Mutum 160,952 ne suka mutu sakamakon cutar korona a duniya
Sabbin alkalu daga Jami'ar Johns Hopkins da ke bin sahun yaduwar annobar korna sun ruwaito cewa mutum fiye da miliyan biyu da dubu 300 ne suka harbu da cutar.
Ta kara da cewa mutum dubu 160,952 suka mutu, yayin da 598,584 suka warke.
Kasashe 7 da suka fi yawan masu cutar:
Amurka: 735,287US
Spaniya:194,416
Italiya: 175,925
Faransa: 152,978
Jamus: 143,724
Birtaniya: 115,314
China: 83,804