuma Amurka.

Asalin hoton, Getty Images
Shugaban kasar Rwanda, Paul Kagame ya yi gargadin cewa sai an dauki kusan "tsawon karni ko fiye da haka" kafin Nahiyar Afirka ta farfado daga wahalhalun annobar cutar korona.
Kagame ya fada wa jaridar Financial Times cewa Afirka za ta bukaci kusan dala biliyan 100 na agaji daga kasashen waje.
Tuni Bankin Duniya ya yi gargadin cewa nahiyar za ta iya fadawa cikin tabarbarewar tattalin arziki a karon farko cikin shekara 25, yayin da kasuwanci tsakanin kasashen duniya yake tambal-tambal sannan farashin kaya yake faduwa.
Mista Kagame ya ce yana da kwarin gwiwa cewa za a iya samun ci gaba biyo bayan abin da ya kira "kyawawan matakai" da kasashe "abokan hulda irinsu Faransa da Jamus da China da Amurka" ke dauka.
Kasashe 20 mafiya karfin tattalin arziki a duniya na G20 sun sanar a makon da ya gabata cewa sun amince su yafe wa matalautan kasashe bashin da suke bin su, ciki akwai kasashen Afirka da yawa.

Asalin hoton, @AWTambuwal
Gwamnan jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal ya haramtawa Alhaji Musa Bashir mahaifin mai kamfanin man fetir na Rahamaniyya shiga Sokoto saboda cutar koronavirus.
Gwamnan Tambuwal ya shaidawa manema labarai cewa sun ji labarin daya daga cikin ‘ya’yansa gwaji ya tabbatar da yana dauke da cutar korona.
Gwamnan ya ce ya yi magana da shi har sau biyu, “amma ya nuna min yana kan hanya sai ya shigo Sokoto, kuma na ba da umurni a mayar da shi, saboda a cikin iyalin shi akwai mai dauke da cutar Kuma shi ba a yi mashi gwaji ba.”
“Wadanda ke hulda da Alhaji Musa Bashar da ake kira Rahamaniyya su yi magana da shi kada ya kuskura ya shigo Sokoto,” in ji Gwamna Tambuwal.
Sai dai duk da zargin da gwamna Tambuwal ya yi bai bayar da cikakken bayani ba kan hukumar da ta tabbatar masa da cewa daya daga cikin 'ya'yan Alhaji Musa Bashir na dauke da cutar.
Amma Gwamna Tambuwal ya ce zai dauki duk matakin da ya dace domin kare al’ummar jihar Sokoto idan har ya yi watsi da shawarar da aka ba shi.
Cutar korona na ci gaba da yaduwa a jihohin Najeriya, amma har yanzu cutar ba ta tsallaka jihar Sokoto ba.
Tuni gwamnatin Jihar ta dauki matakan dakile cutar daga jihar ta hanyar rufe iyakokinta.
Wasu al'ummar jihar kuma tuni suka fara barazana ga Alhaji Musa Bashir, kan za su dauki mataki akansa idan har ya taka kafarsa cikin Sokoto.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
Hukumomi a Italiya sun ce adadin mutanen da ke kamuwa da cutar korona ya yi kasa a karon farko a kasar tun bayen barkewar cutar.
''A karon farko mun ga gagarumin ci gaba: adadin wadanda ke kamuwa da cutar a yanzu ya ragu,'' kamar yadda shugaban hukumar kare fararen hula Angela Borelli ya shaida wa manema labarai.
Ya zuwa ranar Litinin, akwai mutum 108,237 da ko dai suna asibiti ana duba su ko kuma suna samun sauki a gida bayan gwajin da aka yi musu ya nuna suna dauke da cutar. Wannan adadin ya ragu da mutum 20 idan aka kwatanta da ranar da ta gabata - adadin ba yawa amma dai babbar nasara ce.
A ranar Lahadi, Adadin wadanda suka kamu da cutar ya kai 486.
Italiya ce kasa ta uku da ke da yawan masu dauke da cutar korona a duniya, bayan Spaniya da Amurka.
Sai dai cikin wannan lissafi babu mutanen da suka mutu a gidajensu da kuma wadanda suka mutu a wasu cibiyoyin lafiyar da ba na gwamnati ba.
Da yawan likitoci a kasar sun yi amannar adadin wadanda suka mutu da wadanda ke dauke da cutar zai iya fin wanda hukumomin suke fada.

Asalin hoton, Getty Images
Farashin man fetur a Amurka ya yi faduwar da bai taba yin irinta ba ta kashi 40 cikin 100 - rabon da a ga hakan tun shekarar 1986.
Faduwar ta zo ne duk da yarjejeniyar da aka cimma a farkon wannan watan na rage yawan man da ake fitarwa a kasuwar duniya domin farfado da darajar farashin man.
Farashin man a Nahiyar Turai ma ya fado amma ba da yawa ba. Wakilin BBC na tattalin arziki ya ce faduwar farashin a Amurka ta faru ne sakamakon yanayin kasuwar.
Sai dai annobar cutar korona na ci gaba da yin walagigi da farashin man a kasuwar duniya, yayin da man da ake da shi ya fi yawan abin da ake bukata.
Wakilin BBC ya ce yarjejeniyar da Shugaban Amurka Donald Trump ya jagoranci kullawa - ta rage kashi 10 cikin 100 na mai a kasuwar duniya - ba lallai ne ta yi wani tasiri ba.

Asalin hoton, Getty Images
Hukumar kwallon kafa ta Nahiyar Turai, Uefa za ta bayyana shirin yadda za a kare kakar bana ta 2019-20, inda za ta yi taro da mambobinta 55 ta bidiyo ranar Talata.
Uefa na fatan a kammala wasanni cikin watan Agusta, inda hukumar ta raba wasu mahukunta gida biyu, inda za a tantance kalandar wasanni.
Ana sa ran tsayar da takamaimiyar ranar karkare wasanni zuwa a kalla.tsakiyar Mayu.

Asalin hoton, KNSG
Gwamnatin Jihar Kano ta yi watsi da labaran da ake yadawa cewa an samu mace-mace a birnin a ranar Litinin, abin da wasu suka rika alakantawa da cutar korona.
A safiyar yau Litinin ne dai wasu hotuna da bidiyo suka fara yawo a shafukan zumunta cewa an samu mutuwar mutane a birnin Kano da ba a saba ganin irinta ba a lokaci guda, inda wasu suka rika alakanta hakan da cutar korona.
A wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na Twitter, Ma'aikatar Lafiya ta Jihar Kano ta ce tuni ta kaddamnar da wani shiri na tura masu jiyo mata abin da ke faruwa a cikin al'umma bisa tsarin Hukumar Lafiya ta Duniya.
Aikin wadannan masu kawo rahoto shi ne, a cewar gwamnatin, bayar da rahoton wadanda suka mutu da kuma zuwa makabartu domin tantance wadanda aka kai domin binnewa a kowacce rana.
"An bincika wannan jita-jita kuma an gano ba ta da tushe. Saboda haka wajibi ne mu yi watsi da ita," a cewar sanarwar.
Daga karshe sanarwar ta yi kira ga mutane musamman masu mabiya da yawa a shafukan sada zumunta da su taimaka wurin ilimantar da al'umma kan rashin sahihancin labarin.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X

Asalin hoton, Getty Images
Hukumomi a ksar Kenya sun tsare mutum 455 a cibiyoyin killace masu cutar korona bayan sun karya dokar hana fita da aka saka domin dakile yaduwar cutar.
Da ma can sai da suka gargadi mutane cewa za a killace duk wanda ya karya dokar bayan mutane da yawa sun fara karya dokar a wuraren taruwar jama'a da shagulgula.
Kazalika akwai rahotannin da kecewa mutane na bai wa 'yan sanda cin hanci domin su kyale su su wuce wurin duba ababen hawa.
Akwai cibiya 33 ta killace wadanda suka harbu da cutar korona a Kenya.
Ministan Lafiya Mutahi Kagwe ya bayyana a ranar Litinain cewa gwamnati na tanadar wurin kebewa na musamman ga ma'aikatan lafiya. Sannan ya ce gwamnati ce za ta dauki nauyin jinyar tasu tare da tallafi daga kungiyar Amref da Gidauniyar Rockefeller.
Karin mutum 449 sun mutu a asibitocin Birtaniya a cikin awa 24 da suka wuce, a cewar alkaluman gwamnatin kasar.
Hakan ya sa jumullar adadin ya zama 16,509 ya zuwa karfe 5:00 na ranar Lahadi.
Adadin na rana guda bai kunshi wadanda suka mutu a gidaje da kuma na gidan kula da gajiyayyu ba.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
Dokar hana fita ta mako uku da shugaban Ghana Nana Akufo-Addo ya dage ta janyo ce-ce-ku-ce a kasar.
Kananan ‘Yan kasuwa da dama da kafa dokar ya kawowa nakasu a harkokinsu sun yi maraba da matakin, yayin da jami'an lafiya ke kira da a sake tsawaita dokar.
Ana dai bayyana fargaba kan matakin dage dokar yayin da mutane suka yi watsi da shawarar da ake bayarwa cewa a dinga bayar da tazara tsakani.
Kusan mutum sama da dubu daya suka kamu da korona a Ghana, yayin da mutum tara suka mutu.

Alkaluman baya baya nan na cibiyar yaki da cututtuka masu yaduwa ta tarayyar Afrika sun nuna cewa mutum sama da 22,000 ne suka harbu da cutar korona a fadin nahiyar.
Tarayyar ta kara da cewa fiye da mutum 1000 sun rasa rayukansu.
Har wa yau, Tarayyar ta ce a wasu kaashen Afrika ciki har da Najeriya sun samu matukar karuwar yawan wadanda suka kamu da cutar.
Fasinjojin daya daga cikin manyan jiragen ruwa uku na duniya da ke ci gaba da zirga-zirga a saman teku sun tsaya a tashar jiragen ruwa ta Marseille da ke Faransa bayan shafe watanni a saman ruwa suna kokarin kaucewa cutar Korona.
Jirgin da ake kira MSC Magnifica dake dauke da fasinjoji 1700 yawancin su yan Faransa da Jamus da Italiya, ya soma balaguronsa ne bayan tashi daga tashar jiragen ruwa ta Italiya da ke birnin Genoa a ranar 1 ga watan Janairu.
Sai dai an dakatar da zirga-zirgar jirgin bayan da wasu kasashe suka ki amince wa ya ratsa ta yankunansu saboda fargabar annobar.
Ba a gudanar da gwajin cutar ga fasinjojin jirgin ruwan ba, yayin da bayanai ke cewa kusan kwanaki 40 kenan babu wanda ya fita waje daga cikin jirgin.
Har wa yau, su ma sauran jiragen biyu da suka hadar da gimbiyar Pacific da Costa Deliziosa za su tsaya yau din nan a Los Angels da kuma Barcelona.
Ma’aikatan jinya a Malawi sun shiga yajin aikin sai baba ta gani don nuna damuwa a kan karancin kayan kariya.
Ma’aikatan sun kuma nemi gwamnati ta kara yawansu, sannan ta kara musu albashi.
A halin da ake ciki mutane 17 ne aka tabbatar sun kamu da cutar korona a Malawi.
Rahotanni sun ce tasirin yajin aikin nasu ya shafi kusan dukkanin asibitocin gwamnati da ke fadin kasar.
A makon da ya gabata ne ministan lafiya Jappie Mhango, ya ce gwamnati ta dauki gabarar share musu hawaye, ta hanyar daukar karin ma’aikatan lafiya 1000 don yaki da annobar.