Tun bayan da Najeriya ta tabbatar da samun mutum na farko da ya kamu da coronavirus, har ya zuwa jiya Asabar mutum 5,000 aka yi wa gwajin cutar a kasar, a cewar kamfanin dillancin labarai na AFP.
Tun a ranar 27 ga watan Fabrairu ne Najeriya ta tabbatar da bullar cutar a jikin wani dan kasar Italiya bayan ya isa Jihar Legas sannan kuma ya je Jihar Ogun.
Zuwa lokacin hada wannan rahoton mutum 318 sun kamu da ita - 10 sun mutu 70 sun warke.
Kasar Afirka ta Kudu mai adadin mutum miliyan 57, ta yi wa mutum 73,000 gwajin cutar ta Covid-19.
Ministan lafiyar Afirka ta Kudu ya ce: "Wannan ya yi matukar kadan in aka kwatanta da hadarin cutar a Afirka ta Kudu." Ya ce suna fatan su rika gwada mutum 30,000 a kullum.
Najeriya wadda ta fi girman tattalin arziki a Afirka kuma mai yawan al'umma miliyan 190, mutum 5,000 ne kawai suka samu yin gwajin ya zuwa ranar Asabar.
"Gwajin nan jidali ne," in ji wani likita da ke aiki a wani asibiti mai zaman kansa a Jihar Legas da ya bukaci kada a ambaci sunansa. Ya kara da cewa: "Ba mu sani ba ma ko adadin daidai-wadaidaita yake."
Rashin kayan aikin gwajin kan sa wasu kasashe su yi hasashen adadin mutanen da ke kamuwa da cutar. Kasar Kenya ga misali, ta yi hasashen cewa nan da karshen watan Afrilu masu cutar za su kai 10,000 a kasarta.
Sai dai kwana 10 da shiga Afrilu, mutanen da suka kamu da cutar ba su wuce 200. Babban darakta a ma'aikatar lafiyar kasar ya fada a farkon watan nan cewa hakan ya faru ne saboda ba su yi wa mutanen gari gwajin ba.
Shugaban hukumar yaki da cutuka masu yaduwa ta Africa Centres for Disease Control and Prevention ya fada wa AFP cewa sakamakon gwaje-gwajen cutar a Afirka "ba cikakke ba ne, ba mu da kayan aiki".