Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Cutar korona ta bulla jihar Jigawa

Wannan shafin na kawo muku abubuwan da ke faruwa a duniya baki daya dangane da annobar coronavirus.

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail and Awwal Ahmad Janyau

  1. Rufewa

    A nan za mu dakata da kawo maku labarai da rahotanni kai tsaye kan abubuwan da ke faruwa a duniya dangane da annobar coronavirus.

    Da fatan za ku kasance da mu zuwa gobe inda za mu ci gaba da kawo maku labaria kai-tsaye kan abubuwan da ke faruwa a duniya.

    Sai gobe.

  2. Labarai da dumi-dumi, Coronavirus ta bulla a Jigawa

    Gwamnatin Jihar Jigawa ta tabbatar da bullar cutar korona a jihar da ke makwabtaka da Kano.

    Kwamishinan lafiya na jihar Abba Zakari ya tabbatar wa da BBC cewa an samu mutum na farko mai dauke da cutar a karamar hukumar Kazaure.

    Ya ce mutum wanda dan asalin Jigawa ne ya dawo ne daga jihar Enugu, kuma gwaji ya tabbatar da yana dauke da cutar bayan ya nuna alamunta

    Gwamnatin jihar ta sanar da matakin hana shiga da fita yankin Kazaure domin dakile bazuwar cutar.

  3. ‘Yan wasan Roma sun hakura da albashi har wata hudu

    ‘Yan wasa da masu horar da su a kulub din Roma na Seria A a Italiya sun sadaukar da albashinsu har tsawon wata hudu domin taimaka wa kungiyar farfadowa daga hasarar kudaden da ke shiga da wasannin da aka dage sakamakon annobar cutar korona.

    Sai dai kuma idan har aka kawo karshen annobar, kulub din ya amince ya kara wa ‘yan wasan albashi.

    Cutar korona ta fi kisan Mutane a Italiya fiye da ko ina bayan Amurka.

    ‘Yan wasa a wasu kungiyoyin sun amince su a datse masu albashi don taimakawa kungiyoyin.

    Tun a Maris aka dakatar da wasanni a Italiya

  4. Yawan masu coronavirus a Turkiya sun zarce na China

    Sabbin alkalumman da aka fitar a Turkiya sun nuna cewa yawan masu fama da cutar korona a yanzu sun zarce yawan na China inda aka fara samun barkewar cutar.

    Cikin sa’a hudu an samu mutum kusan dubu hudu da suka kamu da cutar a Turkiya, inda yanzu jimillar mutum dubu tamanin da shida suka kamu da cutar a kasar.

    Yanzu Turkiya ta fi yawan masu cutar fiye da sauran kasashen Asia. A rana mutum dubu dari da ashirin da bakawai suka mutu.

  5. Coronavirus ta kama ma'aikatan zabe a fadar shugaban Afghanistan

    Ma'aikatan zabe da dama ne a fadar shugaban kasa a Afghanistan suka kamu da cutar korana. kamar yadda kafofin yada labaran kasar suka tabbatar.

    Mutum 20 ne tun da farko rahotanni suka ce sun kamu da cutar, amma a ranar Lahadi jaridar New York Times ta ce adadin ya kai mutum 40.

    Gwamnatin Afghanistan ba ta ce komi ba kawo yanzu kuma babu wani kan ko shugaban kasar Ashraf Ghani wanda ke fama da cutar kansa ko ya kamu da cutar korona.

    Mutum kusan 1,000 suka kamu da cutar korona a Afghanistan kuma 33 sun mutu.

    Ana fargabar cewa cutar za ta ci gaba da yaduwa a kasar, bayan dawowar wasu 'yan Afganistan daga Iran yayin da kuma wasu daruruwa suka dawo da Pakistan

  6. Coronavirus: Na'urar ventilator 60 ga mutum miliyan 11

    Yayin da ake da adadin da bai wuce 60 ba na na'urar taimaka wa numfashi ta ventilator, mutum kusan miliyan 11 ne a kasar Haiti da ke yankin Latin Amurka ke cikin hadadrin cutar korona.

    Hakikanin hadarin da ake ciki a dakunan kulawar gaggawa na Haiti ba karami ba ne, kamar yadda wani bincike na 2019 ya nuna.

    A cewar wani likitan numfani Stephan Dragon a babban birnin kasar Port-au-Prince, adadin ventilaors din bai wuce 40 ba kuma babu mamaki 20 daga cikin ba sa aiki.

    Ya zuwa yanzu wannan matalauciyar kasa ta bayar da rahoton mutuwar mutum uku da kuma 40 da suka harbu da cutar korona. Sai dai akwai yiwuwar samun wasu da ke dauke da cutar a sassan kasar.

    Shekara 10 kenan da afkuwar wata girgizar kasa da ta halaka mutum fiye da dubu 200 sannan wasu kusan miliyan daya suka rasa muhallansu.

  7. Daga gida zan yi tafsirin azumi – Sheikh Ahmad Gumi

    Fitaccen malamin addinin a Najeriya Shiekh Dr Ahmad Gumi ya ce zai gudanar da tafsirin azumin bana ne daga gida, ba kamar yadda aka saba ba sakamakon annobar cutar korona da ake fama da ita.

    A shekaru da dama da suka wuce, Ahmad Gumi yakan gudanar da tafsirin azumin watan Ramadana ne a Masallacin Sultan Bello da ke birnin Kaduna a arewa maso yammacin Najeriya.

    Sheikh Gumi ya shaida wa BBC cewa zai fara tafsirin na bana ne a ranar Talata mai zuwa, inda mutum kasa da 10 za su halarta sannan kuma a yada shi kai-tsaye ta kafar Facebook baya ga gidajen rediyo a jihar da za su saka.

    Jihar Kaduna na cikin dokar hana fita tun ranar 26 ga watan Maris domin dakile yaduwar cutar korona.

    Gwamnan Jihar ta Kaduna Mallam Nasir El-Rufai ne gwamna na farko da ya kamu da cutar a Najeriya a ranar 28 ga watan Maris, kuma a ranar Laraba gwamnan ya ce har yanzu bai warke ba.

  8. Coronavirus: Kusan mutum 10,000 sun kamu a Saudiyya

    Hukumomi a Saudiyya sun ce karin mutum 1,088 sun kamu da cutar korona inda jimilar masu dauke da cutar a kasar suka kusan kai 10,000.

    Ma’aikatar lafiya ta Saudiyya ta ce adadin mutum 9,362 ne suka kamu da cutar korona a Saudiyya kawo yanzu. Kuma adadin zai ci gaba da karuwa.

    Kamfanin dillacin labaran Saudiyya SPA ya ambato kakakin ma’aikatar lafiya Dr. Muhammad Al-Abdel Ali na cewa cikin sa’a 24 an kara samun mutum biyar da suka mutu.

    Kuma zuwa yanzu jimillar mutum 97 cutar corona ta kasha a Saudiyya.

    Sai dai ya ce wadanda suka mutu daga baya dukkaninsu ba ‘yan kasar ba ne amma sun kunshi mutum hudu mazauna Makkah da kuma mutum daya mazauni Jeddah.

    Yawan wadanda ke dauke da cutar korona sun fi yawa a Makkah inda mutum 251 ke dauke da cutar.

    Mutum 210 ke dauke da cutar a Jeddah, sai mutum 194 a Damman, yayin da mutum 177 ke dauke da cutar a Madinah. An samu bullar cutar a sauran sassan Sadaudiyya.

    Zuwa ynazu mutum 1,398 suka warke daga cikin wadanda suka kamu da cutar a Saudiyya, kuma ma’aikatar lafiyar kasar ta ce kashi 17 daga cikin sabbin wadanda suka kamu da cutar ‘yan asalin kasar ne, yayin da kashi 83 ‘yan kasashen waje ne.

  9. Ma'abota TikTok ku daura damara, an samu "Gidan TikTok" a Birtaniya

    Mutum shida mafiya shahara da ke amfani da dandalin sadarwa na TikTok a Birtaniya sun koma zama a gida daya a yunkurinsu na habaka adadin bidioyon da suke samarwa ga matasa, yayin da ake fama da zaman gida.

    Kamfanin Bytehouse ne ya shirya zaman nasu tun kafin a saka dokar hana fita a Birtaniya.

    Wannan ne "Gidan TikTok" na farko a Birtaniya, wanda tun-tuni ake da irinsa a Amurka.

    Mutanen wadanda suke da mabiya miliyan 14 jumulla, mutum kusan miliyan 73 ne ke kallon bidiyonsu a duk sati.

    TikTok, dandalin sadarwar da ake yada gajerun bidiyo, ita ce manhajar da aka fi saukewa a kan wayoyiyi a shekarar 2019 bayan WhatsApp.

    • Labarai da dumi-dumi, Wadanda suka mutu a Birtaniya sun karu da 596

      Adadin wadanda suka mutu a asibitocin Birtaniya ya kai 16,060 ya zuwa karfe 5:00 na yammacin ranar Asabar, a cewar Sashen Lafiya da Kula da Jama'a.

      Hakan na nufin an samu karin mutum 596 a cikin awa 24 da suka gabata, wanda kuma ragi ne in aka kwatanta da 888 na rana kafin wannan.

      Zuwa karfe 9:00 na safiyar Lahadi, an yi wa mutum dubu 482,063 gwajin cutar kuma 21,626 daga ciki an yi su ne a ranar Asabar.

    • Dokar hana fita: An kama masu jana'izar karya a Kenya

      'Yan sanda a kasar Kenya da ke sa ido kan dokar hana fita sun kama wasu mutum hudu da suka yi badda-kama a matsayin masu jana'iza dauke da gawa a kan titin birnin Nairobi.

      Sun bar babban birnin Nairobi kuma suka yi tafiyar kilomita 370 zuwa yamma da fankon akwatin gawa a motarsu kafin daga baya a kama su, a cewar ministan lafiya a ranar Asabar.

      Kusan mako biyu kenan ba a shiga ba a fita a birnin Nairobi da kuma wasu yankuna uku da suka fi fama da cutar korona.

      Rukunin masu sojan-gonar sun samu wuce wuraren ababen hawa da dama kafin wasu 'yan sandan gaza gani a Homa Bay County su bude akwatin gawar, in ji Ministan Lafiya Mutahi Kagwe.

      Daga baya an gano direban motar yana dauke da cutar. Su ma sauran abokan tafiyar tasa an tsare su.

    • Da fatan ba ku manta da #DontRushChallenge ba

      Na san za ku iya tunawa da bidiyon nan na 'yan mata da samari da suka gallabi shafukan sada zumunta da yadda suke kwalliya da burushin shafa hoda.

      Idan ma tsautsayi ya sa ba ku sani ba, to ga bidiyon da kuma wadanda suka kirkiro shi domin nishadantarwa.

      Latsa hoton kasa ku sha kallo

    • Babu damuwa don an hana mu shiga Aso Villa – Garba Shehu

      Garba Shehu, mai magana da yawun Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce "ba wani abin mamaki ba ne" don an hana su shiga Fadar Shugaban Kasa ta Aso Villa saboda sun halarci jana'izar Abba Kyari.

      Mallam Garba Shehu yana mayar da martani ne kan wasu rahotanni da ke cewa an rufe wa wadanda suka halarci jana'izar Mallam Abba Kyari kofar shiga Villa, wadda aka yi jiya Asabar a Abuja.

      Daga cikin wadanda suka halarci jana'izar har da Ministan Sadarwa Dr Isa Ali Pantami da shi Garba Shehu da kuma da yawa daga cikin mataimaka na musamman ga Shugaba Buhari a fannoni daban-daban.

      "Ai da ma a mafi yawan lokacin nan ta intanet aka fi yin harkoki a Villa saboda haka ba wani sabon abu ba ne don an hana mu shiga," in ji Garba Shehu, a wani sako da ya wallafa a Twitter.

      Ya kara da cewa: "An yi hakan ne bisa umarnin hukumar NCDC da kuma Ma'aikatar Lafiya. Ana yin hakan ne kuma domin dakile yaduwar cutar korona."

      Tuni hukumar birnin Abuja ta FCTA ta ce an tafka kuskure yayin jana'izar ta Abba Kyari bayan an ga wani mutum yana jefar da kayayyakin kariyar da suka yi amfani da su a gefen titi bayan binne gawar a Makabartar Gudu.

      Hukumar ta ce ta tsare ma'aikatan da ta gano ba su yi aikin yadda ya kamata ba domin ganin ko sun kamu da cutar da kuma dakile ta.

    • Labarai da dumi-dumi, Mutum daya ya mutu a Legas, 23 sun kamu

      Ma'aikatar Lafiya ta Jihar Legas ta ce mutum daya ya mutu a jihar sakamakon cutar korona sannan wasu 23 sun kamu da cutar a cikin awa 24 da suka gabata.

      Kazalika ma'aikatar ta ce an sallami wasu mutum hudu da suka hada da maza uku da mace daya daga asibiti bayan sun warke daga cutar.

      Jumullar adadin masu korona a Legas zuwa yanzu sun kai:

      Wadanda suka harbu da cutar: 309

      Wadanda ke dauke da ita a yanzu: 196

      Wadanda suka warke: 94

      Wadanda suka mutu: 14

      Wadanda aka sauya wa wurin jinya: 3

    • Yadda ya kamata ku mu'amalanci yaranku yayin zaman gida

      Hukumar NCDC mai yaki da yaduwar cutuka a Najeriya ta zayyana yadda ya kamata ku mu'amalanci yara a wannan lokaci na zaman gida sakamakon cutar korona

      A karkashin wani kamfe na wayar da kai game da yaki da cutar korona mai taken #TakeResponsbility, NCDC ta bayyana yadda za ku yi magana da 'ya'yanku.

      Daga cikinsu akwai:

      • Ku yi tattauanawa ta gaskiya (ba wasa ba) da yaranku game da dalilin da ya sa aka hana su fita zuwa inda suka saba zuwa kamar makaranta
      • Ku tambaye su abin da suka sani game da cutar korona, yaya suke ji game da ita sannan kuma me ya sa suke jin hakan
      • Ku yi musu bayanin irin girma da hadarin cutar
      • Ku yi musu bayanin yadda za su iya kamuwa da cutar
      • Ku jaddada tare da koya musu yadda za su kare kansu
      • Ku rika aikata abin da kuka koya musu a gabansu - Hausawa na cewa zuwa da kai ya fi sako

      Za ku iya ci gaba da karanta abubuwan da ya kamata ku rika yi yayin zaman gida a shafin NCDC cikin Ingilishi

    • Musulmai su bi umarnin hukumomi a lokacin Ramadana – Zauren Malamai

      Zauren manyan malaman Musulunci da ke kasar Saudiyya ya shawarci al'ummar Musulmi a fadin duniya da su bi shawarwarin da hukumomin lafiya ke bayarwa a lokacin azumin Ramadana da ke tafe.

      Kamfanin dillancin labaran Saudiyyya SPA ya ruwaito zauren malaman yana bayar da wasu shawarwari kamar haka:

      • Ya kamata Musulmai su bi umarnin kwararru a harkar lafiya da gwamnatoci wadanda aka tanada domin kare lafiyar al'umma daga cutar korona
      • Ya kamata Musulmai su yi sallolin farilla da na Asham (Tarawihi) a gidajensu idan har hukumomi sun umarce su da yin hakan
      • Wajibi ne Musulmai su guji yin taruka - ganin cewa bincike sahihai sun tabbatar da cewa an fi harbuwa da cutar ta hanyar haduwar mutane wuri guda, ciki har da taron shan ruwa (bayan Magariba) da kuma lokacin sahur.

      Da ma dai tuni Saudiyya ta ce ba za a yi sallar Asham ba (Tarawihi) a masallacin Ka'aba a lokacin azimi.

      A cikin makon nan ne ake sa ran Musulmi a fadin duniya za su fara azimin na watan Ramadana, wanda ake shafe kwana 29 ko 30 ana yi daga asuba zuwa faduwar rana.

    • Mutum 541 ne suka kamu da cutar korona a Najeriya, ba 542 ba

      Hukumar NCDC mai yaki da yaduwar cutuka a Najeriya ta ce ta yi kuskure a rahoton da ta bayar a daren jiya Asabar da yake cewa an samu karin mutum daya da ya kamu da cutar korona a Jihar Ekiti.

      Saboda haka hukumar ta ce ya zuwa daren jiya 18 ga watan Afrilun 2020, akwai mutum 541` da suka harbu da korona, ba 542 ba, sannan kuma jihar Ekiti mutum uku take da su ba hudu ba.

      Hukumar ta ce kuskuren ya faru ne a lokacin tantancewa.

      Saboda haka BBC ma ta gyara rahotonta: mutum 541 ne suka harbu da cutar korona a Najeriya, an sallami 166 sannan 19 sun mutu.

      To kuma da ma kun san ba ma yin kwai sai da zakara! Ko ba gaskiya ba?

    • Za a sassauta wa yara dokar hana fita a Spaniya

      An garkame yara a kasar Spaniya a gidajen iyayensu ne tun a ranar 14 ga watan Maris domin a dakile yaduwar annobar cutar korona.

      Yanzu Firaminista Pedro Sánchez ya ce zai sassauta dokar a ranar 27 ga watan Afrilu domin ba su damar "shakar iska"

      A wannan makon ne Shugabar yankin Barcelona - Ada Colau - wadda ita ma take da yara, ta roki gwamnati da ta kyale yara su fita waje.

      Mutum sama da 20,000 ne suka mutu a Spaniya tun bayan bullar annobar korona a kasar kuma kusan dubu 200 ne suka harbu da ita.

      A wani jawabi da ya yi ta kafar talabijin a yammacin Asabar, Mista Sánchez ya ce "Spaniya ta shallake wani yanayi mafi tsanani na cutar".

    • Masu sharhi sun fara muhawara kan wanda zai maye gurbin Abba Kyari

      Jim kadan bayan jana'izar Abba Kyari - ko kuma kafin a yi - mutane suka fara hasashen wanda zai maye gurbinsa a fadar shugaban Najeriya.

      Wasu masu sharhi kan harkokin siyasar kasar na ganin cewa yanzu hankali zai koma kan mutumin da zai gaje shi.

      Daga cikin wadanda ke hasashen daya daga cikinsu zai zama Shugaban Ma'aikatan Fadar Gwamnati akwai:

      • Hammeed Ali
      • Adamu Adamu
      • Nasir Elrufai
      • Babagana Kingibe
    • Idan ba ku manta ba...bayan jana'izar Abba Kyari

      • Abba Kyari Shugaban Ma'aikatan Fadar Gwamnatin Najeriya ya rasu a daren ranar Juma'a a Jihar Legas bayan ya yi jinyar cutar korona. An yi jana'izarsa a Makabartar Gudu da ke Abuja ranar Asabar
      • Kwamishinan Ayyuka na Jihar Kano, Injiniya Mu'azu Magaji ya nuna jin dadinsa ga mutuwar ta Abba Kyari
      • Gwamnan Kano Abdullah Ganduje ya tube kwamishinan daga mukaminsa
      • Jim kadan bayan binne Abba Kyari, aka ga daya daga cikin wadanda suka binne gawar yana tube kayan kariyar da ya saka yana jefar da su a gefen titi - a wani bidiyo da ya bulla a shafukan sada zumunta
      • Hukumar birnin Abuja ta ce ta fara bincike domin gano mutumin da ya aikata wannan danyen aiki.
      • Tun a jiya Asabar aka fara hasashe tare da jita-jitar wanda zai maye gurbin Mallam Abba Kyari a matsayin shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa.