Coronavirus: Amurka ta fi kowacce kasa yawan wadanda suka mutu
Amurka a yanzu ta zarta Italiya a yawan wadanda suka rasa rayukansu sakamakon annobar coronavirus a duniya baki daya.
Sabbin alkaluma daga Jami'ar Jons Hopkins sun nuna cewa sama da mutum 20,000 ne suka mutu a Amurkar.
Wannan adadi maras dadin ji ya samu ne jim kadan bayan kasar ta bayyana samun fiye da mutum 2,000 da suka mutu a rana daya kacal - adadi mafi yawa kenan tun bayan barkewar cutar.
Gwamnan Jihar New York, Andrew Cuomo ya fada a ranar Asabar cewa adadin ya daina karuwa daga yadda aka saba.
New York ce jihar da cutar ta fi yin kamari a Amurka, inda fiye da mutum 180,000 suka kamu da ita daga cikin kusan 530,000 a kasar.
Zuwa ranar Asabar, kowacce jiha a Amurka ta ayyana matakan yaki da annoba domin dakile yaduwar cutar.