Spain ta sassauta doka kan coronavirus
Spaniya, daya daga cikin kasashen da suka fi fama da annobar coronavirus, ta soma sassauta dokar hana fita wadda ta kusan durkusar da tattalin arzikinta.
An soma barin mutanen da ke aiki a ma'aikatun kere-kere da wasu ma'aikatun su koma bakin aiki, ko da yake an gindaya musu tsauraran sharuda.
Dole ma'aikatan sauran wurare su ci gaba da zama a gidajensu.
Kimanin mutum 17,500 ne suka mutu sanadin Covid-19 a Spaniya, amma an samu raguwar wadanda ke kamuwa da cutar.
Italiya - kasar da ta fi fama da coronavirus a Turai, inda kusan mutum 19,900 suka mutu - za ta takaita masana'antun da za su sosa aiki ranar Talata.