Karin mutum 14 sun harbu da Covid-19 a Najeriya

Wannan shafin na kawo muku abubuwan da ke faruwa a duniya baki daya dangane da annobar coronavirus.

Rahoto kai-tsaye

Nasidi Adamu Yahaya, Halima Umar Saleh and Umar Mikail

  1. Coronavirus: Iran na son a ba ta bashin dala biliyan biyar

    Hassan Rouhani

    Asalin hoton, af

    Bayanan hoto, Hassan Rouhani ya ce al'ummar duniya ba za su amince da nuna wa Iran wariya ba

    Iran ta nemi Asusun Ba da Tallafi na Duniya IMF, ya amince da ba ta bashin gaggawa na dala biliyan biyar domin taimaka mata wajen yaki da coronavirus, a yayin da yawan wadanda suke mutu ya kai 4,000.

    Shugaba Hassan Rouhani ya yi gargadi cewa ''bai kamata a nuna wariya'' wajen amincewa bukatu ba.

    Amurka ta sha kin amincewa da bashin, inda jami'ai ke cewa Iran tana da isassun kudade a lalitarta.

    Mr Rouhani ya kira wannan lamari da ''abin kunya a tarihi.''

    Iran ce kasar da cutar Covid-19 ta fi kamari a Gabas Ta Tsakiya, kuma tuni masu dauke da coronavirus suka kai miliyan 1.4 a fadin duniya, sannan tuni mutum 82,000 suka mutu.

    A ranar Laraba ne ma'aikatar lafiya ta Iran ta ce yawan mutanen da suka kamu da cutar a kasar ya karu da 1,997 inda yanzu yawansu ya kai 64,586, sannan wadanda suka mutu ya karu da 121, jumullarsu kuma 3,993.

  2. Covid-19: Za a killace dukkan 'yan majalisar dokokin Botswana

    Za a killace dukkan 'yan majalisar dokokin Botswana 57 tsawon kwana 14 bayan wata nas da ke aiki a majalisar ta kamu da Covid-19.

    Daraktan Lafiya na kasar Malaki Tshipayagae ya bayyana daukar wannan mataki, a cewa sakon Twtter da gwamnatin kasar ta wallafa.

    Ranar Alhamis kasar ta sanar da karin mutum bakwai da suka kamu da coronavirus,cikinsu har da ma'aikaciyar lafiyar da ke aiki a majalisar dokokin.

    Shi ma Shugaba Mokgweetsi Masisi ya halarci muhawarar da 'yan majalisar dokokin suka yi kan tsawaita dokar ta-baci zuwa wata shida.

    Kwanan baya shugaban kasar ya kammala zaman killace kai da ya yi na kwana 14 bayan ya koma daga Namibia a watan Maris.

    Botswana tana da mutum 13 da ke dauke da coronavirus.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

    An hana zirga-zirga tsawon kwana 28 Botswana

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, An hana zirga-zirga tsawon kwana 28 Botswana
  3. Tarayyar Turai 'za ta iya rushewa saboda coronavirus'

    Firai Ministan Italiya ya shaida wa BBC cewa Tarayyar Turai na cikin hatsarin rushewa saboda coronavirus.

    Giuseppe Conte ya ce dole Tarayyar Turai ta dauki matakan da suka dace wajen taimakawa kasashen da cutar ta fi tagayyarawa.

    Mr Conte ya ce Tarayyar Turai tana bukatar ta tashi tsaye domin fuskantar abin da ya kira "kalubale ma fi girma da ake fuskanta tun bayan Yakin Duniya na Biyu."

    Wannan ne karo na farko da ya yi hira da wata kafar watsa labarai a Burtaniya tun da annobar coronavirus ta yi kamari a Italiya makonni bakwai da suka wuce.

    Giuseppe Conte
  4. Covid-19: Mutanen da suka mutu a Spain sun kai 15,000, sabbin kamu sun ragu

    Adadin mutanen da suka mutu sakamakon kamuwa da coronavirus a Spain ya kai 15,238, amma alkaluman sabbin kamuwa da cutar sun ragu.

    Alkaluman da aka fitar awa 24 da suka wuce sun nuna cea mutanen da suka mut a Spain sun kai 683 – hakan ragi ne idan aka kwatanta da mutum 757 da aka bayar da rahoton mutuwarsu ranar Laraba.

    Alkaluman sun nuna yadda ake samun raguwa ta mutuwa sanadin cutar a kasar a kullum. Adadin wadanda suka kamu da cutar ya ragu a kwana na hudu a jere, ko da yake ya dan karu a ranakun Talata da Laraba.

  5. Covid-19: Hira ta musamman da kwamishiniyar lafiyar Kaduna

    BBC Hausa tana kawo muku hira kai tsaye da kwamishiniyar lafiyar jihar Kaduna da ke Najeriya, Dr Amina Baloni.

    Tana yin bayani ne kan matakan da gwamnatin jihar take dauka wajen dakile yaduwar Covid-19, cutar numfashin da kwayar cutar coronavirus take haddasawa.

  6. Coronavirus: An samu wanda ya mutum a karon farko a Somalia

    Somalia ta sanar da mutuwa a karon farko sakamakon Covid-19, cutar sarkewar numfashi da coronavirus ke haddasawa.

    Mutumin da ya mutu yana da shekara 58 a duniya, a cewar ministar lafiyar kasar Fawziya Abikar Nur.

    Mutumin ba ya cikin wadanda suka koma kasar daga kasashen waje kuma an ba shi kulawa a asibitin Martini da ke Mogadishu, babban birnin kasar, a cewar kakakin gwamnati Ismail Mukhtar Orongo.

    Kazalika ma'aikatar lafiyar ta sanar cewa jami'an lafiya biyu na cikin karin mutum hudu da suka kamu da coronavirus a kasar.

    Ya zuwa yanzu mutum 12 ne suka kamu da cutar a Somalia.

    Ya zuwa yanzu mutum 12 ne suka kamu da cutar a Somalia.

    Asalin hoton, AFP

  7. Covid-19: Afirka za ta fada matsin tattalin arziki ma fi girma a shekara 25

    Babban Bankin Duniya ya yi hasashen cewa a wannan shekarar nahiyar Afirka za ta fada matsin tattalin arziki wanda bata taba fuskanta ba a karon farko cikin shekara 25.

    Hasashen ya nuna cewa tattalin arzikin nahiyar zai takure da abin da ya kai kashi 5.1 saboda annobar coronavirus.

    Ya bayyana irin tasirin da cutar za ta yi a kan manyan abokan kasuwancin Afirka da kuma faduwar farashin kayayyaki.

    Kasashen Afirka da dama sun hana zirga-zirga a wani mataki na dakile yaduwar coronavirus.

    Hakan zai yi tasiri mai girma a kan tattalin arzikinsu,a cewar Bankin.

    Ya bayyana irin tasirin da cutar za ta yi a kan manyan abokan kasuwancin Afirka

    Asalin hoton, AFP

    Bayanan hoto, Ya bayyana irin tasirin da cutar za ta yi a kan manyan abokan kasuwancin Afirka
  8. Labarai da dumi-dumi, Coronavirus: Za a saki fursunoni 2600 a Najeriya

    Hukumar kula da gidajen gyaran hali ta Najeiya za ta sallami fursuna 2600 daga gidajen yarin da ke fadin kasar.

    Ministan harkokin cikin gidan kasar, Rauf Aregbesola ne ya bayyana haka a taron da aka gudanar ranar Alhamis a Abuja, babban birnin kasar.

    A cewarsa, za a saki fursuna 70 daga gidan yarin Kuje da ke Abuja a yau Alhamis, sannan daga bisani a saki sauran fursunonin.

    Fursunonin da za a saka sun hada da tsofaffi da marasa koshin lafiya da masu tabin hankali da kuma wadanda aka ci tarar su kasa da N50,000.

    Sa dai ya ce ba za a saki wadanda aka kama da laifin ta'addanci da satar mutane da kisan ba.

  9. An tuhumi mutum biyu da ta'addanci saboda coronavirus

    Ma'aikatar Shari'ar Amurka ta ayyana coronavirus a matsayin "makami mai yada cututtuka" kuma za a iya yi wa duk wanda ya ce cutar karya ce daurin da zai kai na shekara biyar.

    Domin yin aiki da wannan umarni, an zargi wani mutum a Florida da laifin yin tari da tofa yawu kan wasu 'yan sanda lokacin da aka kama shi bisa laifukan cin zarafi a watan Maris.

    Takardun kotu sun nuna cewa wani mutum mai shekara 31 ya shaida wa wani dan sanda cewa: " Ina dauke da corona." Bayan an yi masa gwaji, an gano cewa ba ya dauke da cutar.

    Kazalika, wani mutum a jihar Texas yana fuskantar irin wannan zargi bayan a shafinsa na Facebook ya yi karyar cewa ya biya wani mutum kudi domin ya yada coronavirus a wani babban kantin sayar da kayayyaki a birnin San Antonio.

    Mutum fiye da 14,800 ne suka mutu sanadin coronavirus a Amurka, a cewar Jami'ar Johns Hopkins University.

  10. Covid-19: Shin NCDC ta kashe N1bn domin aikewa da sakonnin waya?

    Hukumar yaki da cututtuka masu yaduwa ta Najeriya, NCDC, ta karyata rahotannin da ke cewa ta kashe kimanin N1bn wajen aike wa 'yan kasar sakonnin text kan yadda za su kauce wa kamuwa da cutar.

    A sakon da NCDC ta wallafa a shafinta na Twtter, ta ce ko da yae sadara na cikin manyan hanyoyin yaki da covid-19, amma kamfanonin wayar salula ne suka dauki nauyin aike wa da irn wadannan sakonni.

    Ya zuwa daren ranar Laraba dai, NCDC ta ce mutum 276 ne suka kamu da coronavirus a kasar, yayin da aka sallmi mutum 44 bayan sun warke, o da yake mutum biyar sun mutu.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  11. Alamun Coronavirus: Abubuwan da suka kamata ku dinga yi

    Abubuwan da suka kamata ku dinga yi
    Bayanan hoto, Abubuwan da suka kamata ku dinga yi
    Abubuwan da suka kamata ku dinga yi
    Bayanan hoto, Abubuwan da suka kamata ku dinga yi
    Abubuwan da suka kamata ku dinga yi
    Bayanan hoto, Abubuwan da suka kamata ku dinga yi
  12. 'Yan sanda sun kama shugaban ma'aikatan shugaban kasa

    An kama shugaban ma'aikatan fadar shugaban Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo ranar Laraba a Kinshasa, babban birnin kasar awowi da dama bayan an yi masa tambayoyi kan zargin kashe kudi ba bisa ka'ida ba.

    An yi wa Vital Kamerhe tambayoyi kan rawar da ya taka game da zarge-zargen cin hanci a kwangilar gudanar da manyan ayyuka wadda ke karkashin kulawarsa a kwanaki 100 na wa'adin da ya wuce na jagorancin Shugaba Félix Tshisekedi's a bara.

    An yi awon gaba da shi zuwa babban gidan yarin kasar mai suna Makala, inda ya kwashe daren jiya.

    Ba a sani ba ko za a tuhume shi a kan zarge-zargen.

    Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ambato mai magana da yawun Shugaba Tshisekedi yana cewa "shugaban kasa ba ya tsoma baki a kan harkokin da suka shafi shari'a".

    Magoya bayan Mr Kamerhe sun yi zanga-zanga a mahaifarsa da ke Bukavu, a gabashin Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo sannan suka toshe hanyar shiga hedikwatar jam'iyyarsa, a cewar AFP.

    Jam'iyyar Mr Kamerhe ta Union for the Congolese Nation (UNC) ta goyi bayan Mr Tshisekedi a zaben shugaban kasar da aka gudanar a watan Disambar 2018.

    Vital Kamerhe (L) supported Félix Tshisekedi (R) in the presidential election

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Jam'iyyar Mr Kamerhe (Hagu) ta goyi bayan Mr Tshisekedi a zaben shugaban kasar da aka gudanar a 2018.
  13. Mutum fiye da 329, 000 sun warke daga coronavirus

    Jami'ar Johns Hopkinsta Amurka da ke bin diddigin yaduwar annobar coronavirus, ta ce mutum 329,876 sun warke daga cutar a fadin duniya zuwa safiyar ranar Alhamis 9 ga watan Afrilu, 2020.

    Jami’ar ta kara da cewa an tabbatar mutum kusan miliyan daya da dubu dari biyar sun kamu da coronavirus.

    Kazalika mutum fiye da 88, 000 sun mutu sanadin covid-19.

    Ga kasashe goma da suka fi fama da cutar ya zuwa safiyar Alhamis:

    Amurka- 432,132

    Spaniya – 148,220

    Italiya -139, 422

    Faransa – 83,080

    Iran – 64, 586

    Birtaniya – 61, 474

    Turkiyya – 38,226

    Belgium – 23,403

      • Marubuci, Nasidi Adamu Yahya
      • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Hausa, Abuja

    Sashen Hausa na BBC ne yake yi muku barka da warhaka.

    Muna fatan kasance tare da ku tsawon wannan rana domin sanar da ku halin da duniya take ciki.

    Za mu kawo muku labarai da rahotannin da suka shafi rayuwarku, musamman kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Nijar da makwabtansu, har ma da sassan duniya.

    Za ku san halin da ake ciki game da annobar coronavirus, wacce ta buwayi duniya.

    Kafin nan, muna kira a gare ku da ku ci gaba da bin shawarwarin manasa lafiya, kamar yawaita wanke hannuwanku da ba da tazara tsakanin juna da kuma kaurace wa shiga taron jama’a, da sauransu.