Hukumomi a Saudiyya sun
ce karin mutum 1,088 sun kamu da cutar korona inda jimilar masu dauke da cutar
a kasar suka kusan kai 10,000.
Ma’aikatar lafiya ta
Saudiyya ta ce adadin mutum 9,362 ne suka kamu da cutar korona a Saudiyya kawo
yanzu. Kuma adadin zai ci gaba da karuwa.
Kamfanin dillacin labaran Saudiyya SPA ya ambato kakakin ma’aikatar
lafiya Dr. Muhammad Al-Abdel Ali na cewa cikin sa’a 24 an kara samun mutum
biyar da suka mutu.
Kuma zuwa yanzu
jimillar mutum 97 cutar corona ta kasha a Saudiyya.
Sai dai ya ce wadanda
suka mutu daga baya dukkaninsu ba ‘yan kasar ba ne amma sun kunshi mutum hudu
mazauna Makkah da kuma mutum daya mazauni Jeddah.
Yawan wadanda ke dauke
da cutar korona sun fi yawa a Makkah inda mutum 251 ke dauke da cutar.
Mutum 210 ke dauke da
cutar a Jeddah, sai mutum 194 a Damman, yayin da mutum 177 ke dauke da cutar a
Madinah. An samu bullar cutar a sauran sassan Sadaudiyya.
Zuwa ynazu mutum 1,398
suka warke daga cikin wadanda suka kamu da cutar a Saudiyya, kuma ma’aikatar
lafiyar kasar ta ce kashi 17 daga cikin sabbin wadanda suka kamu da cutar ‘yan
asalin kasar ne, yayin da kashi 83 ‘yan kasashen waje ne.