Rufewa
Masu bibiyarmu nan muka kawo karshen wannan shiri na kawo muku bayanai kai tsaye. Da fatan za ku kasance da mu idan Allah ya kai mu ranar Laraba.
Wannan shafin na kawo muku abubuwan da ke faruwa a duniya baki daya dangane da annobar coronavirus.
Nasidi Adamu Yahaya, Halima Umar Saleh and Usman Minjibir
Masu bibiyarmu nan muka kawo karshen wannan shiri na kawo muku bayanai kai tsaye. Da fatan za ku kasance da mu idan Allah ya kai mu ranar Laraba.
Majalisar Dinkin Duniya ta ce kashin farko, na jiragen da ke dauke da kayan agajin yaki da cutar Korona sun tashi daga birnin Adis Ababa da ke Ethopia don rarrabasu sauran kasashen nahiyar.
Jirgin dakon kaya na farko da ya tashi, na dauke da miliyoyin takunkumin da wasu kayayyakin kariya na ma’aikatan kiwon lafiya da naurorin taimakawa numfashi.
Wasu daga cikinsu hamshakin dan kasuwar nan na China Jack Ma ne ya bayar da su kuma Firai ministan Ethopia Abiy Ahmad.
Zuwa yanzu dai cutar ba ta yi kamari a Afrika kamar yadda tayi a sauran nahiyoyin duniya ba.
Gwamnatin jihar Kano ta ce za ta aiwatar da dokar hana fita ta mako guda sakamakon yaduwar cutar korona a jihar.
A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan jihar, Abba Anwar ya fitar, gwamnati ta ce dokar hana zirga-zirga za ta fara aiki ne a ranar Alhamis 16 ga watan Afrilu 2020.
Sanarwar ta ambato gwamna Ganduje na cewa " bayan mao guda za mu ga iko Allah daga nan sai mu dauki matsaya."
Da yammacin ranar Talatar nan ne dai ma'aikatar lafiyar jihar, ta tabbatar da saun mutum na uku da ya kamu da cutar ta korona.
Ma'aikatar ta jihar Kano ta tabbatar da samun karin mutum daya da ke dauke da cutar korona.
Hukumar wadda ta wallafa bayanin a shafinta na Twitter ta ce har yanzu mutum 3 suka kamu da cutar a jihar.
A saboda haka hukumar ta yi kira da a yi watsi da duk wani bayani da ya nuna cewa masu dauke da cutar sun fi 3 a jihar.
A makon jiya ne dai aka fara samun mai dauke da cutar na farko a jihar wanda aka ce ya bar birnin Abuja zuwa Kano.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X

Shugaban kasar Guinea, Alpha Conde ya ce sanya takunkumin fuska ya zama dole a wani mataki na dakile yaduwar cutar korona.
A wani jawabi a gidan talbijin, Conde ya ce dokar za ta fara aiki ne ranar Asabar.
Duk mutumin da aka samu ya karya dokar kin sa takunkumin na fuska a kasar zai biya kimanin $3.
Alpha Conde ya yi kira ga 'yan kasuwa da ma'aikatun gwamnati da sauransu da su sama wa ma'aikatansu takunkuman fuskar wadanda ya ce ya kamata a yi su a cikin gida a farashi mai rahusa.
Yanzu haka dai kasar ta Guinea na da mutum 300 masu dauke da cutar ta korona.

Shugaban fannin lafiya na kasar Mozambique ya yi gargadi cewa amfani da safar hannu domin kariya daga cutar korona ya ce hakan zai janyo daukar cutar.
Rosa Marlene, ta ce " wannan safar ta hannu ba ta kariya daga kamuwa da cutar korona saboda mutum zai taba fuskarsa ko baki ko kuma idanu bayan taba wani abun da ke da cutar.
Dr Marlene ta sake nanatawa cewa wanke hannu da kuma samar da tazara su ne hanyoyin kariya daga kamuwa da cutar korona.

Asalin hoton, BBC Marathi
'Yan sanda a India sun yi amfani da karfi wajen tarwatsa dandazon 'yan cirani masu zanga-zanga wadanda suka yi burus da dokar kulle a yammacin birnin Mumbai.
'Yan ciranin dai sun yi tsammanin cewa dokar kullen za ta karkare a ranar Talata, inda suka yi dandazo a wata tashar jirgin kasa domin komawa gidajensu, kamar yadda ministan cikin gidan kasar, Anil Desmukh ya shaida wa BBC.
Firai minista, Narendra Modi dai ya sanar da tsawaita dokar kullen ne har zuwa ranar 3 ga watan Mayun 2020.
To sai dai masu hamayya na cewa zanga-zangar da jama'a suka yi na da alaka da rashin abinci ne da tsaro a wuraren da dokar ta shafa.

Asalin hoton, Getty Images
Kamfanonin waya a Birtaniya sun yi zargin masu kone-kone da kona musu turakun waya guda 20 a karshen mako.
An dai ta yada jita-jitar cewa tsarin fasaha 5G ne ya janyo cutar korona ko kuma ke kara baza ta a duniya.
Labarin hare-haren kan turakun na zuwa ne a dai-dai lokacin da kamfanin Ofcom mai sa ido kan gidajen jarida ya sanar da cewa yana duba yiwuwar angiza mai kantu ruwa da kalaman Earman Holmes dangane da tsarin na 5G da cutar korona.
An samu hare-hare a kan turakun kamfanonin wayar a Ingila da Wales da Scotland.
An kuma samu irin wadannan hare-haren a Netherlands da kuma Ireland.
Jami'an Hukumar Unicef sun bayyana fargabar barkewar cutar kyanda sakamakon cutar korona kasancewar ana samun tsaiko dangane da allurar rigakafi.
Unicef ta ce kananan yara 117 a kasashe 37 ka iya rasa samun allurar rigakafi a kan lokaci.
An samu karuwar barkewar cutqar ta korona a kasashen nahiyar Turai da dama inda allurar ta rigakafi ta yi karanci.
Shugaban Uganda Yoweri Museveni ya tsawaita dokar hana fita a kasar a kokarin dakile cutar korona.
An tsawaita dokar ne da kwana 21.
A jawabin da ya yi wa 'yan kasar a karshen wa'adin kwana 14 na hana fita, shugaban kasar ya ce za a ci gaba da aiwatar da dukkan matakan da aka gindaya a baya.
Matakan sun hada da rufe iyakokin kasar, da filin jirgin saman kasa da kasa na Entebbe da kuma dokar hana fita ba dare ba rana da ma haramta shiga motocin haya.
Mr Museveni ya ce tsawaita dokar hana fitar zai bai wa ma'aikatan lafiya su sanya ido kan yaduwar cutar da kuma mutum sama da 18,000 da suka shiga kasar tsakanin ranar 7 zuwa 22 ga watan Maris.
Ya zuwa yanzu an dauki samfurin mutum 5,600 da aka yi wa gwaji inda aka tabbatar mutum 54 sun kamu da cutar, yayin da ta yi ajalin mutum takwas.

Asalin hoton, Getty Images
Ana fitar da dubban 'yan Ethiopia da ba su da takardu daga Saudiyya a kokarin da kasar take yi na dakile cutar korona.
Da ma dai a ko da yaushe 'yan kasar Ethiopia da ba su da takardu amma suke aiki a Saudiyya a shirye suke a fitar da su daga kasar.
An fitar da daruruwan dubban bakin haure daga Saudiyya tun lokacin da kasar ta soma fitar da wadanda ta bayyana a matsayin "'yan kasashen waje da ba su da takardu" a 2017.
Saudiyya ta ci gaba da fitar da bakin haure bayan an kwashe mako biyu ana tafka takaddama.
'Yan kasar Ethiopia kimanin 2,000 sun isa Addis Ababa, babban birnin kasar a farkon watan Afrilu inda ake sa ran isar wasu nan gaba.
Ya zuwa yanzu dai an tabbatar da mutum 82 da suka kamu da cutar korona a Ethiopia.

Asalin hoton, Getty Images
Kungiyar kare hakkin bil adama ta Human Rights Watch ta soki tsarin da gwamnatin Najeriya ta yi na tallafa wa masu karamin karfi domin rage musu wahalar da ke tattare da dokar hana fita.
Kungiyar ta ce tallafin da gwamnatin Najeriyar ke bayarwa ba ya isa hannun mafi yawan matalautan kasar.
Ta bayyana cewa hanyoyin da gwamnatin Najeriya ke bi wajen agaza wa marasa galihun na da rauni, don haka da yiwuwar a yi a kare ba tare da tallafin ya kai hannun mutanen da su ne talaucin ma ya yi musu kanta ba.
A cewar kungiyar dokar hana fitar da gwamnatin tarayya ta kafa, duk da cewa ta yi haka ne da nufin rage yaduwar cutar korona, a bangare guda kuma tana da kuntata rayuwar talakawa, musamman ma masu rayuwa hannu-baka-hannu-kwarya, kasancewar za su rasa aikin yi.
Wannan ne ma ya sa kungiyar ta tunatar da mahukunta cewa hakki ne da ke wuyan gwamnati ta samar da abinci da muhulli da sauran muhimman abubuwan more rayuwa ga al`umma.
Ke nan akwai bukatar gwamnatin tarayyar ta sake lale wajen lalubo ainihin talakawan da ke galabaita don tallafa musu, musamman ma a wannan lokacin da gwamnatin ta tsawaita dokar hana fita da karin mako biyu a jihohin Legas da Ogun da kuma Abuja, babban birnin tarayyar kasar.
Shugaba Muhammadu Buhari dai ya yi alwashin cewa gwamnati za ta fadada shirin ta yadda zai kai ga hannun maru karamin karfi miliyon uku da dubu dari shida.

Asalin hoton, FACEBOOK/BUHARI SALLAU
Ku kalli wannan bidiyon na dakika 56 domin ganin yadda ake wanke hannaye.
Kungiyar Tarayyar Turai ta bai wa gwamnatin Najeriya tallafin euro miliyan 50, a matsayin gudunmowarta ga kasar don yaki da #COVID19.
Mai taimakawa Shugaba Buhari kan shafukan sada zumunta Bashir Ahmad ne ya sanar da hakan a shafinsa na Twitter a ranar Talata.
Bashir ya ce shugaban EU Ambasada Ketil Karlsen ne ya sanar da ba da tallafin a wata ganawa da ya yi da Shugaba Buharin ranar Talata a Abuja.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
Hukumar Tarayyar Turai ta roki kasashen nahiyar su rika tuntubar ta game da kowane shiri na saukaka dokar hana zirga-zirga don yaki da Cutar Korona.
Wasu kunshin bayanai na cikin gida da BBC ta samu sun nuna cewa Tarayyar Turai ta bayar da shawarar ko da za a saukaka dokar, kamata ya yi a ce an soma ne da 'yan kasuwa, shagunan abinci da makarantu, yayin da su ma za su suke kiyaye dokar yin nesa-nesa da juna.
Ta kuma yi gargadin cewa ci gaba da saukaka dokar hana zirga-zirga kai tsaye na iya kawo karuwar mutanen da ke kamuwa da cutar a duniya.
Wannan dai na zuwa ne bayan da kasashen Turai da dama ciki har da Italiya da Austria da Demmark suka soma bai wa jama'a damar fita don ci gaba da harkokinsu.
Kayan aikin lafiya kashi na farko daga Hukumar Lafiya Ta Duniya WHO sun isa birnin Addis Ababa na Habasha a ranar Talata.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
Kayan sun hada da miliyoyin takunkuman rufe fuska, da tabarau da safar hannu da rigunan kariya da sauran kayan kariya na ma'aikatan lafiya, da ventilators ga masu jinya, a cewar Hukumar Samar Da Abinci Ta Duniya, WFP.
Za a rarraba kayayyakin a Djibouti da Sudan da Eritrea da Somalia da kuma Tanzania, daga wadannan wurare kuma za a aika wa sauran kasashe da dama, kamar yadda Reuters ya rawaito mai magana da yawun WFP Elisabeth Byrs tana cewa.

Asalin hoton, Science Photo Library
Ana fargabar barkewar annobar kyanda a yayin da ake tsaka da yaki da annobar cutar korona, jami'ai sun ce hakan na iya faruwa ne saboda an dakatar da yin riga-kafin kyandar don fafutukar dakie Covid-19.
Asusun Kula da Yra na Majalisar Dinkin Duniya ya ce ba za a yi wa yara miliyan 117 a kasashe 37 riga-kafin a kan lokaci ba.
An samu barkewar annobar kyandar a wasu sassan Turai inda aka samu raguwar yin allurar riga-kafin cutar.
Tuni Burtaniya ta rasa tunkahonta na zama kasar da ba ta fama da annobar kyanda, saboda sabbin wadanda suke kamuwa da cutar da ake samu.
Kyanda cuta ce da ke jawo tari da kuraje a jiki, amma ana iya riga-kafinta ta hanyar yin wata allura ta MMR, wacce take kyauta ce ga dukkan yara a Burtaniya.
Bayani na baya bayan nan game da Asia:
Firai ministan India ya yi gargadin daukar tsauraran matakai nan da mako mai zuwa, a yayin da ya tsawaita dokar hana fita zuwa ranar 3 ga watan Mayu. Za mu saurari karin bayani ranar Laraba.
Gwamnatin Eswatini, kasar Kudancin Afirka da a baya ake kiranta Swaziland, ta musanta rahotannin da kafafen watsa labarai ke bayarwa cewa Sarki Mswati na III ya kamu da Covid-19.
Gwamnati ta wallafa sakon Twitter da ke cewa Sarki "yana nan lafiya kalau" sannan ta yi watsi da rahotannin inda ta bayyana su a matsayin "labaran karya tsagwaronta".
"Gwamnati tana gargadin masu yada wannan labarin karya cewa suna keta dokar sanya ido ta Covid-19 kuma suna iya fuskantar shan dauri a gidan yari," in ji kakakin gwamnati Sabelo Dlamini.
Kasar ta Eswatini na cikin kasashen duniya kalilan da sarakuna ke jagorancinsu.
Ya zuwa wannan lokaci an tabbatar mutum 15 sun kamu da cutar korona a kasar.

Asalin hoton, Getty Images
Asusun bayar da Lamuni na Duniya ya bayar da umarnin gaggawa na sassauta bashin da yake bin kasashen Afirka 19 zuwa wata shida domin su samu damar yin amfani da kudaden wajen yaki da cutar korona.
Burkina Faso, Chadi, Jamhuriyar Tsakiyar Afirka da Mozambique na cikin kasashen da za su ci moriyar wannan sassauci.
Sauran kasashen sun hada da Benin, Comoros, Jamhuriyar Domikradiyyar Congo, The Gambia, Guinea, Guinea-Bissau, Liberia, Madagascar, Malawi, Mali, Niger, Rwanda, São Tomé and Príncipe, Sierra Leone da kuma Togo.
Soke bashi da kuma bayar da tallafi ga kasashen Afirka na cikin matakan da kungiyoyin da ke fafutuka suka yi kira a dauka domin dakile yaduwar cutar korona.

Asalin hoton, Getty Images