Hukumar yaki da cututtuka ta Afirka, Africa CDC, ta ce mutum 2570 ne suka warke daga coronavirus a kasashe 52 mambobin kungiyar Tarayyar Afirka ya zuwa ranar Litinin, 13 ga watan Afrilun 2020.
Sanarwar da ta wallafa a shafinta na Twitter, hukumar ta ce 14,528 ne suka kamu da cutar yayin da mutum 788 suka mutu a kasashen.
Ya zuwa yanzu dai, Afirka na cikin nahiyoyin da ba a samu mutuwa sosai kan coornavirus ba, abin da masana kiwon lafiya suka alakanta da rashin isassun na'urorin gano masu dauke da cutar.
Sun jaddada kira ga mutane su dauki matakan kare kansu daga kamuwa da cutar, wadanda suka hada da yawaita wanke hannaye da yin nesa-nesa da juna da amfani da kyalle wajen yin atishawa da makamantansu.