Za a yi gwajin riga-kafin covid-19 a kan mutane
Kafofin watsa labaran China sun rawaito cewa za a yi gwajin riga-kafin cutar korona guda biyu a jikin dan adam.
Kwanan baya, Hukumar Lafiya ta Duniya ta bayyana cewa ana gwada fiye da riga-kafin cutar korona 70 a fadin duniya, kuma uku daga cikinsu sun kai matakin gwada su a jikin dan adam.
Biyu daga cikin ukun, an gwada su ne sa Amurka, yayin da na ukun aka gwada shi a China. Wadannan riga-kafi su ne na hudu da na biyar da suka kai matakin gwaji kan dan adam.
Ruguguwar da ake yi na samar da riga-kafin cutar korona na nufin ana tsallake ka'idojin da al'adance ake dauka wajen samar da riga-kafin cututtuka.
Sai dai kamar yadda wakilin BBC James Gallagher ya bayyana a farkon watan nan, samu riga-kafin cutar zai dauki lokaci.
"Ko da wadannan gwaje-gwaje sun yi nasara, ba a tsammanin kamfanonin magunguna za su soma yin magunguna da yawa ba sai tsakiyar shekarar 2021," in ji shi.







